‘Akwai masu fada aji da ke neman halasta tabar wiwi a Najeriya’
Ya kamata jama’a su goya mana baya wajen yaki da ta’ammali da tabar wiwi.
Buba Marwa
Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce, akwai wasu masu fada aji da ke kokarin ganin an halasta tabar wiwi a Najeriya.
Shugaban NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa ne ya bayyana haka ne a wajen wani taro da halarta ranar Alhamis a Legas.
- ’Yan Najeriya miliyan 133 na fama da talauci —Rahoto
- ’Yan sanda sun kama mijin da ya azabtar da matarsa da yunwa
Ya ce, “Wasu jiga-jigan Najeriya sun ba da himma wajen neman a halasta tabar wiwi domin ba su damar noma ta.
“Wannan kuwa wata alama ce ta daure wa matasan kasar gindi wajen ci gaba da aikata ba daidai ba,” inji shi.
A cewarsa, maimakon neman a halasta wiwi a kasa, “kamata ya yi jama’a su goya mana baya wajen yaki da ta’ammali da ita.”
Kazalika, ya ce masu safarar miyagun kwayoyi kimanin su 19,000 ne suka fada a komar NDLEA a tsakanin shekaru biyun da suka gabata.
Kazalika, ya ce an samu nasarar hukunta mutum 3,011 daga cikin adadin da aka kama.