“Akwai manakisa a gobarar cibiyar kayan gargajiya ta Abuja”
Mutanen da matsalar gobara ta shafa a cibiyar kera kayan al’adun gargajiya ta Abuja (Abuja Arts and Craft billage) da ke kusa da zauren taro na Shehu Musa Yar’aduwa, sun bukaci da a aiwatar da bincike a kan gobarar, wadda ta auku a ranar Juma’ar da ta gabata, inda shaguna 18 daga cikin 75 da […]

Mutanen da matsalar gobara ta shafa a cibiyar kera kayan al’adun gargajiya ta Abuja (Abuja Arts and Craft billage) da ke kusa da zauren taro na Shehu Musa Yar’aduwa, sun bukaci da a aiwatar da bincike a kan gobarar, wadda ta auku a ranar Juma’ar da ta gabata, inda shaguna 18 daga cikin 75 da ke wajen suka kone tare da abubuwan da ke cikinsu bayan wutar ta fara ci da misalin karfe 9 zuwa 11 na dare.
Wani da lamarin ya shafa mai suna malam Adamu Garba, ya ce ya rasa shaguna 2 a yayin gobarar, ya yi zargin cewa masu gadin cibiyar sun hana mambobinsu shiga wajen a farkon farawar gobarar sama da minti arba’in.
A cewarsa masu gadin sun shaida masu cewa ba za su bude wajen ba har sai sun samu umarni daga hukumar da ke kula da cibyar.
Shugaban kungiyar masu sana’ar kayan gargajiya ta cibiyar Mista Zekanayo Chukwumeze tare da shugaban kwamitinsu na amintattu, Malam Mustafa Chidama, sun shaida wa ’yan jarida cewa masu gadin sun ki barin mambobinsu shiga cibiyar sama da minti arba’in bayan faruwarta. “Bayan zuwan motocin kashe gobara biyu ne tare da tsanata neman a bude wajen, a nan ne masu gadin suka bude kofar sannan ko a nan ma motocin ba su iya shiga wajen ba, kasancewar an gindaya wata motar jif a daidai kofar shiga wajen, har sai da gungun jama’a suka daga ta zuwa gefe, sannan motocin kashe gobarar suka samu iya shiga,” inji shugaban kungiyar.
Haka nan kungiyar ta bukaci dakatar da babban daraktan hukumar NCAC, wadda cibiyar ke karkashinta Mista Otunba Olusegun Runsawe kan zargin jawo wa wajen koma baya tun lokacin da ya fara aiki ta hanyar kafa “dokoki marasa kan gado” kamar yadda su ka bayyana. “Wannan waje na daga cikin wurare masu jan hankalin baki da birnin Abuja da ma kasa baki daya ke tinkaho da shi. Sannan baki musamman daga hotel din Sheraton ko a yayin taro a cibyar Shehu Yar’adua kan shigo mana nan sosai tare da yin sayayya sannan wajen ya sada wuraren biyu da kuma wajen shakatawa na Silber bird da ke kusa da mu nan, sai dai zuwan wannan daraktan sai ya sa a ka rufe kofar da ta sada wajen da can.
“Sannan kuma wannan gobarar ta faru ne a ranar da kotu ta ba da umarnin a bude karamar kofar da daraktan ya sa aka rufen har sai an gama shari’a a kan al’amarin tukuna, a daren ne wannan musiba ta auku. “To idan ka hada wannan da kuma na jinkirta bude kofar da ake amfani da ita a yanzu a lokacin da wutar ke ci, sai ka ga maganar manakisa ta kara bayyana.
“A saboda haka muna neman a gudanar da bincike a kan wannan lamari daga wajen ma’aikatar idan har za a yi mana adalci, kasancewar nade-naden ma’aikatar ya karkata ga wata kabila guda daga sama har kasa, inda son kai na iya samun saukin shiga idan aka yi bincike daga wajen,” a cewar shugaban.
Haka nan sun yi zargin cewa har zuwa lokacin ganawar a ranar Talatar da ta gabata babban daraktan bai ziyarci cibiyar ba kamar yadda shi ma manajan wajen ya kaurace zuwa ofishinsa. Babban jami’in ’yan sanda na Wuse Zone 3, CSP Yakubu Sulaiman ya tabbatar da faruwar lamarin tare da fara yin bincike a kai.