Akwai bukatar sarakuna a harkar wayar da kai don kauce wa mutuwar jarirai
Sarkin Yakin Gagi Alhaji Sani Umar Jabbi ya bukaci gwamnati ta sanya sarakunan gargajiya a cikin harkar wayar da kan mata su san muhimmancin zuwa asibiti yin awon ciki da zuwa asibiti in nakuda ta taso masu don kauce wa mutuwar jarirai da ake samu barkatai a kasar nan. Sarkin Yakin ya bayyana haka ne […]
Sarkin Yakin Gagi Alhaji Sani Umar Jabbi ya bukaci gwamnati ta sanya sarakunan gargajiya a cikin harkar wayar da kan mata su san muhimmancin zuwa asibiti yin awon ciki da zuwa asibiti in nakuda ta taso masu don kauce wa mutuwar jarirai da ake samu barkatai a kasar nan.
Sarkin Yakin ya bayyana haka ne a zantarwarsa da manema labarai a Sakkwato inda ya ce, abin da zai kawo karshen lamarin shi ne a wayar da kan mata su rika tafiya awon juna biyunsu kuma su rika haihuwa asibiti. Kuma don cimma wannan manufa sai an yi amfani da tsari uku, a fahimtar da maza ta hanyar hudubobi a masallatai da wurin taro su gane amfanin zuwa asibiti ga mata masu juna biyu, kuma a dauki mata masu aikin sa-kai su shiga gida-gida su fahimtar da mata hadarin rashin zuwa a asibiti awo da haihuwa, a karshe a mayar da wurin haihuwar mata a tsanake kamar yadda suka saba da shi kaka da kakanni, maza su daina karbar haihuwa a mayar da haihuwa saman tabarma sabanin saman gado.
Sarkin Yakin ya ce, akwai babban amfani mace ta haihu a hannun jami’an lafiya. “Muna magana da al’umomi sosai a Jihar Sakkwato su kara kula da lafiyarsu. A karshen bara mun waiwayi rahotonmu mun samu cewa yawan mata masu zuwa asibiti awo da haihuwa ya karu sai dai ana bukatar karin ungozoma da magungunan amfani bayan haihuwa,” inji shi.
Ya ce fadada wayar da kai ya fi samar da duk wata kariya ta samun cutar yoyon fitsari, kan haka ya sanya suka shirya taron bita a kauyukan Tsaki da Gandi da Dabagin Ardo da Gande da Acida da Gidan Madi aka fadakar da su son kara inganta lafiyarsu.
Ya yi kira ga al’umomi da sarakunan gargajiya su shiga cikin shirin inganta lafiyar mutane a kuma samu karin wayar da kai.
Ya ce jami’an kiwon lafiya suna fuskantar kalubale sosai a wurin zirga-zirga da sauran bukatu in aka kwatanta su da wadansu masu aikin taimakon al’umma irinsu.
Ya ce, maganin da muke korafi a kai asibiti zai taimaki rayuwar mata da rage mutuwa don rashin magani. Ya ce suna kokari ne a samu raguwar mutuwar mata a wurin haihuwa a Arewa, inda nan ne abin ya fi kamari, a sanar da mutane hanyoyin kariya daga cutar kanjamau ko yada ta a cikin al’umma. “Muna kokarin bayar da shawara ga iyaye su rika yi wa ’ya’yansu rajistar haihuwa don soma tsari mai kyau,” inji shi.
Ya nemi mutanen da suke kin zuwa asibiti in su ji wani abu na dumunsu, inda ya ce su tafi a duba su don a ba su magani, “saboda kowane ciwo na da nasa kula ta daban su bar yi wa kansu magani barkatai wannan yana da hadari,” inji shi.