Akwai gyara a fatawar Sarkin Kano game da Jifar Shaidan
MALAM TUKUR ADAM AL-MANAR, malamin addinin Musulunci ne a Kaduna. Ya yi gyara game da fatawar da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi game da al’amarin Jifar Shaidan. Malamin ya sanya bayanin nasa ne a turakarsa ta Facebook. Muhimmancin bayanin nasa ne ya sanya muka liko shi nan, domin kalubale ga masana da almajiran […]
MALAM TUKUR ADAM AL-MANAR, malamin addinin Musulunci ne a Kaduna. Ya yi gyara game da fatawar da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yi game da al’amarin Jifar Shaidan. Malamin ya sanya bayanin nasa ne a turakarsa ta Facebook. Muhimmancin bayanin nasa ne ya sanya muka liko shi nan, domin kalubale ga masana da almajiran ilimi:
Sakamakon rasa rayukan Alhazai da ya faru bana a Mina, na ji kowa yana fadin albarkacin bakinsa. Daga ciki, na sami sakon bidiyo na mai martaba San Kano, Alhaji Muhammad Sunusi II, (Allah Ya kara masa martaba da daraja, amin).
Mai martaba mutum ne mai tausayi da amana kamar yadda na san shi. Hakan ya sanya shi fadin maganganu kamar haka:
1-Malamai ne suka kallafa wa mutane jifa bayan zawali. 2-Annabi (saw) ya yi rangwame ga masu kiwon rakuma su hada jifar su, su kwana a Makka. 3-Idan Hukumar Saudiyya ba ta canza wa ’yan Afirika shemomi kusa da wajen jifa ba (saboda nisa ke nan), Alhazan Najeriya su rika zama a Makka kwanakin Mina. 4-Ana iya barin jifa a yi yanka a madadinta saboda gudun mutuwa, domin ran Musulmi ya fi rago daraja. 5-Abdullahi dan Umar (ra), an tambaye shi lokacin jifa; ya ce lokacin da shugabanka yake yi. Saboda haka shi mai martaba ya zabi kafin zawali, sai a bi shi. 6-Sannan an tanbayi Annabi (saw) game da kaddamar da dawafi a kan aski ko yanka a kan jifa da sauransu, ya ce ba komai. Kamar wannan hujja ce, a gabatar da jifa kafin zawali ko wani aiki kan wani ko jinkirta wani kan wani.
Fahimtata Kan Al’amarin:
Alhamdu lillah. Tare da girmamawa ga mai martaba sarkinmu, San Kano ga fahimtata kamar haka: 1-Game da jifan Jamratul Akabah ta ran Sallah, ana yi ne bayan fitowan Alfijir har dare amma ita kuma jifar kwanakin tasriki, ana yin ta bayan zawali ne. Haka Annabi (saw) ya yi a aikace kuma ya ce: “Ku yi ayyukan Hajji kamar yadda na yi.” Kuma a wancan lokacin akwai zafin rana mai tsanani, ba ruwan sha, ba shemomi irin na yanzu da na’urar sanyaya dakuna, ba mota kuma daga Madina sai an yi tafiya ta kusan kwana goma kan rakuma da dawakai.
Sannan ba a ce kowa dole ne ya fito da zaran zawalin ya yi ba, a’a, ana nufin lokacin fara jifar, bayan zawali har bayan Isha.
2-Rangwamen da Annabi (saw) ya yi na hada jifa ba kowa da kowa ba ne, masu kiwo ne da masu shayar da Alhazai ruwa, kamar yadda aka yi sauki ga tsofaffi da mata da yara da masu rakiyar su, su baro Muzdalifa bayan rabin dare zuwa Mina don jifa saboda lalura da ta shafe su. Yanzu kuma ana son kowa ne Alhaji ne zai yi hakan ba tare da bambancewa ba.
3-Nisan shemomin Alhazan Afirika ba shi ba ne ya haddasa mutuwar nan, asali ma su fararen fatar da suke kusa da wajen ne ma suka fi mutuwa. Sannan idan duka Alhazanmu suka koma da zama Makka ma, ai dole za su fito jifar, su hadu da fararen fatan. To, ashe ba ta canza zani ba ke nan.
4-Tabbas ran mumini ya fi duk wani abu a duniyar nan daraja, ba ma rago kawai ba, duk da hakan jifar nan, Allah Ya nema a yi a Jamrah, ba nama Ya nema a wajen ba. Mutum ba ya barin asalin abin da aka nema daga gare shi wanda shi ne Azimah, ya yi riko da Rukhsa, ba tare da wata lalura ba. Ko ma da da lalurar, to sharia ce za ta kaddara ta.
