Akwai rufin asiri a sana’ar suya – Yahaya Lawan

Wani mai sana’ar suya a babbar kasuwar raguna da ke Aduwawa Benin, Yahaya Lawali ya bayyana irin alherin da ya ce akwai a cikin sana’a sayar da suya ga wanda ya rike gaskiya a cikinta.Yahya ya ce: “Akwai rufin asiri ga mai sana’ar, domin ko ba komai mutum zai iya ya daukar nauyin kansa da […]

Akwai rufin asiri a sana’ar suya – Yahaya Lawan
Akwai rufin asiri a sana’ar suya – Yahaya Lawan

Wani mai sana’ar suya a babbar kasuwar raguna da ke Aduwawa Benin, Yahaya Lawali ya bayyana irin alherin da ya ce akwai a cikin sana’a sayar da suya ga wanda ya rike gaskiya a cikinta.
Yahya ya ce: “Akwai rufin asiri ga mai sana’ar, domin ko ba komai mutum zai iya ya daukar nauyin kansa da na iyalinsa a cikin sauki. Dalilin da ya sa na fadi wannan, na kai kimanin shekaru 15 da wannan sana’ar. Alhamdu lillahi, na samu alheri a ciki ba kadan ba tunda a ciki na samu na yi auren fari. A yanzu ina da ’ya’ya guda hudu kuma dukkansu na sa su makarantar Arabiyya da ta zamani.”
Ya kara da cewa, sana’ar bai rike ta da wasa ba, yana yinta ne tsakani da Allah, domin ya samu ya tsira da mutuncinsa, komai nasa na harkar rikon iyali yana samu yana yi masu gwargwadon hali. Ya ce yana samun ciniki, ba ya rainawa.
“Kamar yadda ka gani, wannan tukufar akwai nama na rago da na shanu da kuma gasassun kaji duk kuma manyan kaji ina sayar da kowace daya a kan kudi Naira 1,700 zuwa 2000, nama kuma kona nawa kake bukata ina iya in yanka maka. Bayan wannan ina tsaftace kayan aikina, irin wukake da nake yankan nama, hatta tukufar ba na barinta da wata kazanta. Takardun da nake kunsa wa mutane nama tsaftatattu ne kuma masu sayen nama a wurina ba sai wanda na sani ba ko da yaro karami ne ya zo sayen nama a wurina ina girmama shi.”
Ya karkare da cewa: “Ina kira ga ’yan uwana masu irin wannan sana’ar da su rungumi wannan sana’ar da hannu biyu tare da gaskiya, domin akwai rufin asiri a ciki kuma su yi taka-tsan-tsan da dora wa kansu bashi mara kan gado.”