Akwai masu yi wa Buhari zagon kasa a cikin jami’ansa – Damboa
Alhaji Adamu Damboa dan siyasa ne kuma dan kasuwa mai harkar filaye a yankin Birnin Tarayya, Abuja, a tattaunawarsa da Aminiya ya yi zargin cewa akwai masu yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zagon kasa a cikin jami’an gwamnatinsa, kuma ya bukaci Shugaban kasar ya kori Gwamnan Babban Bankin Najeriya kan abin da ya kira […]
Alhaji Adamu Damboa dan siyasa ne kuma dan kasuwa mai harkar filaye a yankin Birnin Tarayya, Abuja, a tattaunawarsa da Aminiya ya yi zargin cewa akwai masu yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zagon kasa a cikin jami’an gwamnatinsa, kuma ya bukaci Shugaban kasar ya kori Gwamnan Babban Bankin Najeriya kan abin da ya kira kokarin zame wa gwamnatinsa kafa ta hanyar karya darajar Naira a fakaice da sunan mayar da kasuwar musayar kudaden waje mai falle daya:
Aminiya: Me za ka ce kan mayar da kasuwar musayar kudeden waje falle daya da Babban Bankin Najeriya ya yi?
Adamu Damboa: To alhamdulillah, maganar mayar da kasuwar musayar kudaden waje wadda ga alama karya darajar Naira ce a kaikaice, a ganina akwai zagon kasa akwai munafunci daga wadansu da ke cikin gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Misali an fara aiki da wannan kasuwa ce a daidai lokacin da Shugaban kasa ya fita jinya, don haka muka rika tambayar ko an yi haka ne saboda ana tunanin ba zai dawo ba? Me ya sa aka yi haka a daidai lokacin? Me zai sa a dare daya a ce an karya darajar Naira, don haka muna ganin wannan a matsayin wani zagon kasa. Domin mun sha jin Shugaban kasa yana nanata adawa da batun karya darajar Naira, ya kafa hujja da cewa a baya da aka karya darajar Nairar me hakan ya haifar? Ya yi tambayar a fada masa kamfanoni nawa aka kafa bayan karya darajar Nairar, kuma ga shi kwanan nan mun ji Shugaban kasa ya sake nuna damuwa kan wannan mataki da Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya dauka, a lokacin da ya yi buda baki da manyan attajiran kasar nan. Mun ga yadda Shugaban kasa ya nuna damuwa kan haka, kamar yadda mu ma da muka zabe shi muka wahala wajen dora masa wannan amana ta ya shugabance mu domin fitar da mu daga halin da ake jefa kasar nan a ciki na rashin tabbas. Amanar nan ta kowa da kowa ce, ba na wadansu kalilan ba ne. Dukanmu mutanen Najeriya muna hannun Allah ne, sannan muna hannun Shugaban kasa. Don haka ya kamata Shugaban kasa ya dada tashi tsaye domin magance masu neman bata wa gwamnatinsa suna, wadanda suke yi mata zagon kasa. Gwamnan Babban Banki da mukarrabansa da suka yi wannan abu, a hanzarta korarsu daga mukamansu, domin ba shi kadai ya yi haka ba. Abin kunya zamanin mulkin Cif Olusegun Obasanjo ba a karya darajar Naira ba, zamanin Umaru ’Yar’aduwa ba a karya darajar Naira ba, amma a ce a zamanin Shugaba Buhari da muka fi fatar samun alkibla mai kyau kan makomar kasa da tattalin arziki, mutane suke fatar samun saukin rayuwa da jin dadi a ce an karya darajar Naira? To ta Allah ba ta su ba, don haka muna kira ga Shugaban kasa ya gaggauta cire Gwamnan Babban Banki da mukarrabansa kan daukar wannan mataki.
Aminiya: Ba ka ganin wannan shiri akwai hannun Banki Duniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da suka dade suna matsa wa Najeriya ta yi haka?
Adamu Damboa: Wannan gaskiya ce, domin ban mantawa a 1985 zamanin gwamnanmu Abdulmumini Aminu na rike tutar kananan hukumomi biyu daga Jihar Borno, domin nuna adawa da tsare-tsaren IMF. Mun yi adawa da haka ne domin mun lura hukumar tana son mayar da mu bayi ne a kasarmu. Domin ta nuna a cire hannun gwamnati a kusan duk abin da take ba talaka tallafi a karya darajar Naira a yi kaza a yi kaza. Yanzu in ba a yi da gaske ba, Dala sai ta kai Naira 400 ko fiye, saboda haka muna kira ga Shugaban kasa ya tashi tsaye, ba zan gaya masa maganar mulki ba, tunda ya yi mana Gwamna a Jihar Arewa maso Gabas da Borno, ya yi Kwamishinan Mai (Minista) na shekara uku da rabi, ya yi Kwamandan Runduna (GOC), ya yi Shugaban kasa na wata 20 kuma ya shugabanci Hukumar Rarar Man Fetur (PTF), kuma kowa ya ga irin yadda ya bauta wa Najeriya bisa gaskiya da rikon amana, wanda hakan ne ya sa shekara da shekaru jama’a suka sanya shi a gaba domin ya zo ya ceto kasar nan ya dora ta a turba tagari. Don haka tuntuni muke ta kiran a sauke Gwamnan Babban Bankin nan, domin duk wata satar da aka yi a zamanin gwamnatin da ta shude, bankinsa na Zenith ya taka rawa wajen tafka ta, kuma shi ne shugaban bankin. Wai me tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Malam Sanusi Lamido (Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II) ya yi ne aka sauke shi? An sauke shi ne saboda ya fadi muguwar barnar da ake tafkawa wadda daga baya kowa ya ga abin da ya dadi ya tabbata. Saboda haka Shugaban kasa ya tashi ya binciki jami’ansa a musamman a fannin tattalin arzikin kasa da tafiyar da harkokin fadarsa, ya daina zuba musu ido suna kokarin yi masa zagon kasa.
