Akwai rufin asiri a sana’ar waldar robobi

Malam Shu’aibu Adamu, mai sana’ar waldar robobi yana zaune a Dilimi da ke garin Jos. A wannan tattaunawa da ya yi da Aminiya, ya bayyana mahimmancin sana’ar da kuma irin nasarori da cikashin da ya samu a cikinta:Aminiya: Wane lokaci ka fara wannan sana’a?Shu’aibu Mai walda: Na fara gudanar da wannan sana’a tun a shekara […]

Akwai rufin asiri a sana’ar waldar robobi

Malam Shu’aibu Adamu, mai waldar robobi a bakin aikinsaMalam Shu’aibu Adamu, mai sana’ar waldar robobi yana zaune a Dilimi da ke garin Jos. A wannan tattaunawa da ya yi da Aminiya, ya bayyana mahimmancin sana’ar da kuma irin nasarori da cikashin da ya samu a cikinta:
Aminiya: Wane lokaci ka fara wannan sana’a?
Shu’aibu Mai walda: Na fara gudanar da wannan sana’a tun a shekara ta 1984, a Layin Sarki,  a nan garin Jos, a inda na yi shekaru da dama, daga baya na dawo nan Dilimi.
Aminiya: Kamar wadanne abubuwa ne kuke yi a wannan  sana’a?
Shu’aibu Mai walda: To a wannan sana’a  muna  gyaran takalman roba da bokatan roba da jarkokin roba da robobin da suka shafi jikin babura da robobin jikin mota da sauran robobin da suke jikin injina.
Aminiya: Daga lokacin da ka fara wannan sana’a zuwa yanzu, wadanne irin nasarori ne kake ganin ka samu?
Shu’aibu Mai walda: Na sami nasarori da dama a wannan sana’a domin da ita na yi aure har na haifi yara guda 11 kuma ina nan ina kokarin samun muhalli. Kuma na koyar da yara da dama wannan sana’a.
Aminiya: Yaya za ka bayyana mahimmancin wannan sana’a?
Shu’aibu Mai walda: Babu shakka wannan sana’a tana samar da ayyuka ga matasa, musamman a wannan lokaci da ake koke-koke kan rashin ayyukan yi a kasar nan. Domin duk wanda ya sauke girman kai zai iya koyon wannan sana’a, zai sami rufin asiri, kuma, in Allah Ya yarda, zai rika samun abin da zai ciyar da kansa da iyalansa.
Aminiya: Mene ne babban burinka a kan wannan sana’a?
Shu’aibu Mai walda: Babban burina a kan wannan sana’a shi ne na ga cewa na gama  lafiya  a nan duniya da kuma lahira.
Aminiya: Wane kira za ka yi ga gwamnati dangane da mahimmancin tallafa wa masu kananan sana’o’i a kasar nan?
Shu’aibu Mai walda: Duk wani mutum mai hankali zai ji takaicin yadda matasa suka rasa ayyukan yi a kasar nan. Babu shakka wannan babban kalubale ne ga gwamnatoci da  dukkan al’ummar kasar nan. Don haka ina kira ga gwamnati kan ta rika tallafa wa masu kananan sana’o’i domin yin hakan zai samar da ayyukan yi ga dubbin matasan da ba su da ayyukan yi a kasar nan.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna