Akwai lauje cikin nadi a zanga-zangar da aka shirya —Gamji
A cewarsa, sun dawo daga rakiyar zanga-zangar ne bayan jagororin sun shaida masu cewa a jihohin Arewa uku kawai za a yi
Daya daga cikin na gaba-gaba a shirin zanga-zanga da matasa su ka shirya yi a karshen wannan wata a Najeriya, Kwamared Murtala Gamji, ya bayyana dalilin janyewarsa, a yayin da ya rage kasa da mako guda a gudanar da ita.
Kwamared Murtala Gamji wanda har ila yau jagora ne a Kungiyar Matasan Dattawa ta Kasa, ya bayyana dalilan da suka kaurace wa shiga zanga-zangar a tautaunawarsa da Aminiya.
Ya ce shirin zanga-zangan wanda aka fara bayan ta’azzarar farashin kayayyakin masarufi da tsadar rayuwa karkashin Swamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu, ya samu karbuwa wajen wasu manya tare da kara fadada gabanin sauya aniyar tasu.
Sai dai a cewarsa, ya zama dole su dawo daga rakiyar aiwatar da zanga-zangar bayan jagororin sun shaida masu cewa zanga-zangar za ta takaita ne kawai a birane uku da suka hada da Jos a Jihar Fulato da Abuja, sai kuma Kaduna, sabanin jihohi 36 kamar yadda tun farko a ka shirya.
- Zanga-zanga: Ana barazanar hallaka Garkuwan Matasan Zamfara
- Sojoji sun yi wa masu shirin zanga-zanga kashedi
- DSS ta kama buhu 2,000 na shinkafar tallafin da aka karkatar a Katsina
“Wannan ne ya sa muke zargin cewa akwai lauje a cikin nadi.
“Shin me ya sa aka takaita zanga-zangar zuwa wadannan yankuna ukun na Arewa kadai,” inji Gamji.
Ya ce babban burin al’ummar Arewa a yanzu shi ne a samar da tsaro da kuma yin wani abu akan tallafin mai da a ka janye, don al’umma su samu zarafin komawa sana’ar noma da kiwo da aka san yankin da shi.
“Wannan shi ne kiranmu ga Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu kan ya tabbatar da wadannan bukatu namu.
“Idan haka ya samu harkokin kasuwanci za su bunkasa a samu zaman lafiya a ko’ina.”
Murtala Gamji ya kuma yi kira ga sauran matasan kasar da su guji shiga wannan zanga-zanga domin an lullube kura ce da fatar akuya, ta hanyar yin amfani da matasa don tarwatsa kasar.
Sannan ya yi kira ga gwamnati da ta hamzarta daukar duk matakan da suka dace don ganin al’ummar kasar sun samu sauki a rayuwarsu.