Akwai munafukai a cikin manoma da makiyaya da ke ruruta wutar rikici – Shekarau
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Ministan Ilimi, Malam Ibrahim Shekarau shi ne Sakataren Kwamitin Amintattu na Gidauniyar Tunawa da Sa Ahmadu Bello, a tattaunawarsa da manema labarai game da taron zaman lafiya da gidauniyar ta shirya a Kaduna ya bayyana irin kokarin da gidauniyar ke yi wajen ganin an kawo karshen rikicin manoma da […]

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Ministan Ilimi, Malam Ibrahim Shekarau shi ne Sakataren Kwamitin Amintattu na Gidauniyar Tunawa da Sa Ahmadu Bello, a tattaunawarsa da manema labarai game da taron zaman lafiya da gidauniyar ta shirya a Kaduna ya bayyana irin kokarin da gidauniyar ke yi wajen ganin an kawo karshen rikicin manoma da makiyaya a kasar nan. Kuma ya koka cewa akwai munafukai a cikin manoma da makiyaya da ke ruruta wutar rikicin:
Aminiya: Mene ne makasudin shirya wannan taron bita?
Shekarau: Makasudin wannan taron bita a kan rikicin makiya da manoma da ya ki ci ya ki cinyewa, shi ne Gidauniyar Ahmadu Bello Sardauna ta kusan shekara goma da kafa ta. Kuma an kafa ta ce dama tun asali domin ta fito da ayyuka na nagarta da Sa Ahmadu Bello ya yi a lokacin rayuwarsa. Sannan mu tunatar da ’yan baya domin su ga irin nagartar da aka samu musamman a bangaren hadin kai. Sai muka ga wadannan rigingimu na makiyaya da manoma wadanda dai muka sani ba wai abubuwa ne da suka fara faruwa shekara biyu ko hudu baya ba. Amma sai abin yake neman zama karfen kafa ana kashe rayuka, ana kone gonaki ana kone gidaje da makamantansu.
Sai muka duba muka ga cewa lallai a shawo kan abin nan duk kuwa da muna sane da irin kokarin da kowa ke yi da abin da gwamnatoci ke yi amma duk kyan abu idan ba ka hado shi wuri daya ba sai ka ga ba a dace ba. To, abin da gidauniyar Sardauna ke son yi ke nan, inda aka gayyaci wadanda suke da ruwa-da-tsaki a harkar. Ba wai manoma da makiyaya kawai ba duk wanda abin ya shafa yana nan, wato wakilansu suna wurin kuma mun ce tattaunawa za mu yi ba wai cewa muka yi za mu nuna wane ne ke da laifi ko wancen ke da laifi ba.
Manufarmu ita ce sanin abin da ya janyo rikice-rikicen suka yi zafi, idan ba a shawo kansu ba sai a nemi mayar da abin rigingimu na kabilanci, rigingimu na wa ya riga wani zuwa da sauransu.
Aminiya: Ko kuna samun goyon bayan gwamnatocin jihohi a kan wannan kokari da kuke yi na nemo maslaha?
Shekarau: kwarai kuwa gwamnatoci suna ba mu hadin kai, mun ziyarce wasunsu, kuma da saninsu muke wannan taro. Kuma da zarar mun kammala muka tace muka samu abin da muke ganin shi ne mafita misali ta hanyar shawara za mu neme su za mu zauna da su da yake mun sanar da su za mu yi wannan aiki. Amma sai muka ce su koma gefe su kyale mu domin wannan harkar ba siyasa ba ce ba kuma magana ba ce ta a ware su wane ko ba za a saurari su wane ba. Kowa na da ruwa-da-tsaki domin abin da ya shafi rayukan mutane ya wuce zancen ka ce wani bangare ne ke da laifi. A samo yadda kawai za a tserar da rayuka kuma in Allah Ya yarda idan muka gama shawarwarin da muka tattara za mu kira duk wanda abin ya shafa a zauna da su.
Daga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da malamai da limamai duk babu wanda ba wakilansu a nan, kuma in Allah Ya yarda za a samu mafita.
Aminiya: An dade ana irin wannan zaman domin magance matsalolin da suke damun Arewa, ko yaya kake ganin wannan zai bambanta da tarurrukan baya?
Shekarau: Tarurrukan baya gaskiya akwai bambanci da na yanzu domin a baya abin nan ne da ake kiran masana a zo a yi ta gabatar da kasidu a tashi. Amma abin da mu muke yi yanzu shi ne a kira a zauna a kuma rufe kofa domin tattauna don nemp maslaha. Shi ya sa a ciki iyakan wadanda aka gayyata ne ka gani mun san dama suna da ruwa-da-tsaki. Shi ya sa ka ga mutane ne ’yan kadan a cikin dakin taron, a kyale kowa ya amayar da abin da yake ganin yana janyo wannan matsala, ta haka ne in Allah Ya yarda za a samo maslaha.
Shi ya sa mako biyu da suka wuce Masarautar Kano da Sarkin Musulmi suka wakilta ni in je mun zauna an kira irin wannan zama a tsakanin kungiyoyi har muka samo mafita.
Domin su kansu kungiyoyin sun yarda zarge-zarge na shiga tsakaninsu, wato tsakanin makiyaya da manoman da kuma a tsakanin kungiyoyinsu. Su ma kansu a nan muka gano akwai manufunce-munafunce a tsakaninsu. A wurin aka tayar da wadansu inda suka rantse cewa sun daina kaza da kaza. Akwai wadanda aka tsige su a kan mukamansu na kungiyoyin domin su ne ummul-haba’isin rigingimun da suke faruwa, an yi wannan an kuma samu zaman lafiya.
Aminiya: Me za ka ce game da dokokin hana kiwo da wasu jihohi suka fito da su?
Shekarau: Jihohin da suka kafa dokokin muna son fara zama da su domin dokar da ka yi amma wanda ka yi bai fahimci abin da ya sa ka yi dokar ba, bata lokacinka kake yi. Kamata ya yi wanda ka yi dokar dominsa ya fahinci dokar, al’ummar da suke zaune a wurin da makiyaya da manoman kowa ya gane cewa dokar nan an yi ta ce domin amfaninsu. To, su ma gwamnatocin ýmuna kokarin su fahinci hakan, in Allah Ya yarda kuma yana cikin abin da za a tattauna a nan kuma za a samu mafita insha Allahu.