Akwai gyara a maganar Mai martaba Sarki

A makon jiya ne Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi na II ya bayyana ra’ayinsa a karo na farko game da yaran da aka sace a Kano amma aka gano su a Jihar Anambra bayan an sauya musu addini da sunaye, inda ya nuna cewa da a ce shi ne zai yanke hukunci da iyayen […]

Akwai gyara a maganar Mai martaba Sarki

A makon jiya ne Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi na II ya bayyana ra’ayinsa a karo na farko game da yaran da aka sace a Kano amma aka gano su a Jihar Anambra bayan an sauya musu addini da sunaye, inda ya nuna cewa da a ce shi ne zai yanke hukunci da iyayen yaran da aka sace ’ya’yan nasu zai sanya a daure su a gidan yari saboda laifin yin sakaci da ’ya’yansu.

Mai martaba Sarki Sunusi ya kara da cewa lokacin da ya samu labarin gano yaran ya so ya tambayi ’yan sanda ko akwai wata doka da ta tanadi hukuncin da za a yanke wa iyayen da suka yi sakaci da ’ya’yansu domin a hukunta iyayen yaran da aka gano ’ya’yansu a Jihar Anambra? A ganin Mai martaba Sarkin Kano laifin iyaye ne da suka yi sakaci da ’ya’yansu har suka bari ’yan kabilar Ibo suka sace su.

Sai dai kuma duk da haka Mai martaba Sarki ya ce ya yi magana da Obi na Anacha game da batun sace yaran, kodayake bai bayyana abin da ya fada wa Obi na Anachan ba, shin ya nuna damuwarsa ce game da sace ’ya’yan talakawansa da Ibo suka yi, ko kuwa ya yaba ne da abin da Ibon suka yi domin daidaita sahun talakawansa da ke Kano?

Mutane da dama na ganin Mai martaba Sarkin ya yi kuskure a maganarsa, domin yaran nan da aka sace ba an tura su yawon bara ba ne, makarantar Islamiyya suke zuwa, wadanda mafi yawa a kusa da gida makarantun suke, a kan hanyarsu ta zuwa makaranta ko komawa ake sace su, ko kuma idan suna wasa a kofar gida, tunda yanzu mafi yawan gidaje ba su da yalwa kamar gidaje irin na da wadanda ke da sararin da yara za su iya yin gararamba da sauran wasanni a cikin gida ba tare da sun fito kofar gida ba.

Toi idan za a kama iyayen, shin da maigida da uwargida za a kama ko kuwa uwargida kawai? Domin sanin kowa ne cewa a Kano magidanta da dama idan suka fita tun safe zuwa neman abinci sai dare suke komawa, wadansu kuma barin garin suke yi sai a karshen mako suke komawa gidajensu, wadansu kuma sai wata ya kare iyalinsu za su gansu, wadansu ma ba su komawa wurin iyalinsu sai bayan shekara, iyaye mata ake bari a gida tare da yara.

A nan za a iya cewa ke nan Mai martaba yana ganin magidantan da ke barin Kano su tafi fatauci wasu garuruwan domin neman halaliya sun aikata laifin sakaci ke nan?

Wannan bayani da Mai martaba ya yi sai ya nuna kamar dai bai damu da sace yaran da aka yi ba ne, laifin mutanensa kawai yake gani,  domin a lokacin da wani matashi dan Jihar Kano mai suna Yunusa Yellow da ke zaune a Jihar Bayelsa ya je Kano da wata yarinya da ita da kanta ta amince ta bi shi Kano domin ta musulunta kuma ta aure shi, wannan yaron Mai martaba Sarki shi ya bai wa laifi shi kadai, aka kama yaron a wulakance aka koma da shi Jihar Bayelsa har yanzu yana daure a gidan yari fiye da shekara biyu da suka gabata. Ita kuwa yarinyar tana can tana harkokinta tunda ’yan uwanta sun tsaya mata.

Masu iya magana suna cewa, idan dan uwanka ya fada cikin masifa kokari za ka yi ka ceto shi, ba zarginsa za ka tsaya yi ba, domin a wannan lokaci zargin ba zai yi masa amfani ba, bayan ka ceto shi ne sai ka zaunar da shi ka nuna masa kuskurensa, a wannan lokacin ne zai gane nasihar da kake yi masa.

Amma iyaye sun rasa ’ya’yansu maimakon a yi musu jaje, sai aka koma ana cewa sakacinsu ne, wannan nasihar ba za ta yi musu amfani ba.

Kamata ya yi idan har Mai martaba Sarkin Kano yana ganin laifin iyaye ne da suka yi sakaci har ake sace masu yara, kafin ya fadi haka kamata ya yi ya fito ya nuna damuwarsa game da abin da ya faru, ya kuma yi kokarin ganin an gano sauran yaran da aka sace, daga nan sai ya jawo hankalin iyaye game da bukatar da ke akwai ta su kara kulawa da yaransu domin yanzu zamani ya canja ga irin abin da ke faruwa.

Yana iya tsawatarwa tare da gargadin iyaye cewa nan gaba duk wanda ya yi sakaci aka sace dansa, musamman iyaye mata da za su bari yaro karami ya fita kofar gida ba tare da sun kula ba, za a hukunta su.

Amma mutum ya fada cikin masifa maimakon wadanda yake zaton nasa ne su taimaka masa sai suka koma su ne suke zarginsa, yana iya tuburewa, domin zai dauka ba a kaunarsa ne. Shin da wanne zai ji, da bala’in da ya fada ciki ko da zarginsa da ’yan uwansa suke yi masa?

Irin yadda shugabannin Arewa suke magana a kan wasu al’amura da ke tasowa shi ne yake sanyawa wadansu mutanen suke ganin kamar shugabannin Arewa suna jin tsoron bata wa ’yan Kudu da sauran shugabanni duniya rai ne, shi ya sanya a kullum suke munana wa nasu domin su dadada wa wadancan mutanen rai.

Hausawa suna cewa, “Ka ki naka duniya ta so shi, ka so naka duniya ta ki shi.” Amma ba a kowane lokaci ne wannan maganar take gaskiya ba, wani lokaci dole sai ka rufe ido ka nuna kana son naka sannan za a zauna lafiya.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos