Akwai kwange a rahoton binciken rikicinmu da sojoji – ’Yan Shi’a
kungiyar Harkar Musulunci ta ’yan Shi’a mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky ta yi zargin kwange a bahasin da kwamitin binciken da gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa ya fitar game da yadda aka kashe ’ya’yan kungiyar da dama da ake zargin sojoji da aikatawa a garin Zariya a bara. Wani malamin jami’a kuma jigo a kungiyar, Dokta […]
kungiyar Harkar Musulunci ta ’yan Shi’a mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky ta yi zargin kwange a bahasin da kwamitin binciken da gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa ya fitar game da yadda aka kashe ’ya’yan kungiyar da dama da ake zargin sojoji da aikatawa a garin Zariya a bara.
Wani malamin jami’a kuma jigo a kungiyar, Dokta Abdullahi danladi ne ya yi zargin a lokacin da yake bayani a wajen bikin zagayowar Ranar kudus a garin Abuja a ranar Asabar da ta gabata.
Dokta Abdullahi danladi ya ce kwamitin ya iya gano hannun Kwamandan Runduna ta daya a al’amarin amma a lokaci guda ya gaza gano ko shi umarnin wa ya bi a aikata al’amarin. Haka ya ce “Game da tababa a kan ko abin da sojojin suka aikata cika umarni ne na gwamnati, za mu gane matsayar gwamnatin ne gwargwadon yadda ta aiwatar da rahoton binciken, ta hanyar aiwatar da shawarwarin kwamitin ko yin fatali da shi, wannan shi ne zai nuna mana ko ta na da hannu.”
Ya kara da cewa “Muna kira a saki shugabanmu Sheikh Zakzaky don yi masa magani a idonsa da aka lalata, ina mamaki idan za a kai Shugaban kasa waje don yi masa aiki a kunne guda, wane dalili ne shi wanda ya samu matsala a ido ba za a ba da shi ba, don yi masa jinyar da yake tsananin bukata.”
A jawabin da Dokta Abdullahi Bawa Wase ya gabatar a wurin taron ya bayyana ci gaba da tsare malamin a matsayin rashin adalci, bayan kashe masa mambobi da dama ciki har da ’ya’yansa.
Sauran wadanda suka yi jawabi a yayin taron sun hada da tsohon Shugaban Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta kasa, Farfesa Chidi Odinkalu da Daraktan wata kungiyar yaki da cin hanci Honorabul Ebenezar Oyetakin da kakakin wata kungiyar fafutika ta yankin Neja-Delta Mista Bomo Ogo, sai kuma Mukaddashin Jakadan Iran a Najeriya, wadanda dukkansu suka nuna bacin ransu a kan al’amarin tare da kiran a hanzarta sako malamin domin samun cikakken kular likitoci.
An gabatar da wani mahaifi da ya yi jawabi a kan ’ya’yansa da ya rasa a yayin lamarin na Zariya, da kuma wata mai suna Jummai Kankarofi da ita ma ta rasa ’ya’ya biyar sannan ta kubuta da harbin bindiga a bayanta kamar yadda ta bayyana.
Rahoton rikicin da gwamnatin jihar Kaduna ta saki dai ya zargi Sheikh Zakzaky da sojoji da laifi a rikicin. Rahoton ya dora wa jagoran kungiyar Sheikh Zakzaky laifin duk abin da ya faru da ’yan Shi’ar, kamar yadda kafar labarai ta International Centre for Inbestigatibe Reporting (ICiR) ta ruwaito cewa rahoton kwamitin da jaridar New Telegraph ta samu ya ce, Zakzaky ya ki ya umarci mabiyansa su bude hanya ga shugaban sojojin Najeriya Janar Tukur Buratai da ayarinsa a lokacin da ’ya’yan IMN suka rufe hanyar mahadar PZ da ke Zariya, a Jihar Kaduna.
Rahoton mai shafi 295 da babi 15, ya ruwaito Sakataren Gwamnatin Jihar Kaduna yana cewa Gwamna Nasir El- Rufa’i da kansa ya kira Zakzaky ta waya kan “ya sanya almajiransa su bude hanyar amma ya ki.”
Shi ma Daraktan Hukumar DSS na Jihar ya ce, ya tuntubi jami’in Hukumar DSS da ke Hussainiyya Bakiyatillah (hedkwatar ’yan Shi’ar inda aka sanya shingen) a kan ya lallami ’yan Shi’ar su ba shugaban sojojin hanya ya wuce amma suka ki. Ya ce: “Kiyawar shugaban na IMN ya hada kai da hukumomin da suka kamata wajen umartar almajiransa su ba shugaban sojojin hanya abu ne marar dalili da bai dace ba kuma takala ce.”
“Lura da fasalin kungiyar IMN, inda shugabanta ne ke da cikakken iko a kan ’ya’yanta, Sheikh Ibrahim Zakzay ne za a dora wa laifi kan duk abin da ya faru na gazawa ko kuskuren daukacin ’ya’yan kungiyar ta IMN da kuma fadarta da sojoji saboda kiyawar da ya yi ya ja kunnen almajiransa a lokacin da aka bukaci hakan,” inji rahoton.
Sannan rahoton ya soki sojoji kan “amfanin da karfin da ya wuce kima wajen magance lamarin.”
“Hukumar ta lura rundunar sojin Najeriya ba ta bi dokokinta na yaki ba, kuma yadda ta tafiyar da lamarin ya saba wa dokokin duniya wadanda ya kamata a kiyaye wajen gudanar da abin da ya shafi tsaro a cikin gida,” inji rahoton.
Hukumar ta kuma zargi Kwamandan Runduna ta daya ta sojin Najeriya da ke Kaduna Manjo Janar Adeniyi Oyebade kan bayar da umarni da baki ga sojoji su kewaye tare da gudanar da bincike a gidan Zakzaky da kewayensa.f