Sannan Aikin Hajji ibada ce mai nau’i kala-kala: dawafi, Sa’ayi, Kwannan Mina, Tsayuwar Arfah, Kwannan Muzdalifa, Jifa, Yankan Raguna da Aski. Kowanne da muhallinsa, don haka bai kamata a musanya wani da wani ba. Shi yankan rago a matsayin jifa ai karya doka ne, kaffarar laifin rashin jifar ne. Ko da akwai lalura da za ta hana wani yin jifa, ai ana wakilci. Shi Allah da Ya shar’anta jifar, ai Ya san da akwai ragon; a inda Ya nemi rago sai a yanka, a inda ya nemi jifa kuwa sai a yi jifar.
5-Shi hadisin Abdullahi bin Umar (ra) da aka tambaye shi game da jifa, ya ce lokacin da shugabanka ya yi kai ma ka yi. Wannan fatawar Sahabi ce, ba za ta ture tabbatacciyar Sunnah aikatacciya ta Annabi (saw) ba da ya yi jifa bayan zawali. Sannan a lura, lokacin Amirul Hajjin duniyar Musulmi daya ne ba kamar yanzu yadda kowace kasa take da nata Amirul Hajji ba.
Sannan ya fada wa mai fatawa ne haka domin ammi ne kuma ya san shugaban nasa ba zai saba wa Sunnar Annabi (saw) ba, ko kuma don tsoron fitina ga saba wa shugaba da abin da zai kai shi ga azabtarwa ko rasa rai.
Amma yanzu wani Sarki ya fito ya ce zai jagoranci Alhazai wajen aikata wani abu, sabanin yadda Annabi (saw) ya yi, sai mu ce masa babu da’a ga wanda ya saba wa Mahalicci ko Shari’a.
5-Abubuwan da aka tambayi Annabi (saw) su ne ayyukan da ake yi ranar 10 ga watan Hajji ne kawai kuma su hudu ne, Jifar Jamratul Akabah da Yanka Hadaya da Aski da da dawaful Ifadha. Duk wanda aka gabatar a kan wani ko jinkirtawa, Annabi (saw) ya ce babu laifi, domin haka ya bayyana a hadisi.
6-Sannan idan an samu sadanin Sahabbai da Tabi’ai da Malamai a kan lokacin jifa, to a bar nasun mana a tsaya kan na Annabi (saw) da ayyukansa, kamar yadda Allah Ya ce: “Ku yi wa Allah biyayya, ku yi wa Manzo biyayya da shugabanni ko malamai… idan kun yi jayayya kan wani abu, ku maida shi zuwa ga Allah da ManzonSa kawai.”
Annabi (saw) ya ce: “Na bar muku abubuwa biyu, matukar kuka yi riko da su, ba za ku bace ba, littafin Allah da Sunnata.”
Ga Wasu Tambayoyi Domin Tsokaci:
1-Ni kam wai mutuwar Mina ce kawai mutuwa? Ba a mutu cikin Ka’aba ba? Shin ya za a yi a kauce wa mutuwa, a daina zuwa Haramin ke nan?
2-Idan ana ganin yawan Alhazai ne ke haddasa mutuwa, me ya sa ba za a kawo shawarar rage ko kayyade yawan Alhazai na kowace kasa ba, maimakon barin wasu daga cikin ayyukan Hajjin? A kuma yi kokarin tarbiyyantar da Alhazai a kan da’a da bin tsari, domin wani abun su suke haddasa shi don zakuwa. A koya masu shiga layin hawa mota, jirgi, rabon abinci, da sauransu, inda za ka ga ana yiin ture-ture. A nan gida Najeriya ma, ana mutuwa wajen layin karbar zakka da sauransu.
3-Mene ne ke hana dan Najeriya yin wanka da sanya Ihrami daga gida ranar tashi zuwa Hajji, tun da ana sanar da Mikati cikin jirgi; alhali duk sauran Alhazan wasu kasashe da ke biyowa ta Jidda, suna sauka da Ihraminsu? Shin Haramin wahala ne da shi ko kuma jin kunya ne? In dai wahala ne na awa hudu cikin jirgi da AC, to mene ne bambancin awoyi da ake yi sanye da shi daga Madina zuwa Makka a mota? Sannan kwana nawa ake yi da shi daga fita Mina zuwa ranar Sallah? Kwana uku ake yi, duk wannan ba a ganin gandar jure masa, sai na awa hudu zuwa biyar kuma a jirgi? Da ma mu kyuya da ganda da neman sauki a inda saukin bai kama ba shi ne dabi’armu.
4-Shin irin barnar rayukan da bama-bamai suka haddasa a masallatan Juma’anmu har na Kano da kasuwanninmu da tashoshin mota sun taba hana Musulmi zuwa Juma’a ko kasuwa ko tashar mota? Ko an taba ba da fatawar cewa kowa ya yi Sallarsa a gida?
5-Shin a kowace shekara ce ake mutuwa a Hajji?
6-Sannan ana ganin idan aka dauki wadancan matakan, shi ke nan ba a sake mutuwa a Hajji ke nan?
Daga karshe, ina jawo jankali da cewa Musulunci ba tsarin dan Adam ba ne da duk lokacin da ya motsa kawai ya ce a canza nan a canza can. A yi hattara da yi wa Shari’a kutse.