Akwai siyasa a rikice-rikicen da ke faruwa a kasar nan – Sani Zauro
Alhaji Sani Hukuma Zauro shi ne Shugaban Amintattu na Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi, ya shaida wa Aminiya cewa akwai ’yan siyasar da suke amfani da matasa wajen tada zaune-tsaye: Me za ka ce game da yawan tada zauna-tsaye a kasar nan? Abin da zan ce ’yan siyasar da suke neman mulki ido rufe su […]
Alhaji Sani Hukuma Zauro shi ne Shugaban Amintattu na Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi, ya shaida wa Aminiya cewa akwai ’yan siyasar da suke amfani da matasa wajen tada zaune-tsaye:
Me za ka ce game da yawan tada zauna-tsaye a kasar nan?
Abin da zan ce ’yan siyasar da suke neman mulki ido rufe su ji tsoron Allah, ko Musulmi ko Kirista ka fahimci cewa Allah Ya ke ba da mulki ga wanda Ya so kuma kowane dan Adam Allah Ya tsara masa abubuwan da zai samu a duniya ko an ki ko an so.
’Yan a fasa kowa ya rasa su tausaya wa al’ummar Najeriya, kowa ya ga sakamakon rashin zaman lafiya a Arewacin Najeriya, harkokin kasuwanci sun tsaya, mata an kashe mazansu, kananan yara an kashe iyayensu. Har yanzu wadansu iyaye ba su san inda ’ya’yansu suke ba, wadansu mata ba su san inda mazansu suke ba.
Dukan wadannan tashe-tashen hankula da suke faruwa idan ’yan siyasa suka koma ga Allah za mu samu zaman lafiya.
Amma za ka ga wani dan siyasa idan yana neman wata kujera ta wani dan siyasa da ke kan mulki sai ya yi ta kokarin bin wasu hanyoyi na bata wanda ke kan kujerar. Kamar abin da ke faruwa yanzu a kasar nan, na irin yadda wadansu ’yan siyasa ke amfani da matasa domin tada zaune-tsaye.
Ina kira da babbar murya ga ’yan siyasar da suke haddasa fitina su san cewa duk mutumin da ya rasa ransa a dalilinsu Allah zai tambaye su ranar gobe Kiyama. Idan mutum daya ya rasa ransa sai ya ba da amsa a gaban Allah. Haka su ma wadanda ake sa wa suna kashe jama’a Allah zai tambaye su.
Ana zargin cewa ’yan siyasar ba su da kishin inganta rayuwar jama’arsu, me za ka ce?
Babban abin da muke yi a kullum shi ne wayar da kan al’umma, amma ya kamata a san cewa talakawa ma suna da gagarumar gudunmawa wajen lalata siyasar Najeriya. Abin da ya sa na fadi haka shi ne kullum sun fi son dan siyasar da zai ba su kudi maimakon wanda zai yi musu ayyukan raya kasa ko kare rayukansu da dukiyoyinsu. Amma yanzu ga dukan alamu a wannan siyasa da muke ciki abin ya fara sauyawa tun daga wajen yakin neman zabe na shekarar 2015. Malaman addini da ake ba su makudan kudi a shekarun da suka gabata lokacin yakin neman zabe su ma yanzu ko an ba su kudin, tsayawa suke yi su tsage gaskiya. Shi ma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na ji kwanakin baya yana cewa a zabi duk inda mutumin kirki ya fito.
Mene ne kiranka ga matasa a kan su guji shiga bangar siyasa da shaye-shayen miyagun kwayoyi?
Gaskiya wadansu matasa na kasar nan suna cikin wani hali marar kyau domin wadansu ’yan siyasa sun riga sun bata su da shan miyagun kwayoyi da kuma bangar siyasa saboda rashin hankali.
Matasa su sani cewa su ne ginshikin ci gaban manyan da ke sa su suna aikata miyagun halaye. Idan su ma suka gyaru za su iya kaiwa ga wannan matsayi wanda ba za su so ’ya’yansu su aikata irin abin da suke yi ba. Shan miyagun kwayoyi suna haddasa ta’addanci da cuta mai yaduwa ga al’umma. Saboda haka ya kamata matasa su yi wa kansu kiyamul laili. Haka ma al’umma da shugabannin kasar nan da sarakuna da ’yan siyasa su dauki matakin dakile wannan matsala ta shaye-shaye da bangar siyasa.
Su kuma matasa su zamo masu dogaro da kai wajen koyon sana’o’in hannu da harkokin kasuwanci.