Akwai ’yan ƙwaya a cikin sarakunan gargajiya — Obasanjo

Obasanjo ya ce a cikin sarakunan akwai masu safarar miyagun ƙwayoyi da waɗanda ke garkuwa da mutane.

Akwai ’yan ƙwaya a cikin sarakunan gargajiya — Obasanjo

Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda sarautar gargajiya ke rasa martabarta a ƙasar nan.

A cikin sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’, ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya.

“A yau, akwai ’yan daba, masu safarar miyagun ƙwayoyi, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ake kira sarakuna,” in ji Obasanjo.

“Wannan abu ne mai matuƙar ban takaici, kuma yana daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya.”

Ya ce dole ne a dawo da mutunci da ƙimar sarautar gargajiya domin tana taka rawar gani a ci gaban ƙasa.

Har ila yau, ya gargaɗi shugabanni cewa idan ba su magance matsalolin da jama’a ke fuskanta ba, hakan na iya haifar da rikici a nan gaba.

“Idan gwamnati ba ta saurari kokensu ba—musamman matasa da suka fusata—to nan gaba abubuwa ba za su yi kyau ba,” in ji shi.

“Waɗanda suka hana a samu sauyi cikin lumana, za su gamu da sauyi ta hanyar tashin hankali.”

Obasanjo ya ƙara da cewa idan shugabannin Afirka suka yi watsi da wannan gargaɗi, hakan na iya haddasa rikici a nahiyar gaba ɗaya.

“Yin watsi da wannan gargaɗi kamar yin rawa ne lokacin da gidanka ke ci da wuta,” in ji shi.