Akwai gyara a ciyar da daliban Firamaren Jihar Kaduna

Akwai gyara a ciyar da daliban Firamaren Jihar Kaduna Zuwa ga Editan Aminiya, zan yi farin ciki idan ka ba ni fili a wannan jarida tamu mai farin jini don in yi tsokaci a game da yadda ake ciyar da dalibai abinci a Jihar Kaduna, wanda Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya […]

Akwai gyara a ciyar da daliban Firamaren Jihar Kaduna
Akwai gyara a ciyar da daliban Firamaren Jihar Kaduna

Akwai gyara a ciyar da daliban Firamaren Jihar Kaduna

Zuwa ga Editan Aminiya, zan yi farin ciki idan ka ba ni fili a wannan jarida tamu mai farin jini don in yi tsokaci a game da yadda ake ciyar da dalibai abinci a Jihar Kaduna, wanda Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya fara kimanin makwanni biyu da suka wuce.  A gaskiya akwai gyara, don ana ciyar da daliban makaranta ne da ke zangon karatu na safe, kuma mafi yawan makarantun akwai daliban da ke yin karatu da Yamma (karfe daya zuwa 5), to masu karatu da yamma mene ne makomarsu a game da ciyarwar?  Sannan yadda ake cewa sai mai unguwa ko Dagaci ko wani Basarake ya dandana abincin a wasu makarantu kafin a raba wa dalibai shi ma akwai gyara. Don akwai yiwuwar a sanya son rai wajen tantancewar.  Ma’ana duk Dagaci ko Hakimi ko wani Basaraken da ba ya shiri da mai dafa abincin zai iya cewa abincin babu dadi ko da kuwa akwai.  Don haka ya kamata a yi nazari a wannan batutuwa biyu da na ambata. Na gode.  
Daga Abban Faisal 08097015805.

kungiyar asiri ta cutar da yaro

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Tabbas ko shakka babu duniyar nan da kusan tashi, ganin yadda ake ci gaba da samun marasa imani da suka fifita duniyarsu a kan lahira; ina magana ne kan wasu marasa imani da tausayi ’yan kungiyar asiri a garin Zariya ta Jihar Kaduna, inda suka kama yaro dan shekara 4 suka kwakwale masa idanu a gaskiya dajin wannan labari sai da ya tayar mana da hankali matuka. Da haka muke kira ga mahukuntar jahar kaduna dama jami’an tsaro su dukufa da binciken gano wadanda suka yi wannan aika-aika domin hukuntasu ta hanyar kwakwale masu idanu su ma kamar yadda suka aikata. Daga karshe nake rokon Allah da ya kawo muna karshen miyagun da ke lahanta bayinka albarkar annabinka.
 Daga Naziru Akbubakar Sabo Gusau 07033565999
Kukanmu ga Gwamna el-Rufa’i

Ina rokon jaridar Aminiya da ta mika kukanmu ga Maigirma Gwamnan Jiharmu ta Kaduna. Mu al’ummar Kristocin karamar Hukumar Soba, an hana mu shaidar ‘’yan asalin karamar hukuma (Indigene Form), saboda nuna wariya ta Addini. Mun bi matakai na lumana, amma har yanzu haka ba ta cimma ruwa ba. (1).Mun zauna da kantoman bai ba mu magana ta kirki ba. (2) Mun zauna da Maimartaba Sarkin Zazzau, ya ce zai bincika. Shi ma har yanzu babu labari mai dadi.To mu fa ’yan Najeriya ne. In kuwa an ce ba za a bamu ba, to Gwamnatin Jihar Kaduna, da na karamar Hukumar Soba su zo, su sake man wata kasar.
Daga Rabaran, Ya’u Magaji Unguwar Sarki Yakubu Kwasallo.   08067906144.
Kira ga ’yan fim

Salam Edita. Barka da rana. Ya aiki? Bayan haka, don Allah ina so ka mika min kira na ga ‘’yan Fim din Hausa Da ya kamata su rika gyara Fim kafin ya fito. Domin kiyaye hakkin Allah da na iyayen yara. Nagode.
Daga Aminin Aminiya, Musa Na Musa Pz 0703125910
Kira ga Gwamna Masari

