Akwai rufin asiri sosai a sana’ar gugguru –Salihu Musa
Aminiya: Me ye ya karfafa maka gwiwar bude wannan masana’anta?Babban abin da ya karfafa mini gwiwar bude wannan masana’anta shi ne domin na samarwa kaina sana’a, domin duk mutumin da ba shi da sana’a gaskiya bai yi ba. Domin sana’a ita ce rayuwa ga mutum, musamman irin wannan sana’a ta yin gugguru da nake yi. […]
Aminiya: Me ye ya karfafa maka gwiwar bude wannan masana’anta?
Babban abin da ya karfafa mini gwiwar bude wannan masana’anta shi ne domin na samarwa kaina sana’a, domin duk mutumin da ba shi da sana’a gaskiya bai yi ba. Domin sana’a ita ce rayuwa ga mutum, musamman irin wannan sana’a ta yin gugguru da nake yi. Kuma daga lokacin da na bude wannan masana’anta a watan Disambar shekarar da ta gabata, zuwa yanzu a gaskiya na ga ci gaba. Abokaina suna cewa ada suna ganina ina yin gayu, amma yanzu suna ganina kaca-kaca. Nakan ce masu ai ni yanzu nafi son na ganni kaca-kaca saboda naira 10, naira biyar din da nake samu ta hanyar wannan sana’a tafi mini gayun da nake yi ada.
Aminiya: Kamar ya ya kake yi wajen gudanar da wannan masana’anta?
To yadda nake gudanar da wannan masana’anta shi ne na debo yara ne kamar 15 wadanda suke taimaka mini wajen gudanar da wannan masa’anta. Kuma muna amfani da wani inji ne na tuka-tuka wajen soya guggurun da muke yi.
Aminiya: Me za ka ce game da yadda al’ummar wannan yanki suka rungumi wannan gugguru da kake yi a wannan masana’anta?
A gaskiya wannan gugguru da muke yi ya samu karbuwa sosai da sosai a wannan yanki na Saminaka da sauran yankuna makwabta. Jama’a suna son wannan gugguru da muke yi sosai da sosai, sai dai saboda karamin inji muke amfani da shi bama iya yin yawan adadin abin da jama’a suke bukata. Tun da safe idan na tayar da injina sai dare nake kashewa, amma duk da haka bama iya yin yawan adadin abin da jama’a suke bukata.
Aminiya: Ta yaya kuke sayar da wannan gugguru da kuke yi?
A lokacin da na fara yin wannan gugguru mutane suna zuwa su sayi na naira 10 zuwa naira 50 wasu su auni mudu, amma yanzu ina bi shaguna ina kaiwa masu sari a wannan yanki na Saminaka da sauran sassan makwabta wannan yanki. Sannan dukkan daliban makarantun da suke makwabta da wannan waje, idan an tashi daga makaranta sai kace nan ne makarantar daliban suke saboda yadda suke zuwa su mamaye wannan waje don sayen wannan gugguru.
Aminiya: A kullum kakan yi cinikin kamar nawa?
A kullum muna yin cinikin kamar naira dubu 20 zuwa naira dubu 25.
Aminiya: Ma ye babban burinka kan wannan masana’anta?
Babban burina shi ne na kara fadada wannan masana’anta saboda mutane da dama su zo, su sami abin da za su ci.
Aminiya: Wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga gwamnati da matasa wadanda ba su da aikin yi?
Ina kira ga gwamnati kan ta rika tallafawa masu kananan sana’o’i domin yin haka zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasan kasar nan. Kuma ina kira ga matasa kan su guji raina sana’a komai kankantar ta su tashi su rungumi sana’a komai kankantar ta. A hankali sai su kai ga manyan sana’o’in.