Akwai ’yan Boko Haram da ko Fatiha ba su iya ba – Sojoji
Kakakin Sojin Najeriya Kanar Sani Usman Kuka-Sheka ya ce wasu daga cikin ’yan Boko Haram da sojoji suka kama ko Fatiha ba su iya karantawa balle wasu sassan kur’ani kuma ma ba su yin ayyukan da addinin da suke da’awar suna yaki ne dominsa.Kanar Sani Kuka-Sheka ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook lokacin […]
Kakakin Sojin Najeriya Kanar Sani Usman Kuka-Sheka ya ce wasu daga cikin ’yan Boko Haram da sojoji suka kama ko Fatiha ba su iya karantawa balle wasu sassan kur’ani kuma ma ba su yin ayyukan da addinin da suke da’awar suna yaki ne dominsa.
Kanar Sani Kuka-Sheka ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook lokacin da yake tattauna batun Boko Haram da wasu ’yan Najeriya.
“Da dama daga cikin mayakan Boko Haram da sojojin Najeriya suka kama ba su iya karatun Alkur’ani ba, wasunsu ma ba su iya karatun Surar Fatiha ba, amma suna da’awar suna son kafa ‘Daular Musulunci,” Kanar Sani ya rubuta a shafinsa na facebook.
Babban jami’in na soji ya ce abin kunya ne irin barnar da kungiyar take tafkawa, inda ya ce “Lokacin da sojoji suka kwace sansanoninsu da wuraren da suke samun horo ba su samu Alkur’ani ko Hadisi ko wani littafin fikihu ba,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Abin da suka samu kawai shi ne harsasai… da sauran nau’o’in magunguna ciki har da na kara karfin jima’i,” inji Kuka-Sheka. daruruwan masu bin Kuka-Sheka a shafinsa na Facebook sun yada wannan bayani nasa da ke nuna yadda ’yan ta’addan ke bata sunan Musulunci.
Tuni kasashen Najeriya da Chadi da Kamaru da Jamhuriyyar Nijar suka amince su hada sojoji dubu takwas da 700 domin murkushe Boko Haram kafin karshen shekarar nan.