Akwai rufin asiri a sana’ar gyaran talabijin da rediyo – Yusuf Muhammad

Yusuf Muhammad wani matashi ne da ke sana’ar gyaran kayan wuta a cikin garin Kafanchan. Ya shaida wa Aminiya yayin tattaunawarsu cewa sana’ar gyaran kayan wuta da suka hada da talabijin da rediyo da sauransu akwai matukar rufin asiri a ciki. Ya bayyana irin alherai da kuma matsalolin da sana’ar ke tattare da shi.   […]

Akwai rufin asiri a sana’ar gyaran talabijin da rediyo – Yusuf Muhammad

Yusuf Muhammad wani matashi ne da ke sana’ar gyaran kayan wuta a cikin garin Kafanchan. Ya shaida wa Aminiya yayin tattaunawarsu cewa sana’ar gyaran kayan wuta da suka hada da talabijin da rediyo da sauransu akwai matukar rufin asiri a ciki. Ya bayyana irin alherai da kuma matsalolin da sana’ar ke tattare da shi.

 

Aminiya: Ka fara da gabatar mana da kanka

Ni haifaffen garin Kafanchan ne da ke karamar hukumar Jama’a  a cikin jihar Kaduna kuma nan na taso har zuwa girmana. Na yi makarantar firamarin Waziri Aliyu da kuma sakandirin GSS duka a garin Kafanchan kuma a halin yanzu ina da iyali.

Aminiya: A wane lokaci ka fara wannan sana’ar kuma me da me kake gyarawa?

Na fara koyon sana’ar gyaran rediyo da talabijin ne a shekarar 2001. Bayan na samu kamar shekara bakwai ina gyaran rediyo da bidiyo da kuma talabijin daga nan sai na tafi na koyo gyaran abin da ya shafi kayan satalayit.

Aminiya: Me ya baka sha’awar koyon gyaran kayan wuta?

Farko na fara ne da hada-hadar wayoyi a gida daga nan na fara tunanin a sanya ni koyon gyaran abubuwan da ke amfani da wutar lantarki kuma abinda ya ja ra’ayina a lokacin shine nag a babu wani yaro mai shekaruna da ke koyon irin wannan sana’ar a lokacin.

Aminiya: Wanne irin alheri ka samu a cikin wannan sana’ar?

Na samu rufin asiri sosai wanda bai tsaya a kaina ni kadai ba ya shafi har iyayena dad angina da sauran al’ummar da na ke rayuwa a cikinsu. Na mallaki abubuwan more rayuwa a sanadiyyar wannan aiki kuma alhamdu lillah har yanzu muna samun rufin asiri Ubangiji a kai.

Aminiya: In mun waiwaya zuwa ga matsaloli fa!

Ta nan sai in ce ai babu wani abu da bai tattare da matsala irin na shi. Wani gani yake idan ya kawo gyara da an taca kayan day a kawo shike nan zai tashi ya fara aiki yayin da wani kuma rashin hakuri ne ke damunsa. Sai kuma wani lokaci matsalar yaran aiki.

Aminiya: Akalla yara nawa ke cin gajiyar wannan aiki a karkashinka?

A halin yanzu dai ina da yara guda hudu ta fannin gyaran Rediyo da Talabijin. Ta fannin gyaran satalayit kuwa na yaye yara guda biyar wadanda suka iya aikin.

Aminiya: Wanne kira ka ke da shi zuwa ga matasa ’yan uwanka?

Kiran da zan yiwa matasa shine a daina girman kai a tashi a nemi ilmi da kuma koyon sana’ar da mutum zai dogara dashi don babu abinda yafi wadannan a halin da muke ciki da ma kowanne lokaci a rayuwar dan adam.

Aminiya: Ko a shirye ka ke idan gwamnati da kawo ma ka tallafi a kan wannan sana’ar za ka amsa da hannu biyu?

Ni game da maganar tallafi ma har na gaji da cike-ciken fom na tallafi iri-iri da ake kawo mana. Amma in dai bukatar tallafi ne ai muna matukar bukata. Tunda bamu dogara cewa lallai sai gwamnati ta bamu aiki ba amma dai muna maraba da duk wani abinda zai bunkasa mana sana’o’inmu. A karshe ina kira ga gwamnati da ta yi kokari ta shawo kan matsalolin hauhawar kayayyakin masarufi da sauransu a kasar nan.