Akwai shakku game da alkawarin tallafin da shugaban kasa ya ce zai ba ‘yan kasuwan Sakkwato -Shugaban ‘yan kasuwa

Shugaban ‘yan kasuwa na jihar Sakkwato Alhaji Kabiru Hali ya ce akwai shakku ga alkawarin bayar da tallafin naira miliyan250 da shugaban kasa ya yi wa ‘yan kasuwar jihar domin su rage asarar da suka yi.Shugaban ya yi wannan bayanin ne a lokacin taron tsofaffin shugabannin PDP na Sakkwato ta tsakiya.Shugaban ‘yan kasuwar ya kara […]

Akwai shakku game da alkawarin tallafin da shugaban kasa ya ce zai ba ‘yan kasuwan Sakkwato -Shugaban ‘yan kasuwa

Shugaban ‘yan kasuwa na jihar Sakkwato Alhaji Kabiru Hali ya ce akwai shakku ga alkawarin bayar da tallafin naira miliyan
250 da shugaban kasa ya yi wa ‘yan kasuwar jihar domin su rage asarar da suka yi.
Shugaban ya yi wannan bayanin ne a lokacin taron tsofaffin shugabannin PDP na Sakkwato ta tsakiya.
Shugaban ‘yan kasuwar ya kara da cewa, dole ne mu kalubalanci Jonathan kan wannan tallafin da ya furta zai bayar, don kowa ya sani ‘yan kasuwar Sakkwato ba yau ne suka fara yin asara ta hanyar gobara ba, wannan
kusan shi ne na hudu, amma babu wata rana da fadar shugaban kasa ta jajanta muna balle ta bayar da wata gudunmuwa, sai yanzu da siyasa ta kawo shi Sakkwato, ku muna jira mu gani ko zai cika alkawari.