Akwai fa’ida sosai a sana’ar wankin mota – Malam Bako
Malam Bako Isma’il Muhammad wani matashi ne mai sana’ar wankin mota wanda ya shafe kimanin shekara takwas yana gudanar da sana’ar. Aminiya ta zanta da shi a kamfaninsa da ke garin Minna, mai suna Clean-Clean Car Wash dangane da fa’idojin da ya samu da dai sauransu. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Me ya ba […]
Malam Bako Isma’il Muhammad wani matashi ne mai sana’ar wankin mota wanda ya shafe kimanin shekara takwas yana gudanar da sana’ar. Aminiya ta zanta da shi a kamfaninsa da ke garin Minna, mai suna Clean-Clean Car Wash dangane da fa’idojin da ya samu da dai sauransu. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Me ya ba ka sha’awar bude wannan wurin wanke motoci?
Malam Bako: Babban dalilin da ya sa na bude wannan wurin shi ne domin ba da ta wa gudunmuwar wurin taimaka wa matasa ta fuskar samun aikin yi. Idan ka yi la’akari da wannan zamanin da yara da dama ke kammala ilimi a matakan karatu daban-daban kuma daga karshe ba su samun inda za su rufa wa kansu asiri ta hanyar samun na kansu ta amfani da karfin jikinsu da basirarsu domin cimma wannan burin da suka sa a gaba.
Aminiya: Da ma’aikata nawa ka fara kuma yau kana da ma’aikata nawa ne?
Malam Bako: Lokacin da na bude wannan wurin a shekarun 2006 zuwa 2007, ma’aikatan har da manaja ba su wuce mutane biyar ba. A yanzu da muke magana da kai ina da akalla ma’aikata 30 wadanda ke yi mini aiki a kullum, muna da wadansu na wucin-gadi wadanda kan zo a karshen mako su yi mana aiki. Daga cikinsu muna da masu takardar shaidar Difloma guda biyar, masu takardar Babbar Difloma HND guda uku, sai wadanda suka kammala ilimin sakandare wadanda suke sha’awar neman ilimi mai zurfi a manyan makarantu daban-daban na kasar nan.
Wasu daga cikin kan yi aikin wucin-gadi na shekara daya ko biyu, muddin suka tara abin da suke da buri na zuwa makaranta magana ta kare, sai su kara gaba zuwa makarantunsu. Idan suka zo mana da takardar dauka domin karo ilimi, mukan taimaka musu da abin da Allah Ya hore mana kudi ke nan bakin gwargwadon hali.Wasu daga cikinsu kan dawo nan su ci gaba da wannan aikin idan suka samu hutun makaranta.
Aminiya: Wadanne matsaloli ne kuke fuskanta yayin gudanar da wannan wurin?
Malam Bako: Ka san muddin mutum ya kudurci neman halaliyarsa a rayuwa akwai kalubale masu dama. Haka ma a nan muna fama da su. Wasu da suka zama mashahurai mun shawo kansu tun farko. Wadannan sun hada da ruwa da ma’aikata.
Tsarin da muka yi na gudanar da wurin ya sa muna da kyakkyawar alaka da su musamman wurin biya. Tsarin biya shi ne mu kan biya ma’aikaci a kullum daidai yawan motocin da ya wanke a ranar. Mukan biya kowane ma’aikaci da zarar ya gama aikinsa nan take, sai mu raba biyu, ya dauki rabi, mu kuma mu dauki sauran rabin, ba ruwansa da kudin sabulu da na ruwa, karfinsa kawai da basirarsa kawai muke bukata. Ka ga idan mutum ya wanke motoci kamar biyar a yini sai godiyar Allah.
Aminiya: Wace fa’ida kuke samu daga sana’ar?
Malam Bako: Akwai fa’idoji sosai a sana’ar wankin mota. A gaskiya sai dai mu ce Alhamdulillahi. Kwalliya tana biyan kudin sabulu.
Aminiya: Wadanne nau’o’in taimako ne kuke bukata daga wurin gwamnati domin bunkasa wannan sana’ar?
Malam Bako: Da zarar aka yi maganar gwamnati ta zama uban kowa baki daya. Gwamnati ta taimaka mana da kudin da za mu fadada wannan sana’ar don mu samu karin sukunin daukan ma’aikata. Ka ga muna bukatar injinan wanke motoci. A halin yanzu muna da guda biyu ne kawai.
Da kamar karshen mako ya yi, motoci ne ake gani babu masaka tsinke saboda masu motoci kan yi dandazo da jerin gwano suna neman a wanke musu motoci. Ka ga a nan me injina biyu za su yi a wannan lamarin. Idan har zan samu injina akalla guda biyar, ko shida za su yi kwarai da gaske.
Aminiya: Wace rawa kake ganin masu hannu da shuni za su iya takawa domin taimakawa matasa?
Malam Bako: Abin da nake so jama’a su yi la’akari da shi shi ne arziki jarrabawa ce daga Allah. Da zarar mutum ya samu kansa cikin wannan hali sai ya yi tunanin taimaka wa na kasa da shi domin su ma su samu hanyar da za su samu rufin asiri domin magance zaman banza a al’umma wadanda kan haifar da matsalolin da za su dade kafin a shawo kansu.
Aminiya: Wace shawara za ka ba matasanmu domin su yi amfani da damar da suka samu a rayuwa?
Malam Bako: Ka ga lokaci zuwa lokaci mukan yi gana da ma’aikatana domin tattauna al’amuran da suka shafe mu tare da tattauna yadda za mu shawo kan al’amarin baki daya ba tare da bata lokaci ba. Nakan fada musu kar mutum ya sa dogon buri a rayuwa. Mutum ya nemi albarkar da ke cikin sana’ar da yake yi.
Ba wai ya samu abu mai yawa ya tara shi ne abin alfahari ba.Wannan shi ne babban abin da ya taimaka mana muka kai ga wannan matsayin da muka samu kanmu na samun kustomomi masu yawa wadanda muke mu’amala da su a kowane lokaci.