Akwai kulalliya wajen rabon katin zabe
Edita don Allah ka ba ni dama in yi tsokaci dangane da yadda ake bada katin zabe a Kano.Tabbas akwai matukar mamaki ganin yadda jama’a suka bata lokacinsu a lokacin karbar katin, amma abin takaici sai ga shi mutane da dama ba su ga katinsu ba. Wata sabuwa kuwa duk da sanarwar da hukumar ta […]
Edita don Allah ka ba ni dama in yi tsokaci dangane da yadda ake bada katin zabe a Kano.Tabbas akwai matukar mamaki ganin yadda jama’a suka bata lokacinsu a lokacin karbar katin, amma abin takaici sai ga shi mutane da dama ba su ga katinsu ba. Wata sabuwa kuwa duk da sanarwar da hukumar ta yi, na yi wa mutane sabon katin; sai ga shi an koma gidan jiya, ta inda hukumar ta yi amfani da na’urar yi wa mutane, wato guda daya a kowacce mazaba. Hakan yasa mutane da dama sun kasa daurewa wajen gwagwarmayar karbar sabon katin. Abin tambaya anya kuwa babu wata kullaliya kuwa wajen mallakar katin? Daga Aminu Abdu Baka noma Sani mai nagge Kano 08099479880.
Jinjina ga Aminiya
Edita ina jinjina wa Aminiya. Ina yi muku fatan alheri. Allah Ya kara basira, ku ci gaba da ruwaito mana labarai masu nagarta, don kyautata zamantakewa da tattalin arzikin kasa da siyasa, ta yadda za a samu shugabanci nagari. Daga [email protected]
A yi koyi da Sarkin Kano
Edita masu iya magana na cewa: “Idan hagu ta ki, sai a koma“. Hakika maganar mai martaba Sarki abin dubawa ce sosai. Dole sai mu jama‘a mu tashi a tsaye mu kawar da tsoro da zukatanmu, domin ta hakane za mu samarwa unguwanninmu, da garuruwanmu mafita, daga harin ‘yan ta‘adda. Domin Hausawa na cewa: “jin Tsoron marar kunya, tsoro ne“. Da wannan nake kira ga: Sauran sarakunanmu na Arewa da su yi koyi da Mai martaba Sarkin Kano, wajen fadakar da jama’a. Allah ya yi mana maganin duk wani mutum, ko wata kungiya da ke tayar mana da hankula a yankinmu na Arewacin Najeriya. Daga Isah Ramin Hudu, Hadejia. 08060353382
Hukumar zabe ta gaza
Edita Hukumar zabe ta INEC, ta nuna gazawar ta a fili na rashin iya gudanarwa, da rashin kyakkyawan tsari a raba rijistar zabe ta dindindin (Permanent botersCard) da hukumar ta yi a Jihar Kano. Hakan ya sanya shakku a zukatan ’yan Najeriya da duniya baki daya. Duk da yawan da mutanen Jihar Kano ke da shi, in har hukumar zabe ta INEC ba ta magance irin wadannan matsalolin ba, ba makawa sahihin zabe da hukumar ke ikirari a 2015 ba zai yiwu ba.
Daga Mansoor Said PRP, Kano. 07039215954.
Tsokacin dokar ta-baci
Salam Edita. Don Allah ka ba ni dama in yi tsokaci akan dokar tabaci da ake so a kara mana a jihohinmu na Borno da Yobe da Adamawa. To wallahi za mu kalubalanci majalisar tsaro ta koli, da ma gwamnati, ko da ta hanyar bore ne. Ina kuma mika ta’aziyya ga iyayen daliban da suka rasa rayukansu a harin bom da aka kai Potiskum Daga Muhammad Garba Sabiola Sa’idawa Gashuwa 08096284154.
A dubi ’yan gudun hijira
A gaskiya Gwamnatin Najeriya ya kamata ki taimaka wa ‘yan gudun hijira da ke iyakar Kamaru da ma wadanda harin Mubi ya shafa. Saboda suna cikin wani mayuwacin hali sosai. Akwai karancin abinci da kuma magunguna. Don haka fatana Gwamnatin Najeriya ta duba wannan batun, don yana da matukar mahimmanci. Daga Sunusi London Boy Damaturu.08091735162
Ga Ahmad Garban Bichi
Assalamu alaikum Aminiya, ku mika mini gaisuwa ga Ahmad Garban Bichi, gwamnan gobe da kuma Kwankwaso shugaban kasa mai jiran gado da karfin Allah.
Daga Muhammadu Inuwa Kano, 08059718000
Ga Gwamnatin Jigawa
Muna rokon Gwannati JiharJigawa da ta taimaka ta saya mana na’urorin Kwamfuta 150,domin samun yin jarabawar JAMB cikin kwanciyar hakali. Saboda a gaskiya wuraren jarabawabiyu ne, sun kuma yi mana kadan. Dutse da Kazaure ba za su iya daukar yawan jama’a kamar 13,000 a wadannan wurare biyu. Shi ne muke neman alfarma da abude mana wasu wuraren, a masarautun Hadejia da Gumel da Ringim, domin samun sassauci wajen tafiye-tafiye. Allah yasa a amsa mana rokon mu Ameen. Daga Abubakar Garba Ubali Hadejia (TUKURA).
