Akwai darussan rayuwa cikin wadannan labarun (2)
Jama’a masu karatun Aminiya, muna yi muku sallama, Assalamu alaikum. Bayan haka, yau kuma mun lalubo maku wasu kananan labaru ne na hikima, wadanda ke cike da hikima da koya darussan da suka shafi rayuwar yau da kullum. Muna fatan za su zama masu haska mana rayuwa, domin dai mu samu natsuwa da kwanciyar hankalin […]
Jama’a masu karatun Aminiya, muna yi muku sallama, Assalamu alaikum. Bayan haka, yau kuma mun lalubo maku wasu kananan labaru ne na hikima, wadanda ke cike da hikima da koya darussan da suka shafi rayuwar yau da kullum. Muna fatan za su zama masu haska mana rayuwa, domin dai mu samu natsuwa da kwanciyar hankalin fuskantar wannan kalubale da ke ta kawo mana karo a kullum, wato kalubalen rayuwar yau da kullum ke nan. Ba tare da bata lokaci ba, za mu fara da wannan labarin:
Wata rana ne wasu ma’aikata suka fito domin zuwa wurin aiki, bayan sun dauki dan lokaci sun shakata a waje. Cikin ma’aikatan akwai manajan ma’aikatar da sakatarensa da kuma daya daga cikin kananan ma’aikata. Suna tsakar tafiya sai suka ci karo da wata laya, wacce ke yashe a kasa. Ashe wannan laya ta aljanu ce. daya daga cikinsu ya sanya hannu da nufin kawar da ita daga kan hanya, sai ga wani aljani ya bayyana a gabansu. Har sun ji tsoro za su ruga, sai ya tsayar da su.
“Kada ku ruga, ba zan cutar da ku ba.” Inji wannan aljani da ya fito cikin siffar mutane. “Ni aljani ne bawan wannan layar, duk wanda ya mallaki layar nan kuma ya murza ta, zan fito in yi masa hidimar duk da yake bukata. Don haka yanzu sai ku fadi bukatunku dai-dai, ni kuwa duk zan biya maku.”
Jin haka, sai karamin ma’aikacin nan ya yi zambur ya ce, “Ni zan fara tambayar bukatata, ni zan fara.” Su kuwa sauran mutum biyu, da manaja da sakatare suka amince masa ya fara fadin bukatarsa. Nan take kuwa ya ce shi yana bukatar ya gansa a kasar Dubai yana shakatawa a babban otel, yana cikin karamin jirgin ruwa na alfarma yana shakatawa.
Yana gama fadin haka, sai suka ga ya bace nan da nan, aljanin nan ya dauke shi zuwa Dubai. Daga nan kuma sai sakatare shi ma cikin zumudi ya zakalkale ya ce, “Saura ni, ni ne na gaba!” Manaja ya kyale shi don ya fadi bukatarsa. Nan da na sai ya ce, “Bukatata ita ce, ina son in gan ni a kasar Amurka cikin daula ina shakatawa da budurwata cikin gamsarwa.” Kafin ya rufe baki har ya bace, aljani ya dauke shi zuwa Amurka.
“To saura kai ka rage, sai ka fadi bukatarka domin in biya maka ita kamar yadda na yi wa saura.” Aljani ya fada wa manaja haka. Abin mamaki, sai manaja ya buda baki ya ce, “Ni dai bukatata ita ce, ina son ka yi gaugawar dawo mani da ma’aikatana, in gan su yanzu-yanzu a cikin ma’aikatata suna aiki.”
Kafin ya rufe baki har an dawo da su cikin ma’aikatar suna aikinsu.
Masu karatu, ko kun gane darasin da ke cikin wannan labari? Babban darasin dai shi ne, har kullum idan mutum na tare da shugabansa, to kada ya ce zai sha gabansa, ya bari shugaban ya jagoranci al’amuransa. Wato ba kamar yadda wadannan kananan ma’aikata suka yi wa manaja ba, wanda haka ya sanya suka rasa samun biyan bukatunsu. Tun farko da sun ba shugabansu uzuri ya fara fadin bukatarsa, da su ma za su samu biyan bukatunsu cikin ruwan sanyi. Don haka, ya kamata mu gane cewa, a rayuwa, mu rika yin biyayya ga shugabanni, mu rika ba su uzuri, domin duk wanda Allah Ya shugabantar kan mutane, to akwai dalilin haka, idan ka yi biyayya, kai za ka samu ribar haka.
Yanzu kuma ga labari na biyu: Wata rana ne maiki na zaune kan wata bishiya, sai ga wani dan karamin zomo ya zo wurinsa ya ce masa; “Ko ka amince mani ni ma in zauna kusa da kai yadda na ga kana ta hutawarka a nan?” Shi kuwa maiki ya ce masa, me zai hana ya zauna?
Shi kuwa zomo sai ya zauna bisa wani reshe da ke kasan reshen da maiki ke zaune. Yana zaune haka abinsa, bai ankara ba sai ga dila ya zo ya cafke shi ya cinye abinsa.
Ko an ankara da darasin dake cikin wannan dan labari? Na san ba za ku kasa ganowa ba, domin dai darasin a bayyane yake. Amma bari in dan yi maku matashiya. Abin da labarin nan ke nunawa shi ne, zaman haka nan bai da alfanu. Idan ma kana son yin zaman haka nan, to ka tabbata ka isa, wato, sai ka zauna can kololuwa, inda matsalolin rayuwa ba za su iya cin maka ba. Dubi dai inda maiki ya zauna, wato can sama, shi kuwa zomo ya zauna a kasa. Don haka sai mu kasance cikin taka-tsan-tsan da rayuwa. Idan har ba ki da gashin wance, kada ki ce za ki yi irin kitson wance. Idan ka daka rawar wani, to tabbas za ka rasa turmin daka taka.
Har kullum dai ya kamata kafin mu aikata wani abu, sai mu tsaya tsam mu yi tunani kan wannan al’amari. Mu tambayi kawunanmu alfanun da ke cikinsu, sannan mu yi nazarin ko abin ya dace da mu? Za mu iya aikata shi kuwa cikin fa’ida? Mun isa ma mu aikata shi? Idan ma mun aikata din, to me za mu samu na sakamako? Sakamakon zai amfane mu a rayuwa ko kuwa cutar da mu zai yi?
Gano wadannan amsoshi suna da matukar amfani, muddin dai muna son samun fa’ida daga ayyukan da muke sanya kawunanmu. Domin har kullum abin da ya bambanta mutum da dabba shi ne wannan hankali da muke da shi, wanda da shi muke yin nazarin jiya, mu kwatanta da yau, sannan mu san inda za mu tunkara gobe idan Allah Ya kai mu.
Da wannan nake cewa sai Allah Ya kai mu mako na gaba, inda za mu kara kawo maku wani sabon maudu’in na Sinadarin Rayuwa. Allah dai Ya yi mana muwafaka, mu samu ribar rayuwar yau da ta gobe, amin!