Akwai Munafunci A Lamuran ’Yan Arewa Kan Rashin Tsaro —Sarkin Waka

Mawaki Naziru M. Ahmad ya ce akwai alamun munfunci a yadda ’yan Arewacin Najeriya ke kallon tabarbarewar tsaro a yankin.

Akwai Munafunci A Lamuran ’Yan Arewa Kan Rashin Tsaro —Sarkin Waka

Naziru Sarkin Waka

Mawaki Naziru M. Ahmad, wanda aka fi sani da Sarkin Waka, ya yi zargin munfunci a yadda ’yan Arewacin Najeriya ke kallon tabarbarewar tsaro a yankin.

Naziru ya bayyana hakan ne ta wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, domin tofa albarkacin bakinsa kan yadda bidiyon da ’yan bindiga suka saki na dukan fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da ke hannunsu da ya janyo ce-ce-ku-ce a kasar.

A wani lamari mai kama da kwan gaba kwan baya dai, an ga yadda ’yan bindigar suka yi wa fasinjojin dukan tsiya, tare da ba su damar yin kira ga hukumomi masu fada a ji a duniya da su kawo musu dauki.

Haka kuwa na zuwa ne bayan a baya wani daga fasinjojin da aka fanso daga hannun ’yan bindigar ya ce  ba sa taba lafiyarsu sai dan abin da ba a rasa ba.

A cikin bidyon na Naziru, ya tambayi al’umma me ya sa ba sa tunawa da halin da fasinjojin ke ciki sai lokacin da aka saki bidiyon azabtar da su, wanda ya ce babbar alama ce ta munafunci.

“Anya ko addu’a muna musu kuwa? an ya wadannan rubuce-rubucen da muke yi a kafafen sada zumunta ta ‘na kasa barci’, wani ya yi Allah Ya isa, kuna ganin shi ne mafita?

“To karya muke, munafinci ya fi yawa a cikin al’amuranmu duka, dalili shi ne kwana biyu zuwa uku ne mun manta”, in ji shi.

Ya cigaba da cewa “Amma da an wullo bidiyon mawuyacin halin da suke ciki mun iya zagin gwamnati; to a takaice dai idan muna ganewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari dai ya ce iya abinda zai iya yi ya yi, Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce abin da za su iya kam sun yi… haka Zulum muna ganin yadda yake yawo a titi yadda ka san shi ne jami’in tsaron, Gwamnan Zamfara har cewa ya yi kowa ya kare kansa, Gwamnan Katsina ya fada, abin da ya rage mu da malamanmu ne su fito su fadi abin da ya kamata a yi na gaba.”

Ya kuma ce akwai alamun tambaya a ce tsawon kimanin kwanaki 100 da fasinjojin suka yi a hannun ’yan bindiga an gaza ware ko da wata guda ne da kowacce safiya a yi musu addu’ar kubuta daga hannun ’yan bindigar.

Sarkin Waka dai ba shi ne mutum na farko daga masana’antar Kannywood da ya tofa tasa kan halin tsaron kasar nan ba.

Akwai irnsu Yakubu Muhammad da ya wallafa wakar jan hankalin gwamnati.

Sai kuma Hassan Giggs da ya bayyana takaicinsa kan halin rashin tsaro da yankin ke ciki.