Akwai bukatar zuba jari mai yawa a bangaren sadarwa – NCC
Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) ta ce don ganin an samu bunkasa a bangaren sadarwa, akwai bukatar a ci gaba da bude wuraren sadarwar yanar gizo wato Intanet da hakan zai kara bunkasa bangaren sadarwa a Najeriya. Shugaban Hukumar NCC Farfesa Umaru dambatta ne ya bayyana haka a Leags a taron masu ruwa da tsaki […]
Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) ta ce don ganin an samu bunkasa a bangaren sadarwa, akwai bukatar a ci gaba da bude wuraren sadarwar yanar gizo wato Intanet da hakan zai kara bunkasa bangaren sadarwa a Najeriya.
Shugaban Hukumar NCC Farfesa Umaru dambatta ne ya bayyana haka a Leags a taron masu ruwa da tsaki a harkar sadarwar Intanet a Afirka karo na 27 (AFRINIC-27).
Ya ce zuba jari a harkar sadarwa zai samu bunkasa ne kadai idan aka rika bullo da tsare-tsaren da suka dace.
Ya ce idan aka bunkasa harkar sadarwa ta hanyar bude sansanonin da za a rika amfani da su na yanar gizo (Intanet) ko shakka babu hakan zai ci gaba da samar da ayyukan yi, da hakan zai bunkasa tattalin arziki da kuma yin gogayya da sassan duniya a bangaren sadarwa irin ta zamani.”.
Ya ce tsarin sadarwa na Afircan Regional Internet Registry (AFRINIC), ya sa harkar yanar gizo ta intanet ta bunkasa a Afirka. Ya ce a shekarar 2002 masu amfani da intanet su miliyan 4 da dubu 500 ne kacal amma ya zuwa shekarar 2017 adadinsu ya kai Miliyan 388. (http://www.internetworldstats.com).
Ya ce babbar matsalar da ake fuskanta a Afirka a game da amfani da yanar gizo na Intanet shi ne ci gaba da bunkasar shirin, don haka ne hukumar ke kokarin karfafa wa al’umma gwiwa wajen ci gaba da bude cibiyoyin intanet. Don haka akwai bukatar a ci gaba da kakkafa cibiyoyin intanet musamman masu amfani da na’urar brodaband da hakan zai samar da ayyukan yi da bunkasar tattalin arziki da kuma yin gogayya da kasashen da ke amfani da intanet a sassan duniya.
Ya ce abin la’akari a nan shi ne kamar yadda harkar intanet take bunkasa to haka kuma ake samun karuwar masu cutar al’umma a bangaren yanar gizo a kullum. Don haka wannan ya zama kalubale ga kasashen duniya su ci gaba da lalubo hanyoyin da za a bi wajen hana masu yaudara ko cutar al’umma ta yanar gizo”.
Ya ce tuni Hukumar NCC ta hada kai da masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa don gani an shawo kan matsalar masu amfani da yanar gizo suna yaudarar mutane.
Ya ce tuni hukumar ta kafa cibiyar yaki da masu yaudarar al’umma a yanar gizo ta intanet (Sectorial Computer Security Incident Response Team (CSIRT) inda za ta hada gwiwa da ofishin Mai Ba Shugaban kasa Shawara a bangaren tsaron kasa (ngCERT) don ganin an hada kai da kamfanonin sadarwa wajen yakar masu amfanin da yanar gizo suna cutar al’umma.
Ya ce a game da hada kai da kasashen duniya wajen yakar masu amfani da yanar gizo suna cutar al’umma kuwa, tuni Hukumar NCC bukaci kungiyar yaki da masu zambatar al’umma a yanar gizo ta duniya (International Telecommunications Union (ITU), ta bude ofishinta a Abuja. Ya ce idan aka bude cibiyar a Abuja za ta rika horar da kasashen Afirka musamman wadanda ke makwabtaka da Najeriya wajen yaki da masu damfarar al’umma a yanar gizo.
Shugaban Hukumar NCC ya kara da cewa tsarin broadband na yanar gizo yana da matukar muhimmanci a harkar sadarwa inda ya ce tuni tsarin Nigerian National Broadband Plan (NBP) na shekarar 2013 ya ce zai ci gaba da bunkasa tsarin da akalla kashi 30 daga cikin 100 daga nan zuwa shekarar 2018.
Ya ce a kan haka ne hukumarsa ta dauki tsarin broadband da muhimmanci inda ta mayar da shi daya daga cikin kudurori 8 da take yunkurin aiwatarwa a bangaren sadarwa. Ya ce hakan ne ya sa hukumar NCC take yunkurin ganin ta zarce kashi 30 daga cikin 100 na adadin da take niyyar cimmawa daga nan zuwa shekarar 2018. Ya ce ya zuwa watan Satumbar 2017 Najeriya ta cimma kashi 21.8 ne kacal daga cikin 100 a tsarin broadband.
Ya ce a kan haka ne hukumar ta kuduri bin hanyoyi kamar haka wajen cimma kudurin kashi 30 din kafin 2018 kamar haka:
* Za a samar da tashoshi masu karfin 700MHZ guda biyu don a bunkasa tsarin broadband;
* Haka kuma za a fadada tsarin band mai karfin 800MHz da aka fi sani da Digital Dibidend 1 da za a kara masa karfin 4G da za a dade ana cin moriyarsa (Long Term Ebolution (LTE);
* Haka kuma za a fadada tsarin brodband mai karfin 900MHz zuwa karfin 4G mai cin dogon zango da shi ma za a dade ana cin moriyarsa
* Sannan an bude tasoshin brodband masu karfin 70/80GHz (E-Band) don a bunkasa tsarin broadband
* Sannan an bayar da lasisin bude tashar broadband mai karfin 4G LTE
* Haka kuma an umarci wadansu kamfanonin sadarwa su daukaka darajar na’urorin sadarwarsu zuwa 4G LTE don a samu biyan bukata wajen fadada tsarin broadband.
“Wannan ya nuna nan ba da dadewa ba za a samu ci gaba mai ma’ana a harkar yanar gizo a Najeriya”.
Ya kara da cewa, an samu ci gaba a bangaren samar da kayayyakin sadarwa irin na zamani IdPs a yankin Afirka amma duk da haka akwai bukatar a kara kaimi wajen hada kasashen Afirka da layukan sadarwa. Ya ce hakan ce zai sa Afirka ta rika adana muhimman bayanai da kuma yin hulda da sassan duniya a bangaren yanar gizo ba tare da wata matsala ba.
Don ganin an cimma wannan buri, akwai bukatar kasashen Afirka su bayar da damar samar da na’urar sadarwa irin ta zamani mai karfin IPb6.
Ya dace mu kula da bangaren sadarwar intanet a yankin Afirka da ma a duniya baki daya.
Ya ce “na yaba da kokarin da ake yi wajen bunkasa harkar intanet a Najeriya da ma daukacin Afirka a halin yanzu.
“Abin lura a nan shi ne kamata ya yi a hada kai wajen bunkasa harkar intanet, don haka akwai bukatar hada kai da masu ruwa da tsaki a harkar don a samu biyan bukata.
A kan haka ya ce hukumarsa za ta bayar da nata gudunmawa don a samu biyan bukata musamman a bangaren bayar da shawarwari da kuma samar da dokokin da zai ba al’umma damar mallakar cibiyoyin intanet a farashi mai rahusa da kuma samun lasisin budewa ba tare da sun sha wahala ba da hakan zai bunkasa wannan bangare.