Akwai kamanceceniya tsakanin Masarautar Kano da ta Ingila —Nasir Khalil
A Masarautar Kano kuma da mata da maza wajen gaisuwa duk daya ne, wato ana dukawa ce.
Daraktan Bincike da Fasahar Sadarwa a Kotun Daukaka Kara ta Shari’ar Musulunci da ke Kano kuma dalibi kan abubuwan da suka shafi masarautu da harkar sarauta, Malam Nasir Wada Khalil ya bayyana cewa akwai kamanceceniya a tsakanin Masarautar Ingila da Masarautar Kano.
Malam Nasir Wada Khalil ya bayyana haka ne, a lokacin da yake zantawa da Aminiya.
Ya ce misali a al’adance idan Sarki ko Sarauniyar Ingila tana tafiya. Idan Sarauniya ce mijinta a ’ya’yanta da kowa, bayanta zai bi.
Haka idan sarki yana tafiya, kowa bayansa zai bi. Sai wanda aka saka, don ya gyara hanya, ba wai don sarki ya bi shi a baya ba.
Ya ce irin wannan tafiya, yadda ake yi a masarautar Ingila ke nan, haka ma ake yi a Masarautar Kano.
Ya ce haka kuma gaisuwa idan za a yi wa sarauniyar Ingila gaisuwa, maza suna dukawa ne mata kuma suna rankwafawa ne kamar za su yi durkuso.
A Masarautar Kano kuma da mata da maza wajen gaisuwa duk daya ne, wato ana dukawa ce.
Ya ce sannan idan Sarkin Ingila ko Sarauniyar Ingila, ta shiga wuri to dole ne kowa sai ya mike.
Haka a Masarautar Kano ma, duk inda Sarki ya shiga, dole ne kowa ya mike, sai dai idan mutum ba zai iya tashi ba.
“Sannan akwai tsari na shiga, ba kowace shiga ce ’ya’yan Sarki zasu yi ba, balle Sarki ko Sarauniya.
“Haka yake a Masarautar Kano, misali marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, bai taba zuwa fada da babbar riga mai munduwa ba. Bai kuma taba yin hawa da ita ba.
“Ko dan sarki ko hakimi idan zai fita, ko ba zai yi nadi ba, zai kawo wani dan hirami ya sanya a kafadarsa.”
Malam Nasir Wada Khalil ya yi bayanin cewa sarakuna ba sa nuna bangare a siyasa a Masarautar Kano, haka abin yake a Masarautar Ingila.
Wannan doka ce a Masarautar Kano haka su ma doka ce, a Masarautar Ingila.
Ya ce idan sarauniya ko sarki ya tashi a Ingila, dole kowa ya tashi haka yake a Masarautar Kano.
Ya ce idan sarauniya ta gama cin abinci, ko sarki ya gama cin abinci, dole ne kowa ya dakata ko mutum bai koshi ba, haka yake a Masarautar Kano.
Shi ya sa a Masarautar Kano, ake da wani tsari na sai Sarki ya gama cin abinci, sannan ake bai wa abokan tafiyarsa.