Akwai fa’ida a sana’ar ruwan dumi – Sagir Mai Ruwan dumi
Sana’ar sayar da ruwan dumi bakuwar sana’ace ce domin jama’a ba su fiye shigarta ba kamar sauran sana’o’in yau da kullum, amma akwai wani matashi da yake gudanar da irin wannan sana’ar a unguwar Zango da ke cikin birnin Kano. Matashin mai suna, Sagir Yusuf Muhammad, wanda tsohon mai shayi ne a gefen titin asibitin […]
Sana’ar sayar da ruwan dumi bakuwar sana’ace ce domin jama’a ba su fiye shigarta ba kamar sauran sana’o’in yau da kullum, amma akwai wani matashi da yake gudanar da irin wannan sana’ar a unguwar Zango da ke cikin birnin Kano.
Matashin mai suna, Sagir Yusuf Muhammad, wanda tsohon mai shayi ne a gefen titin asibitin Murtala, ya shaida wa Aminiya cewa ya fara sana’ar sayar da ruwan zafin ne kimanin shekara biyar da suka wuce sakamakon barin unguwar da matar da ke gudanar da sana’ar ta yi.
“Tun asali akwai matar da ke gudanar da wannan sana’ar, amma sai ta bar unguwar, a lokacin ne ta nemi na ci gaba da sana’ar kasancewar baya ga ribar da ake samu, a gefe guda kuma sha’ani ne na taimakon jama’a. Daga nan na ci gaba da yin sana’ar har zuwa yau,” inji shi.
Sagir ya bayyana cewa duk da cewa yana gudanar da sana’ar a kowane lokaci, ya fi samun kasuwa a lokacin sanyi. Haka kuma yana gudanar da sana’a ne da safe da kuma yamma, sai dai a cewarsa an fi sayen ruwan da safe.
Ya kuma bayyana cewa mafi yawan abokan cinikinsu su ne marasa lafiya da ke kwance a asibiti, musamman mata masu haihuwa domin yin wankan jego. Ya kara da cewa “amma sauran jama’ar gari ma sukan sayi ruwan a wurina musammman a lokacin sanyi,” inji shi.
Sagir ya ce yakan fara shirye-shiryen sana’arsa ne tun karfe 2:00 na dare, inda za a dora ruwan domin ganin masu bukatar ruwan sun samu a kan lokaci, idan gari ya waye. “Da zarar karfe 4:00 ya yi za ka ga matan sun fara kafa layi a nan, inda ni kuma zan tsaya na rika zuba musu ruwan a cikin bokitan da suka zo da su. Ina sayar da ruwan ne akan farashin kofi daya, Naira biyar. Idan kuma da yawa ake bukata mukan sayar da kofi uku Naira goma,” inji shi.
Kamar yadda kowace sana’a take, Sagir ya bayyana irin nasarorin da ya samu da kuma wasu daga cikin kalubalen da yake fuskanta. “Babu shakka ina samin fa’ida sosai a wannan sana’ar domin tana rufa min asiri. Ina ci, ina sha, ina yin sutura. Alhamdulillahi. Game da kalubale sana’ar kuwa, muna fuskantar karancin ruwa wanda kowa a jihar nan ya san yadda ake fama da wannan matsala. A gaskiya idan mutum ba jajircewa ya yi a kan sana’ar ba, to daga kan iza wuta kawai zai ji abin ya fice masa daga rai,” inji shi.
A karshe kuma ya yi kira ga gwamnati da ta tallafa musu da jari domin bunkasar sana’arsu.