Akwai gagarumin aikin gaban Cif Bola Tinubu wajen sasanta ‘Yan APC

daya da daya bai zama wani abin mamaki ba tun a ranar 6 ga watan Fabrairun da ya gabata da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada jagoran jam’iyyar APC na kasa baki daya kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas Alhaji Bola Ahmed Tinubu a zaman shugaban kwamitin da zai sasanta dukkan ‘yan jam’iyyar APC a kasa […]

Akwai gagarumin aikin gaban Cif Bola Tinubu wajen sasanta ‘Yan APC

daya da daya bai zama wani abin mamaki ba tun a ranar 6 ga watan Fabrairun da ya gabata da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada jagoran jam’iyyar APC na kasa baki daya kuma tsohon Gwamnan Jihar Legas Alhaji Bola Ahmed Tinubu a zaman shugaban kwamitin da zai sasanta dukkan ‘yan jam’iyyar APC a kasa baki daya, gagarumin aikin da fadar shugaban kasa ta ce ya rage ga shi Tinubu ya zabi irin mutanen da ya ga sun dace su rufa masa baya cikin gudanar da aikin nasa. Abin da ya sanya na ce bai zama wani abin mamaki ba, na nadin da shugaban kasar ya yi wa Tinubun a kan wannan gagarumin aiki, bai wuce irin muhimmiyar rawar da Tinubu ya taka wajen samun hadakar jam’iyyun CPC da ACN da ANPP da wani bangare na jam’iyyun PDP da APGA, da suka narke wuri daya a shekarar 2014, suka kafa sabuwar jam’iyyar APC.

Bayan kafuwar jam’iyyar APC Cif Tinubu ya ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen ganin Shugaba Buhari ya samu nasarar duk da ake bukata da ta kai shi ga lashe babban zaben shekarar 2015. Haka wannan gagarumar nasara ta tabbata da aka sa ni ‘yan takarar APC da suka tsaya takarar neman mukamai, kama daga Kano gwamnonin jihohi zuwa ’yan majalisun dokoki na kasa da na jihohi. Ko ba komai a tarihin siyasar kasa nan tun daga samun ’yancin kai a shekarar 1960, ba a taba samun tafiyar siyasa tare ba da kuma ta haifar da gagarumar nasara tsakanin mutanen Arewacin kasar nan da na shiyyar Kudu maso Yamma, wato kasar Yarabawa kamar yadda aka samu a waccan hadakar da ta tabbatar da kafa jam’iyyar APC. Haka kuwa ba ta rasa nasaba da irin rawar da Cif Tinubu ya taka kasancewarsa a yau ba sai gobe ba shugaba daya tilo da ’yan kabilarsa ta Yarbawa suke saurare fiye da shi. Wannan gagarumar gudunmuwa da ya ba da tana matukar biyansa a siyasance, domin an ce bayan mataimakin shugabam kasa Farfesa Yemi Osinbajo da sanata Tinubu ya kai shi akwai kuma dinbin ‘yan siyasa a wannan gwamnatin da albarkacinsa suke ci.  

Idan muka dawo a kan aikin da aka dora masa na ya sasanta dukkan ‘yan jam’iyyarsu ta APC a kasa baki daya, wala Allah wadanda tuni sukai fushi suka canja sheka zuwa wata jam’iyya ko kuma wadanda rigima ta kaure musu a cikin jiha daya ko makamanta irin wadannan rigingimu, za ka ga cewa ba karamin aiki aka dora wa madugun jam’iyyar APC na kasa baki daya. Yanzu maganar da ake akwai rikicin da ba a ga maciji a jihohi irin su Kaduna da Kogi da Kano da Adamawa da Imo da Zamfara da Bauchi da Oyo da makamantansu. Baya ga wanda aka dade ana yi tsakanin shugabancin majalisar dattawa da fadar shugaban kasa, rikicin da ya yi gagarumar shafar ayyukan bangarorin biyu. Alal misalai, a Jihar Kaduna rikici ne tsakanin gwamna Nasiru El-Rufa’I da sanata Shehu Sani da sanata Sulaiman Hunkuyi lamarin da ya kai ga gwamna El-Rufa’I ya gurfanar da sanata Shehu Sani gaban wata babban kotu yana bukatar diyyar miliyoyin nairori a zaman bata masa suna da ya yi zargin sanata Shehu Sani ya yi masa. Ya yin da gwamnatin jihar ta Kaduna ta rushe gidan sanata Hunkuyi bisa ga zargin an gina shi ba bisa ka’ida ba da kuma aika masa da bil din neman ya biya Naira miliyan 30, a zaman harajin wani gidansa da ke Kaduna da bai biya wa haraji ba na wasu shekaru. Alhali Gwamna El-Rufa’I bai rushe wancan gida da ke Kaduna ba, balle kuma aika  wa sanata Hunkuyi ya biya wancan haraji, sai bayan da sanata Hunkuyi ya mayar da gidan a zaman hedkwatar sabon bangaren jam’iyyar ta APC a Jihar Kadunan.

