Akwai kura-kurai a shari’o’in ta’addanci da ake yi a Najeriya — HRW
Rahoton ya kuma ce a wasu shari’o’in, tuhumar da aka yi wa waɗanda ake zargin ba ta fayyace cikakkun bayanai.
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Human Rights Watch (HRW) ta bayyana damuwa kan shari’o’in ta’addanci da ake yi wa ɗaruruwan mutane a Najeriya, inda take zargin cewa an yanke wa da dama hukunci ne ba tare da isassun hujjoji ba.
A cikin wani rahoto da ta fitar ranar Laraba, ƙungiyar ta ce ta sa ido kan shari’o’in da aka gudanar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a watan Afrilu da Yuni, inda aka gurfanar da fiye da mutum 1,100 a matakai daban-daban.
- Kuɗaɗen ajiyar Najeriya a waje sun ƙaru zuwa biliyan $52.73
- Sanatan Amurka ya sake zargin Najeriya kan muzgunawa Kiristoci
A cewar HRW, an yanke wa mutane da dama hukunci ne bayan sun amsa laifi, ba tare da masu gabatar da ƙara sun gabatar da isassun shaidu ba.
Rahoton ya kuma ce a wasu shari’o’in, tuhumar da aka yi wa waɗanda ake zargin ba ta fayyace cikakkun bayanai, kamar ranar da ake zargin an aikata laifin ko yadda aka aikata shi.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa idan wasu da ake tuhuma sun musanta zarge-zargen, masu gabatar da ƙara kan kasa gabatar da hujjoji, har ma su janye ƙarar.
HRW ta kuma zargi lauyoyin masu kare waɗanda ake tuhuma da rashin gabatar da shaidu ko kiran shaidu a wasu lokuta.
A cewar ƙungiyar, wasu daga cikin mutanen da aka gurfanar sun kasance ne a yankunan da ƙungiyoyin Boko Haram suka mamaye, inda suka yi wasu ababe saboda kawai tsoron kar a kashe su.
Sai dai Daraktan Masu Gabatar da Ƙara na Tarayya ya ce gwamnati na ƙoƙarin yaƙi da ta’addanci tare da kiyaye haƙƙin kowane mutum kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.