Akwai rufin asiri a sayar da kayan gargajiya – Malam Aliyu

Wani dattijo da ya kewaye kasar mai suna Malam Aliyu Suleiman Tashar Kade, wanda ya fito daga karamar Hukumar Kudan Jihar Kaduna. Dattijon ya shafe shekaru mai yawa yana zagaya yankin Kudu-maso-Gabas yana sana’ar sayar da kayan gargajiya da suka hada da tinitin da gashin dawisu da na jimina da sauransu. A tattaunarsa da Aminiya […]

Akwai rufin asiri a sayar da kayan gargajiya – Malam Aliyu
Akwai rufin asiri a sayar da kayan gargajiya – Malam Aliyu

Wani dattijo da ya kewaye kasar mai suna Malam Aliyu Suleiman Tashar Kade, wanda ya fito daga karamar Hukumar Kudan Jihar Kaduna. Dattijon ya shafe shekaru mai yawa yana zagaya yankin Kudu-maso-Gabas yana sana’ar sayar da kayan gargajiya da suka hada da tinitin da gashin dawisu da na jimina da sauransu. A tattaunarsa da Aminiya ya bayyana yadda sana’arsa take rufa masa asiri. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Za mu so muji takaitaccen tarihinka?
Malam Aliyu: Sunana Aliyu Suleiman Tashar Kade kuma ni mutumin karamar Hukumar Kudan ne da ke Jihar Kaduna.
Aminiya: Tun wane lokaci ka fara wannan sana’ar?
Malam Aliyu: Na fara wannan sana’a yau kimanin shekara 15 ke nan. dan uwana Malam Isah wanda yake zaune a Maiduguri, shi ne ya koyamin wannan sana’a. Kuma mun halarci taron kasuwar duniya da na harkar kasuwanci na kasa da kasa da ma na kwallon kafa da kuma taron al’adun gargaji. A cikin kayayyakin da nake sayar wa akwai aikin Kano ,akwai na Zariya da sauran wurare daban-daban.
Aminiya: Wadanne sana’o’i ka yi kafin wannan?
Malam Aliyu: Da can kafin na fara wanna sana’a nayi kasuwanci daban-daban na yi harkar kayan gwari, inda nake kai wa Jihar Legas da Kaduna da Kano da kuma garin Jos da sauran wurare a arewacin kasar nan. Har ila yau, na kai gyada danya a shekarun baya zuwa Jihar Kano da garin Maiduguri, na yi sana’ar sayar da dankali da walaha da rake da sauransu.
Aminiya: Me ya sa ka yi watsi da wadancan sana’o’i ka koma ta kayan gargajiya?
Malam Aliyu: Idan abincin ka ya kare a sana’a ba ka da yadda ka iya, sai ka bar ta ka kama wata ta daban.
Aminiya: Shin wannan sana’ar da kake yi yanzu tana bukatar jari mai kauri?
Malam Aliyu: Wallahi ba ta bukatar wani babban jari, babban jarinta shi ne ka rike gaskiya da rukon amana iya dadi iya wuya. Akwai wurin da zaka je a baka wadannan kayan sai ka sayar ka kai kudi daga baya. Kuma kasuwar da zakaje ka sayar da duk abin da zaka yi kayi gaskiya da rukon amana idan Allah ya yarda ko baka yi kudi ba zaka zauna cikin rufin asiri.
Aminiya: Nan kurmi ne ba kasar Hausa ba, kana samun masu sayen kayan kuwa?
Malam Aliyu: banyan ,yan siyasa wato honarabul, masu rike da sarautun gargajiya nasu na nan suke saye sai kuma wani zubi matasan suma suna saye wani zubin.farinn gashin jimina yafi daraja wanda ba sai lallai mutanen jahar kuros riba ko na ribas ba suke saye ba har mutanen mu na arewa suna saye suna yin amfani dasi wajen adon daki muna ma yin mafecin sa manya sarakuna suna saye ko kuma manyan mu dake zaune a kasar waje idan zasu zo har kwangilar aikin suna bamu.
Aminiya: Ka ce farin gashin jimina ya fi tasiri shi bakin mai ya hana shi?
Malam Aliyu: Alhamdulillahi, shi wannan farin ana amfani da shi ne lokacin bikin al’adun gargajiya na ’ya’yan sarakuna da manyan ’yan siyasa ko manyan attajirai a yankin kudancin kasar nan. Sukan sanya shi akan hulunansu. Bakin kuma ana yin mafici da kuma wasu Fulani baroroji da suke sanyawa a kan hularsu.
Aminiya: Wace fa’ida kake ganin ka samu daga wannan sana’ar ?
Malam Aliyu: Alhamdulillahi ka susa mini inda yake min kaikayi. Da wannan sana’ar nake kula wa da iyalina kamar biyan kudin makarantar yara da abinci da sutura da bangaren kiwon lafiyarsu. Har ila yau, idan da dama nakan taimaka wa’yan uwa da abokan arziki.
Aminiya: Wato dai ana samun rufin asirin daga wannna sana’ar ke nan?
Malam Aliyu: Tabbas, sai dai mu ce Alhamdulillahi.

’Yan bindiga sun kashe mutum 7 da sace dabbobi a Katsina  

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista