Akwai harsunan da za su bace a karshen karni na 21 – Masana
Masana a fannin Kimiyyar Harsuna sun yi tsokacin yiwuwar durkushewa da kuma bacewar wadansu harsunan duniya a karshen karni na 21 muddin ba a dauki kwararan matakan dakile faruwar hakan ba.Sun yi wannan tsokacin ne a lokacin da aka gudanar taron tunawa da Marigayi Farfesa MKM Galadanci a Jami’ar Bayero da ke Kano a makon […]
Masana a fannin Kimiyyar Harsuna sun yi tsokacin yiwuwar durkushewa da kuma bacewar wadansu harsunan duniya a karshen karni na 21 muddin ba a dauki kwararan matakan dakile faruwar hakan ba.
Sun yi wannan tsokacin ne a lokacin da aka gudanar taron tunawa da Marigayi Farfesa MKM Galadanci a Jami’ar Bayero da ke Kano a makon jiya.
Makasudin taron shi ne don yi nazari a kan yaduwar harsuna da kuma alamun durkushewa da kuma bacewar wasu harsunan a duniya.
Akwai harsunan da suke fuskantar barazanar bacewa ko durkushewa a duka nahiyoyin duniya da suka hada da Turai da Afirka da Asiya da Amurka ta Kudu da ta Arewa da Gabas ta Tsakiya da sauransu.
Sashin Kimiyyar Harsuna da ke Jami’ar Bayero ta Kano ne ya dauki nauyin shirya taron.
A lokacin bikin bude taron, Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed, ya ce an shirya taron a karo na farko ne don a ba masana dama su baje-kolin nazarce-nazarcensu a kan yaduwa da bacewar wadansu harsuna tare da kawo mafita daga lamarin.
Ya dora alhakin lalacewar kananan harsunan ne sakamakon mamaye su da manyan harsuna suka yi, inda ya ce hakan ya faru ne dalilin zamananci da kuma mulkin mallaka.
Wasu dalilan kuwa ya ce sun hada da daukaka wasu harsuna a kan wasu da hukumomi da gwamnatoci suke yi.
Shi kuma a tasa mukalar, mai taken ‘Yawaitar harsuna da barazanar durkushewar harsuna’, Shugaban Sashen Kimiyyar Harsuna na Jami’ar, Farfesa Mukhtari A. Yusuf, ya ce, yawaitar harsuna a rayuwar dan Adam a duniya ya zama abin bai wa muhimmancin gaske, saboda samun barazanar durkushewa da wasu harsunan ke fuskanta dalilin mamayar da manyan harsuna suke yi musu.”
“A bisa dalilin barazanar da harsunan suke samu ne, a shekarar 1992 Hukumar Majalisar dinkin Duniya ta UNESCO ta kafa kwamiti na musamman don nazarin barazanar bacewar wasu harsuna a duniya, tare da samar da wani kundi na musamman da ya kunshi hanyoyin habaka irin wadannan harsunan, tare da kuma samar musu kariya daga durkushewa.”
Shi kuwa a tasa makalar mai taken “Dakile hanyoyin bacewar da durkushewar harsuna a Najeriya ta hanyar bincike,” Daraktan Tsara Manhajar Karatu na Cibiyar Binciken Ilimi ta Najeriya (NERDC) da ke Abuja, Farfesa Ismail Junaidu ya ce, “kodayake batun bacewar harsuna abu ne da ya shafi duniya, sai dai kuma matsalar ta bayyana ta kowane mataki tare da barazana ga harsunan Najeriya, inda ya ce tuni masana suke ta kokarin nusar da gwamnatoci da cibiyoyi da kungiyoyin da abin ya shafa, don daukar matakan da suka hada da yin dokokin gwamnati, don amfani da harsunan a bangaren magana da rubutu da kuma tantance dokoki da ka’idojin nahawun magana da na rubutunsu.”
Ya karkasa matakan karfin harsuna zuwa kashi 3, kaso na farko farko ya kunshi harsuna masu karfi, na tsakiya masu dan rauni, da na karshe wadanda nan ba da jimawa ba suna iya bacewa saboda wasu dalilai da suka hada da: karancin masu aiki da wadannan harsunan tare da mamayar da wasu harsuna suka yi musu da kuma sakaci na al’ummar da suka gaji wadannan harsunan suka yi.
Ya ce: “Misalin harsuna masu karfi a Najeriya sun hada da Hausa da Yarabanci da Ibo; na tsakiya sun hada da Igala da Urhobo da Ibibio da Anang da Angas. Na karshe sun hada da berre da Bokyi da Ninzom da Kilba da Higgi da sauransu.
A taron na yini biyu masana kimiyyar harsuna daga jami’o’i da manyan makarantu na sassa daban-daban na Najeriya da cibiyoyi daban-daban sun gabatar da makaloli masu take daban-daban a kan fannonin bincike daban-daban.
Masanan sun shawarci gwamnatoci da duk masu ruwa da tsaki da su dukufa wajen kare harsunansu daga durkushewa ko bacewa gaba daya.