Akwai rufin asiri a sana’ar gwangwan – Alhaji Usaini
Alhaji Usaini Zango daya daga cikin fitattun ’yan gwangwan ne da ke masana’antar gyaran motoci ta Kwakwacin Dawanau, ya bayyana wa Aminiya yadda sana’arsa ta sayar da karafan ababen hawa take bunkasa tattalin arziki tare da samar da ayyukan yi ga al’umma da sauransu. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Yaya ka fara wannan sana’a?Alhaji […]
Alhaji Usaini Zango daya daga cikin fitattun ’yan gwangwan ne da ke masana’antar gyaran motoci ta Kwakwacin Dawanau, ya bayyana wa Aminiya yadda sana’arsa ta sayar da karafan ababen hawa take bunkasa tattalin arziki tare da samar da ayyukan yi ga al’umma da sauransu. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Yaya ka fara wannan sana’a?
Alhaji Usaini: Wannan tambaya taka tana da muhimmanci kwarai da gaske, sai dai lokaci ba zai bari na fayyace maka tun lokacin da na fara wannan sana’a ta gwangwan ba, amma dai na fara wannan harka ce tun lokaci mai tsawo. Alhamdulillah, wannan sana’a ta mu tana da albarka fiye da yadda ake tsammani kuma abar alfahari ce ga dukkanin mai yin ta.
Ta hanyar wannan sana’a, akwai mutane masu tarin yawa wadanda suke samun ayyukan yi domin dogaro da kai, saboda albarkar da ubangiji ya yi mata domin kuwa duk wanda ya je masana’antar gyaran motoci ta Kwakwacin Dawanau zai yarda cewa sana’ar sayar da kayan gyaran mota tana da alfanu.
Hakazalika, dukkanin ’yan gwan-gwan da muke harkoki da su a wannan guri su ma suna da mutane da ke samun abinci karkashin su wanda hakan ya nunar da cewa sana’ar tamu tana da alfanu kwarai da gaske, sannan kowa yana cikin farin ciki da rufin asiri.
Aminiya: Wadanne irin matsaloli kuke fuskanta a wannan sana’ar ?
Alhaji Usaini: Kasan cewa a kowace irin sana’a ana samun kalubale ta wani fannin, amma muna kokarin ganin mun magance kowace irin matsala da ta taso mana ta yadda za mu ci gaba da gudanar da al’amuran mu bisa sanin ya kamata. Sannan muna hada hannu wajen warware duk wata matsala da ta faru walau tsakanin masu sayar da kayan gyraya wato ’yan gwan-gwan da masu motoci ko kuma tsakanin kanikawa da masu sayar da kaya. A gaskiya akwai dangantaka mai kyau tsakaninmu da daukacin abokan huldarmu na yau da kullum.
Aminiya: Masana’antar ku ta Kwakwacin Dawanau ta yi suna sosai wajen iya gyaran motoci, yaya kake kallon wannan a matsayinka na daya daga cikin masu sana’ar gwan-gwan a gurin?
Alhaji Usaini: Babu shakka masana’antar gyaran motoci ta Kwakwacin Dawanau ta yi fice wajen iya gyara da duk wani abu da mota ke bukata. Wannan ya faru ne saboda rikon gaskiya da kuma amana da ake yi tun lokacin da aka dawo wannan guri shekaru masu yawa. Kanikawanmu suna da kwarewa sannan suna da amanar aiki, babu cuta ko ha’inci. Har ila yau, masu sayar da kayan gyara suna kawo mana ingantattun kaya domin mun dauki wannan harka tamu da mutunci don haka muke rike da kambun mu na rikon amana wajen komai.
Aminiya: Ko akwai wata matsala da take damun ku ta fuskar sana’arku?
Alhaji Usaini: Gaskiya muna fama da rashin wadatacciyar wutar lantarki, kuma idan da ace akwai wuta mai kyau, ina tabbatar maka da cewa da yanzu mun wuce haka. Tun da Allah Ya ba mu kwararrun kanikawa kuma kowace irin mota ka kai gyara Kwakwaci za a iya gyara ta, ta koma abar sha’awa. Sai dai matsalar da ke ci mana tuwo a kwarya ita ce ta wutar lantarki. Ayyukanmu suna bukatar wuta wadatacciya kuma mai karfi.
Ina mai amfani da wannan dama na roki gwamnatin, Jihar Kano da ta karamar Hukumar Dawakin Tofa da su taimaka wajen kawo karshen rashin wuta a wannan masana’anta wadda ake alfahari da ita a fadin kasar nan, harma da wasu kasashe na yankin Yammacin Afirka. Na yi amannar cewa Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje zai duba wannan matsala tamu domin jagora ne mai matukar kokari duba da irin ayyukan da gwamnatinsa ke yi, duk da cewa ana fama da matsalar karancin kudi a kasa baki daya.
Aminiya: Me nene sakon ka ga daukacin masu harkoki a masana’antar gyaran motoci ta Kwakwaci?
Alhaji Usaini: Sakona na farko shi ne inaso kowa ya kara rike sana’arsa da gaskiya domin ita ce mutuncinsa, sannan a kara rike amanar abokan hulda insha Allah kowa zai rabauta daga albarkar sana’ar da yake yi a wannan guri kamar yadda a yau muke. Ga masu kai gyaran motoci ina fata za su ci gaba da hakuri da kanikawan mu ta yadda za a dade ana yi.