Akwai hadin kai tsakanin ’yan Arewa da ’yan Neja-Dalta – Shugaban Karar Agbor
Alhaji Yunusa Jidda Shugaban karan Shanu na Agbor ya yi bayani akan abin da yake ganin kyakkyawar alaka ce da hadin kai tsakanin ’yan Arewa da ‘yan kabilun jihar Delta, Alhaji Jiddah ya fadi hakan ne a cikin wata hira da wakilin Aminiya a makon jiya a garin Agbor. ‘’Mu al’ummar Arewa ’yan kasuwa masu […]
Alhaji Yunusa Jidda Shugaban karan Shanu na Agbor ya yi bayani akan abin da yake ganin kyakkyawar alaka ce da hadin kai tsakanin ’yan Arewa da ‘yan kabilun jihar Delta, Alhaji Jiddah ya fadi hakan ne a cikin wata hira da wakilin Aminiya a makon jiya a garin Agbor.
‘’Mu al’ummar Arewa ’yan kasuwa masu sayar da dabbobi na nan garin Agbor , muna kara samun hadin kai tsakaninmu da ‘yan kabilun wannan jihar, musamman tsakaninmu da abokan huldar mu na kasuwancin. Kkuma da Shugabanni na nan garin da na gwamnatin jihar , wannan ya ba mu damar tafiyar da harkokinmu cikin kwanciyar hankali,” inji shi.
Alhaji Jiddah ya kara da ce wa , ina ganin ya kamata mu rika tuntubar juna akan abin da ya shafi harkokin kasuwanci da sauran al’amuran da suka danganci bangaren zaman lafiya, inda ya ci gaba da cewa, mu a zamanmu a nan muna nisanta kanmu daga duk wata hanyar fitina, domin mu samu dorewar zaman lafiyarmu da al’ummar mu .
Ya ce abin da ya shafi batun manoma da masu dabbobi a nan jihar, akwai fahimtar juna tsakaninmu mu masu dabbobin da kungiyar manoman jihar, don haka a duk lokacin da aka samu wani kuskure na barnar gona, to lallai mu shugabanni muna tashi tsaye, mu tabbatar da mun bi ma masu gona kadin hakinsu. Sannan ya fadi wasu matakan da kungiyarsu ta ’yan kasuwa ta dauka , inda ya ce: “Muna yin tarukan tattaunawa a kowane karshen mako da kuma na wata, inda mukan tattauna a kan muhimman batutuwa. A cewarsa, muna yin irin wadannan tarukan ne mu shagabanni , tare da jama’armu da ‘yan kasuwa da manoma, domin tattauna batutuwa da suka shafi ko wani bangare.
Alhaji Jiddah ya karkare da cewa mu shugabannin a duk lokaci muna tara jama’ar mu domin fadakar da su.
‘’Muna fadakar da al’ummar mu da wayar da kansu akan muhimmancin hadin kai da zaman lafiya da yin hakuri da juna.,” inji shi.