Akwai sirri a cikin sana’ar hayar babur – Aliyu Bakwai

Wani matashi mai suna Aliyu Bakwai da ke sana’ar haya da babur din keke-Napep ya ce, ya ki barin sana’ar saboda alherin da ake samu a cikinta.Aliyu Bakwai dan kimanin shekaru 25 da haihuwa dan asalin jihar Zamfara ya shaida wa Aminiya a Abuja cewa ya tsunduma cikin sana’ar ta hanyar wani abokinsa.Ya ce, “Gaskiya […]

Akwai sirri a cikin sana’ar hayar babur – Aliyu Bakwai
Akwai sirri a cikin sana’ar hayar babur – Aliyu Bakwai

Wani matashi mai suna Aliyu Bakwai da ke sana’ar haya da babur din keke-Napep ya ce, ya ki barin sana’ar saboda alherin da ake samu a cikinta.
Aliyu Bakwai dan kimanin shekaru 25 da haihuwa dan asalin jihar Zamfara ya shaida wa Aminiya a Abuja cewa ya tsunduma cikin sana’ar ta hanyar wani abokinsa.
Ya ce, “Gaskiya ita wannan sana’a ta haya da babur a Abuja tana da alheri da kuma sirri. Wani abokina ne ya janyo ni cikinta. Lokacin ina zaune a garinmu Kwashabawa ba ni da sana’ar yi bayan na kammala makarantar boko. Shi da ma ya dade yana yin ta a Abuja. Da muka zo sai ya yi mani hanya na samu mashin. A yanzu zancen da nake yi da kai na samu alheri da yawa.”
Ya ci gaba da cewa, “Nakan aika wa mahaifiyata kudi da ’yan’uwana da kuma abokanen arziki. Sannan kuma nakan dauki nauyin kaina kamar yin sutura da kudin abinci da sauran dawainiyar rayuwa. Babu abin da zan ce sai godiyar Allah. Shi ya sa na ki canja sana’a saboda ina jin dadin wannan sana’ar.”
Ya bayyana cewa duk da yake babur din da yake aiki da shi ba na sa ba ne amma yakan biya balas din da aka yanke masa har ya tsira da wani abu.
“Ba zan gaya maka abin da nake samu ba amma a kullum ta Allah idan na fito na yi aiki nakan samu balas har na samu rarar kudi da zan ajiye ba tare da wata matsala ba. Ni ba na yin nisa. Daga Iyafot jukshin nake dauko fasinja zuwa jabi har bega ina zuwa ba tare da wata matsala ba,” inji shi.
Sai dai Aliyu ya bayyana cewa duk lokacin da Allah Ya hore masa jari zai koma gida ya ci gaba da karatu tare da gudanar da sana’ar haya garinsu.