Akwai kura-kurai a kalaman Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Mai kowa Mai komai, Wanda Ya ba ni damar yin wannan  gajeriyar fadakarwa zuwa ga Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II da daukacin masu irin ra’ayinsa game da satar yara da ake ta yi a kwaryar birnin Kano da kuma Najeriya. Sanin kowa ne Allah […]

Akwai kura-kurai a kalaman Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II

Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Mai kowa Mai komai, Wanda Ya ba ni damar yin wannan  gajeriyar fadakarwa zuwa ga Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II da daukacin masu irin ra’ayinsa game da satar yara da ake ta yi a kwaryar birnin Kano da kuma Najeriya.

Sanin kowa ne Allah Ya ba wa Mai martaba Sarki baiwar ilimin addini da na zamani. Hakan yana taimaka masa wajen iya gogayya da jama’a a duk fadin duniya. Kuma sau da yawa Sarki yana fadar gaskiya kuma tana yi wa mutane dadi. Amma a wannan jikon Sarki ya yi maganganu masu ban-mamaki da al’ajabi da muke ganin Sarki ya yi tuntuben harshe ba haka ya kamata ya ce ba.

Ko shakka babu,  abubuwa da dama sun faru da Mai martaba Sarki na wajen kasa fahimtar irin ra’ayoyinsa. Sau da yawa mukan yi uwa da makarbiya wajen wayar da kan al’umma. Amma a wannan karo ba ma tare da Sarki. Saboda ya ci karo da tsarin mu’amalar rayuwa da ma koyarwar addinin Musulunci.

Sanin kowa ne Annabi (SAW) yana fada a cikin wani sahihin Hadisi cewa “Musulmi ya fada wa dan uwansa Musulmi magana mai dadi sadaka ce.” Ni na dauka Mai martaba Sarki zai fada musu maganganu masu natsar da zuciya, ba kalaman da za su sa iyayen yara jimami ba.

Mai martaba Sarki ya kamata ya san akwai bambanci tsakanin ’ya’yan talakawa da ’ya’yan masu kudi. A cikin talakawan ’ya’yansu suna zuwa makarantu na boko da Islamiyya. Sau da yawa yaran nan da kansu suke tattaki zuwa wadancan makarantu sabanin abin yadda yake a gidan masu  hannu da shuni.

Zan iya tuno sa’ar da muke yara mu ke zuwa marantar firamare da Islamiyya a kafa, inda muke tafiyar kimanin kilomita shidazuwa da dawowa. Amma tun a lokacin ’ya’yan masu kudi a mota ake kai su. Saboda haka babu yadda shugaba zai zargi iyaye da laifin barin yara suna fita daga gida. Ko kadan yin hakan ba daidai ba ne.

Maganar da Sarki ya yi ka iya tsunduma iyayen yara su hadu da cutar damuwa da tunani (depression), wadda ba karamar illa ba ce a gare su.

Amma ina son mai karatu ya fuskanci zancena ba ina nuna iyayen yara ba su da laifi ba ne. Su ma iyayen yara ya zama dole su kula da ’ya’yan su sosai.

Muna kira ga Mai martaba Sarki ya yi gaggawar ba wa jama’ar Jihar Kano hakuri musamman iyayen yaran da suka salwanta.

Allah Ya bayyana mana su, Allah Ya kiyaye gaba, amin.

Khalid Sunusi Kani  52ND SUG PRESIDENT BUK LEBEL 600 MEDICAL STUDENT (Email: [email protected] <mailto:[email protected]> Phone Number: 07030631259)