Akwai rufin asiri a sana’ar ginin tukwane – Malama Indo
Malama Aisha Garba wacce aka fi sani da Indo Mai Tukunya mace ce da ta dauki tsawon shekara 30 tana gudanar da sana’ar ginin tukwanen kasa a garin Dawakin Tofa da ke Jihar Kano. Dattijuwar ta ce sana’ar tana da rufin asiri sosai duk da cewa akan samu asara, “inda wasu sukan fashe.” Har ila […]
Malama Aisha Garba wacce aka fi sani da Indo Mai Tukunya mace ce da ta dauki tsawon shekara 30 tana gudanar da sana’ar ginin tukwanen kasa a garin Dawakin Tofa da ke Jihar Kano.
Dattijuwar ta ce sana’ar tana da rufin asiri sosai duk da cewa akan samu asara, “inda wasu sukan fashe.” Har ila yau, ta ce ta gaji sana’ar daga mahaifiyarta.
Game da abubuwan da ake tanada don gudanar da wananna sana’a Malama Indo ta bayyana cewa “idan mutum zai fara sana’ar ginin tukunta yana bukatar tanadar abubuwa da suka hada da talge wato wurin da za a yi ginin tukunyar da kuma kasa har iri uku da suka hada da tabo da yunbu da kuma dala sanann akwai bukatar dinduke da madadi da wuka da kuma mazaniya.”
Daga nan ta bayyana cewa suna samun yunbun da suke ginin tukunya ne daga wani gari da ake kira Watari, inda masu jakuna ke zuwa su hako su kawo musu su saya akan kudi naira 200 a kowane mangala na jaki “Idan muka sa yi wannan yunbu sai mu ajiye shi mu bari ya tsane. Misali idan aka kawo mana yau sai dai mu bari zuwa washegari sannan mu fara aiki da shi. Har ila yau, shi wanann yunbun mukan ajiye shi koda ya bushe babu abin da zai yi. A duk lokacin da muka tashi amfani da shi sai mu jika shi mu hau aiki da shi kamar yadda muke bukata.”
Malama Indo ta bayyana cewa “idan mutum zai yi tukunya bayan ya jika yunbunsa sai ya kwaba shi da tabo idan ya kwabu sosai sai ya dunkule shi wuri guda ma’ana ya yi musu curi-curi. Daga nan sai ya dauka ya dora shi a talge, wurin da aka haka don yin ginin tukunya. Sai ya dauko dinduke ya dinga fadada wanann curin yunbun da shi. Zai yi hakan ne daidai bukatar abin da yake son ginawa danginsu su tukunya ko murhu ko bala-bala ko kwatarniya ko kasko da sauransu. Idan ya fadada yunbunsa daidai bukatarsa sai ya dauko madadi ya gyara cikin ginin da shi sanann ya kawo wuka ya gyara bakin ginin da ya yi. Daga nan kuma sai ya zo ya gina madaurin bakin. Idan ya gama sai ya dauko mazaniya don yi wa ginin tukunyar zanen ado a jiki. Daga nan sai a shanya shi ya bushe kafin a zo batun tuya. Sai mun yi ginin tukwane da yawa sannan sai mu kai su matoya don toyawa,” inji ta.
Ta ci gaba da cewa a matoya ne ake hada wuta ganga-ganga a zuba duka tukwane a ciki a bar su su kwana a ciki, sai washegari sai a kwashe. Ha ila yau, Malama Indo ta bayyana cewa suna yi wa tukwannesu zane ne don su bambance tukwanen junansu a lokacin da aka hada su a wurin tuya.
“Kasancewar sai kowa ya gama kawo tukwannesa sanann ake hadawa a kai matoya don toyawa. Kuma a cikin matoyar nana duk tukwanen ake hada wa a awuri daya, to ta hanyar irin zanen da ka yi wa tukunyarka ne kawai zai sa a gane kayanka. Don haka kowa da irin znen da yake yiwa tukunyarsa don a bambance,” inji ta.
Da aka tambayeta yawan tukwanen da take gina wa a rana, sai ta ce, “a tsawon rana guda daga safe zuwa yamma nakan iya gina tukunya 15 zuwa 20. Malama Indo mai tukunya ta bayyana cewa sana’ar ginin tukunya tana da lokaci, ma’ana ba sa samun sukunin gudanar da sana’asu lokacin damina, saboda ba a samun yunbu a lokacin sakamakon ruwa da ya cika koguna.
“Lokacin damina shi ne lokacin da muke rasa aikin yi, saboda ba ma samun yunbu sakamakon ruwan sama da ake yi da ya cika rafuna. Ba a iya samun yunbu sai a lokacin rani.
A karshe ta bayyana cewa tsawon shekaru 30 da ta dauka tana gudanar da wanann sana’a ta sami nasarori masu tarin yawa inda ta ce sana’ar na rufa mata asiri. “Babu babbar nasara a rayuwa irin idan bukata ta taso maka ka samu damar biyan wanann bukatar taka. Mun aurar da ’ya’yanmu da wannnan sana’ar sun haihu mun yi musu hidima da kudin.