Akwai shakku kan aiwatar da sahihin zabe a badi – Sheikh Zakariyya
Wani malamin addinin Musulunci a Abuja, Sheikh Hussaini Zakariyya ya koka kan yadda al’amura ke gudana a kasar nan a yanzu, inda ya ce muddin ba a shawo kansu ba, zai yi wuya a gudanar da sahihin zabe a badi. Sheikh Hussaini Zakariyya ya bayyana haka ne a yayin rufe tafsirinsa na bana a ranar […]
Wani malamin addinin Musulunci a Abuja, Sheikh Hussaini Zakariyya ya koka kan yadda al’amura ke gudana a kasar nan a yanzu, inda ya ce muddin ba a shawo kansu ba, zai yi wuya a gudanar da sahihin zabe a badi.
Sheikh Hussaini Zakariyya ya bayyana haka ne a yayin rufe tafsirinsa na bana a ranar Talatar makon jiya a masallacin Usman bin Affan da ke kusa da Baned Plaza a Abuja, inda ya ce gaza shawo kan matsalar tsaro a jihohin Arewa maso Gabas da musguna wa jam’iyyun adawa ta hanyar tsige gwamnoninsu da kashe makiyaya da kora shanunsu da barazanar yi wa jama’a rajista a tsakanin Arewa da Kudu suna iya haifar da matsala ga zaben na badi.
Babban bako a yayin rufe tafsirin, Janar A. B. Mamman mai ritaya, bukatar Musulmi ya yi su ci gaba da aikata kyawawan halaye da sauran ibadoji da suka koya a watan Ramadan, inda ya ce haka ne alamar azuminsu ya karbu.
Shugaban kwamitin masallacin Alhaji Sani Baba addu’a ya yi ga wadanda suka taimaka wajen sake gina masallcin wanda ya hada da wani bawan Allah da ya taimaka da sama da Naira miliyan 70 da wasu da suka yi aiki na sama da Naira miliyan 20 da wadanda suka gina wajen tsarki da alwala da sauran jama’a da suka taimaka a matakai daban-daban.