‘Akwai sirri sosai a sana’ar sarrafa fatun maciji’
‘Akwai sirri sosai a sana’ar sarrafa fatun maciji’
Ubale Majemar Kofar Wambai, dattijo ne da ya shafe kusan shekara 60 yana sana’ar sayar da fatar macizai a unguwar Kofar Wambai da ke Kanon Dabo a Najeriya.
A cikin tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana mana sirrin da ke cikin wannan sana’ar da kuma wuraren da suke samo macizan.