Akwai farfaganda kan labaran rashin zaman lafiya a Najeriya – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce akwai farfaganda kan labaran matsalar tsaron da ake bayarwa a Najeriya. Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi wajen rufe taron bita kan aikin Hajji da kungiyar ta shirya […]

Akwai farfaganda kan labaran rashin zaman lafiya a Najeriya – Sheikh Jingir
Akwai farfaganda kan labaran rashin zaman lafiya a Najeriya – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya ce akwai farfaganda kan labaran matsalar tsaron da ake bayarwa a Najeriya.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi wajen rufe taron bita kan aikin Hajji da kungiyar ta shirya wa maniyyata a Jos, inda ya ce a kullum ana yada labaran cewa babu zaman lafiya a Najeriya, ana kashe-kashe a ko’ina.
Ya ce a yanzu duk wanda yake jin labaran Najeriya daga waje zai dauka kamar ba za a iya shigowa kasar nan ba. “Amma duk wanda ya shigo Najeriya, ya shiga birane da kauyuka zai ga mutane na gudanar da harkokinsu na yau da kullum. Hatta a Maiduguri ana gudanar da harkokin kasuwanci. Mutanen Arewa na daukar kayan amfanin gona suna kaiwa Kudu, haka su ma mutanen Kudu suna dauko kayan kasuwancinsu suna kawowa Arewa, ba tare da wata matsala ba. Wannan ya nuna cewa har yanzu akwai zaman lafiya a Najeriya,” inji shi.
Ya ce duk da labaran da ake bayarwa kan matsalar tsaro a Najeriya, akwai nasarorin da aka samu masu yawa. Ya kawo misali cewa a bana kadai an samu filayen jiragen sama hudu da ake jigilar maniyya zuwa kasa Mai tsarki.
Sheikh Jingir ya yi kira ga maniyyatan kasar nan kan kada su razana, su tafi aikin Hajji a natse su roki Allah, su yi wa Najeriya addu’o’in alheri. Kuma su bi dokokin Saudiyya kada su yi abubuwan da za su zubar da mutumcin kasar nan.
A jawabin jami’in shirya bitar, Hafiz Aminu Yusuf ya ce sun shirya bitar ce don ilimantar da maniyyata kan aikin Hajji.  Ya ce za su ci gaba da gabatar da taron bitar a kowace shekara ga maniyyatan da za su tafi aikin Hajji.