2015: ga fari da baki
Edita ina kira ga ‘yan Najeriya mu yi amfani da hankalin da Allah ya yi muna wajen bambancewa tsakanin fari da baki, shin, Shugaba Jonathan masoyinmu ne da ya cancanci ya ci gaba da jagorancinmu, har ya maimaita ko akasin hakan.Muna rokon Allah ya kawo mana zaman lafiya a kasar mu Najeriya da ma Afirka baki daya.
Daga Abdulmalik Saidu Maibiredi Tashar Bagu, Gusau. 08069807496.
Allah ya yi mana magani
Edita hakika kasar mu na bukatar taimako ganin yadda rikici da son kai yake neman mamaye yankin Arewa saboda rashin adalcin shugabannin mu na Najeriya, wanda yau ya kaimu ga ba mu da kowa sai Allah, amma kuma duk da haka su ’yan siyasa duk wannan abun bai dame su ba, sai neman madafun ikon yadda za su koma Abuja, su ci gaba da zama, kamar yadda suka saba. Saboda haka ina kira ga talakawan Najeriya da su koma ga Allah, domin shi ne Mai komai, kuma shi ke da maganin komai. Don haka wani dan siyasa ba zai iya kawo mana canji da zaman lafiya, ba a cikin kasa sai da yardar Ubangiji. Mun yi tawakkali ga Allah, in sha Allahu zai kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya baki daya. Daga Usman Adamu Aliero Najeriya 07061594299.
Ga Gwamnatin Yobe
Aminiya don Allah ku isar min da wannan kira nawa zuwa ga Gwamnatin Jihar Yobe da cewa, su ji tsoron Allah, su kuma tausaya wa daliban makarantun gaba da sakandire da ke makarantu daban-daban a jihar, su biyasu kuddinsu na tallafihn karatu (scorlarship). Kimanin shekara biyu zuwa uku ke nan ba a bai wa dalibai wannan kudi ba. Kuma hakan ya yi matukar shafar karatu da walwalarsu . Da fatan gwamnati za ta duba wannan kira nawa da idon basira, ta kuma dauki matakin da ya dace cikin hanzari. Daga Usman bin Affan Damaturu 08038001563.\
Darasi ga kasashen Afirka
Fata nagari lamiri ba komai ba ne yasa na fara da wannan kalami ba, sai Yadda shugabanin kasashen Afirka ke maida Mulki gado. A kwanan nan ne talakawan Burkina Faso suka gudanar da zanga -zangar juyin-juya hali, har ta kai ga sauke shugaban kasar Blaise Compaore. Tur da mulkin malaka’u da shugabannin Afirka ke yi wa al’ummar su da fatan za su gyara halayensu, don talakawa su bi su sawu da kafa. A karshe muna addu’ar Allah Yasa taron kungiyar AU, na kwamitin tsaro, ya zama alheri a kasashen Afirka baki daya amin. Daga Alhaji Umar Foreber,Gashua 07089404010-08108003333
Ga Gwamnatin Jihar Kebbi
Assalamu alaikum Edita. Don Allah ka ba ni dama in isar da sakon zuwa ga Gwamnatin Jihar Kebbi, wadda ke kula da abincin makarantun sakandare, cewa wai ina aka kwana kan batun biyan kudin abinci da malamman ke binsu tsawon wata tara? Ina rokon gwamnatin jiha don Allah ta taimaka ta biya wadannan malammai Saboda wallahi wadansun su sun fara shiga wani hali . Ya kamata gwamnati kiyi koyi da wadda kika gada wajen biyan kudin abinci ina rokon Allah yasa a share musu hawayen su amin. Daga Nasiru Musa Maiyama, Jihar Kebbi. 08062206733/08084151555.
Ga ’yan majalisar kasa
Salam Aminiya. Don Allah ku isar mini da sako zuwa ga ’yan Majalisar Najeriya da ma dukkan Gwamnonin na PDP dama APC, wanda suke cikin kungiyar gwamnoni 19 na Arewa, cewa wallahi mu talakawan Arewa ba za mu lamunta ba, in har ba su dauki mataki akan kashe-kashen da ake yi wa ’yan Arewa ba, a kashe mutane, a kore su daga garuruwan su. Talakawa sun zama ’yan gudun hijira, yau har sarakunan mu ma wasu sun zama ’yan gudun hijra, har gobe ba mu ga me Gwamnoni da sanatoci da wakilan mu a abuja suke yi ba
Daga Ahmadu Manager Anguwan Karofin Madaki, Bauchi.08065189242.