Aminiya: Wace shawara za ka ba gwamnonin Arewa wajen bunkasa noma ganin faduwar farashin mai ya jefa jama’a a cikin talauci?
Adamu Damboa: Kowa ya san duk abin da dan Adam zai kama bayan noma ba zai fisshe shi ba, domin kusan duk abin da zai bukata sai bayan ya wadata da abinci tukun zai fuskance shi. Ko suturar da mutum zai sanya daga noma ake samar da ita, don haka dole ne kasar nan ta koma ga noma. Sai dai abin takaici wadansu gwamnoninmu ba akidar ci gaba ce a gabansu ba. Tunaninsu da akidarsu da manufarsu ba irin na Shugaba Buhari ba ne. Ka duba Shugaban kasa ya tausaya musu ya ba su kudi su biya albashin ma’aikata, amma akwai Gwamnan da aka ce ya je ya biya kansa wasu hakkoki na tun yana shugaban majalisar jiharsa. Ya ci kudin ya bar ma’aikata suna ta ci gaba da wahala. Mu dai a jihohin Arewa maso Gabas inda na fito, Gwamna daya ne tak yake aiki, wato Gwamnan Jihar Adamawa Alhaji Umaru Jibrilla Bindow. A Arewa maso Yamma gwanda-gwanda Gwamnan Katsina, Aminu Masari da takwaransa na Kaduna Nasir El-Rufa’i, amma saura ba sa da akidar Buhari. Don haka ya wajaba Shugaban kasa ya tsawatar musu, domin dukkansu an zabe su ne saboda shi, saboda wani in ba domin Buhari ba, ko shugaban karamar hukumarsa ba zai ci ba. Idan Shugaba Buhari bai tsawatar wa gwamnonin nan ba, za su ci gaba da shafa wa gwamnatinsa kashin kaji. Rashin yin abin da ya dace daga gwamnonin ya sa ake ta kuka ake ta fama da talauci da yunwa, yaya za a ce wai albashi na neman gagara? Idan har jihohi za su gaza biyan albashi, ta yaya za su inganta rayuwar jama’a balle a yi maganar noma da sauransu?
Gwamnonin nan galibinsu ba akidarsu gyaran kasa irin Shugaba Buhari ba ne, yawancinsu ba su sanya Allah a harkokin mulkinsu ba. Ka dubi kudin da Shugaban kasa ya ba su don biyan albashi amma a ce har akwai Gwamnan da zai karkatar da wannan kudi. Shin idan iyayensu ne suka yi aiki suka yi ritaya ko suke cikin aikin za su bar su da talauci su karkatar da kudin. Yaya mutum zai shafe shekara 35 yana aiki, amma dan fanshon da za a ba shi ya gagara, a ce mutum ya koma yana farskare ko wani aikin da zai lalace. Shin idan iyayensu ne za su yarda a yi musu haka? Shugaba Buhari ya tashi ya tsawatar wa gwamnoni su inganta noma akalla ta wajen samar da isasshen takin zamani da taraktoci ko shanun huda da sauransu. Kuma a tilasta kowane Gwamna ya gina akalla madatsar ruwa daya kowace shekara a jiharsa domin noman rani. Babu abin da talaka yake bukata irin a samar masa da hanyar da zai gudanar da noma cikin sauki, in aka yi masa haka zai iya daukar nauyin karatun ’ya’yansa da kiwon lafiyarsu da sauran dawainiyarsu, kuma hakan zai kara samar da kwanciyar hankali da zaman lafiya a kasar nan. Mu da muka yi ta tallata Buhari, muna ta shan zagi da habaici daga abokan adawa, kuma ba wani abu ke jawo haka ba, face gazawar gwamnonin jihohi su yi koyi da Shugaban kasa wajen sauke amanar da aka dora musu. Don haka Shugaba Buhari ya tashi tsaye ya zuba ido a kan abubuwan da ake gudanarwa a tarayya da jihohi, kada ya dauka kowa mutumin kirki ne mai gaskiya da rikon amana irinsa, wani sai an sa kulki an zungure shi kafin ya yi abin da ya dace. Wani sai an kwankwashe shi, wani sai an mangare shi, wani ma sai an kore shi saboda wani ya gani ya ji tsoro. Labaran da suke zuwa mana hatta a cikin gidansa na Fadar Shugaban kasa, akwai masu hana ruwa gudu, na san yadda muka ji shi ma ba zai gaza ji ba, ko ma ya ji fiye da mu. Don haka ya sa amintattun mutane su bincika cikin sirri don tabbatar da ya yi waje da ire-iren wadannan mutane, ya samu ya tsayar da kafafun gwamnatinsa. Mu talakawa muna tare da Shugaban kasa, za mu ci gaba da goya masa baya, duk wanda ya ki bin sawun Shugaban kasa wajen yin abin da ya dace ga jama’arsa, kada ya sa ran zai sake shiga rigar Buhari ya ci zabe.