Zuwa ga Edita. Bayan gaisuwa mai yawa da fatan alkhairi, Allah ya sa haka amin. Bayan haka  ina so a ba ni dama domin in mika kukan mutanen Daura ga  Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari. Muna rokon maigirma don Allah a taimake mu a gyara mana mayankar dabbobi ta Daura, saboda ba mu da isasshen ruwa, kuma mayankar ba ta da rufi ga plaster kasa, inda muke aikin nama, duk ya lalace. Don haka muna roko gareka ya maigirma gwamna a gyara mana. Mu ma a yi mana irin ta zamani. Babu  abin da ya fi ci mana tuwo a kwarya, sai wannan rashin rufi. Muna fatan Allah ya ba ka ikon yi. Amin.  Daga Hadi Tsohon Sarki Daura 08148442241   08085127726
Kira ga Gwamna Kano

Salam Edita. Ina son isar da sakona zuwa ga Gwamna Kano, Allah ya kara jagoranci  amin. Don Allah gwamna raya karkara akwai hanyar da tashi daga Bich zuwa Komau, ta nufi kauyan Gawu ta wuce daddarawa ta wuce ’Yanmamma. Mutanen  kewayen na fama da rashin hanya na tsawon lokaci ana auna ta, amma har yanzu babu labara. A taimake mu Ganduje Allah ya kara ma lafiya da jagoranci mai alfanu.
Daga  Aliyu Sani karamar Hukumar Tsanyawa, a mazabar daddarawa 08058027785.
Kukanmu ga Gwamna Bindow

Salamu alaikum Aminya. Ina son ku mika kukanmu ’yan Adamawa wajen Gwamna Bindow mu ba mu ga canji ba har yanzu kuma muna son gani a kasa in ba haka ba 2019 kamar gobe ne. Daga dahiru Umaru Abubakar Mubi South.07016020420
Kira ga Malaman Jihar Kaduna

Salam Edita. Barka da aiki, ya hakuri da mu? Ina so don Allah ka ba ni fili in yi kira ga malaman makaranta, musamman ma na Jihar Kaduna da su daina yi wa dalibai wulakanci, domin hakan bai dace ba. Ko da dai ilimi kyauta ne (Free Education) ne ai Gwamna Malam Nasir el -Rufa’i. ai bai ce da dalibi ya yi dan laifi kadan a koro shi ba; saboda ana ganin ba kudi yake biya ba. Don haka ina fatan in sun ji za su gyara, tunda ana biyan su albashinsu, yadda y akamata, su ma dalibai ya kamata a ba su kulawa, yadda ya kamata.
Daga dayyabu Isah Soba, Shugaban kare hakkin ’yan makaranta 08160118035.
Tambaya ga Gwamnatin Kano

Salam zuwa ga Aminiya. Don Allah ku tambayar mana Gwamnatin Kano shin ’ya’yan Hassan Gwarzo su suka fi ’ya’yan Malam talaka?  Daga dan Bashir Madatai 08103135352.
Jinjina ga Hamid Ali

Jinjina ga Shugaban Hukumar Kwastam Kanar Hamid Ali, muna goyan bayan yaki da cin hanci da rashawa a hukumar kwastam. Duk abin da ya ba ka tsoro, wata rana zai ba ka tausayi.  Daga Babangida Ahmad Jibrin Zango Gwarzo 08141667702.
Bodinga ba mu da kowa a gwamnati

Assalamu alaikum,don Allah Edita ka mika min sakona ga Gwannan Jihar Sakkwata Barista Aminu Waziri Tambawal,ya raba mukammai ya ba Sifawa da Dingyadi, to mu cikin garin Bodinga me za  a ba mu? Halan ka dauka in ka ba Sifawa da Dingyadi mukami ka ba Bodinga.Daga cikin wadannan mutane in ban da garin su.a taimaka mu samu wakilci, ko kuma mu ce Allah Ya bi kadin hakkin mu. Mun gode. Daga Bala Buhari Bodinga.07033155737.
kungiyar asiri ta cutar da yaro

Assalamu alaikum ga  Aminiya barka ku da hidamar jama’a. Don Allah Edita ka ba ni dama in yi kira ga ’yan jami’yyar adawa ta P D P ta Sakkwato ya kamata ku yi maza-maza ku tara kudin da Kanar Sambo ya bai wa Bafarawa, ya ba ku, ka da abin ya kawo Sakkwato. Kuma mu  Sakkwatawa,.  muna   jinjina ga  hukumar EFCC,  saboda yanzu ta fara adalci kai mayaudaran  gwamnati kotu. Don haka Kanar Dasuki da Baffarawa kuwa Allah ku  ba  da kudi mutane  in ba haka ba, to gidan yari tanan  na jiran ku Allah ya agaji ku mutanen P D P  na Bafarawan  sakkwato.  
Daga M. Murtala Amwa. Sakkwato.Kanwuri. nagode.