A Jihar Kano ma cikin jam’iyyar APC din rigima ce ta kaure tsakanin tsohon gwamnan jiha, kuma sanata mai ci yanzu Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso da gwamna mai ci Dokta Abdullahi Umar Ganduje, wanda yake ko ba komai tunda aka fara wannan mulkin jamhuriyar a 1999, suke tare ko dai a zaman mataimaki gwamna ko kuma mataimaki na musamman, abin da ya kai har Gwamna Ganduje ya gaji sanata Kwankwaso a zaben shekarar 2015, amma dai yanzu ta yi mummunan zafi tsakaninsu da ma mabiyansu. Haka labarin yake na rashin irin wannan fahimtar tsakanin Gwamnan Jihar Bauchi,  Alhaji Muhammdu Abubakar da sanatocin jihar guda 3, da shi kan shi Kakakin majalisar wakilai ta tarayya Mista Yakubu Dogara da kusan dukkan ‘yan majalisar wakilai da suke wakiltar Jihar Bauchi. Babban laifin da suke zargin Gwamna Abubakar bai wuce ya saki layi a bisa ga alkawarin da suka yi da shi kafin cin zabe. 

A Jihar Imo Gwamnan jihar Cif Rochas Okorocha ya fara samun kalubale da jiga-jigan jam’iyyar APC na jihar tun bayan da ya furta cewar surikinsa, kuma shugaban ma’aikatan fadar Gwamnatin jihar Mista Uche Nwosu shi zai ga je shi. Mai karatu haka ake ta fama da wadannan rikice-rikice a cikin jam’iyyar ta APC a jihohin da ban iya kawowa ba. 

A kasa akwai gagarumar rigima tsakanin fadar shugaban kasa da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, tun bayan zaben da majalisar dattawan sukai yi ma sanata Saraki a zaman shugabansu, alhali ba shi jam’iyya ta fadar shugaban kasa suke bukata ba. Daga karshe ma dai kotu hukumar da’ar ma’aikata ta maka sanata Saraki a zaman tana tuhumarsa da yin coge wajen bayyana kaddarorin da ya mallaka tun yana gwamna a jiharsa ta Kwara. Wannan rashin jituwa ita haddasa majalisar dattawan ta ja daga ta ki amincewa Shugaba Buharin ya nada Malan Ibrahim Magu a zaman cikakken shugaban EFCC, da ma wasu irin sunaye da shugaban ya mika tuntuni don neman amincewar majalisa. Hakan kuma shi ya haddasa a shekarar 2017, majalisar ta cire sanata Ali Ndume daga kan mukaminsa na shugaban masu rinjaye na majalisar, kuma ta dakatar da shi har tsawon watanni 6. Kai! Yanzu ma ta kai majalisar dattawan ta kama hanyar rabewa gida 2, tsakanin magoya bayan shugaban majalisar dattawan da kuma ofishin shugaban kasa.

Shi kansa sanata Tinubu tun tuni ba tun yau ba yake cikin takun sakar rashin fahimta tsakaninsa da shugaban jam’iyyar APC na kasa baki daya Cif John Odigie Oyegun, kama daga fitar da dan takarar neman mukamin Gwamnan Jihar Ondo da aka yi a shekarar 2016, ya zuwa yanzu a kan wannan kwamitin sasantawa da har ta kai sanata Tinubu ya bara, inda ya aika da wata wasika shugaban jam’iyyar APC din na kasa baki daya ya kuma tura kofe-kofen wasikar zuwa ga shugaban kasa da mataimakinsa da shugaban majalisar dattawa da shugaban majalisar Wakilai na tarayya, inda ya ke zagin shugaban jam’iyyar APC din ta hana ruwa gudu da kawo tarnaki cikin ayyukan yin sulhun ga ‘yan jam’iyya, bisa ga zargin har zuwa wancan lokaci da shugaban jam’iyyar ya ki ya ba shi cikakken rahotan jihohin da suke fama da rigingimu duk kuwa da neman hakan da ya yi. 

Mai karatu da wannan dan takaitattacan bayani za ka iya gane cewa dukkan wadannan sabani da rigingimu da hauma-hauma duk kasuwar bukata ce, amma ba don jama’a ba sai don son zuciya, duk kuma abin da ya shafi son zuciya, to kuwa gyaran sai Allah.