Akwai ’yan Najeriya sama da 7,000 da ke aiki a Qatar
Ayyukan da suke yi sun hada da likitanci da injiniyanci da harkar gine-gine.
Jakadan Najeriya a kasar Qatar, Yakubu Abdullahi Ahmed ya ce akwai ’yan Najeriya sama da mutum 7,000 da ke ayyuka daban-daban a kasar.
Ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a cikin sakonsa na murnar samun ’yancin kai ga ’yan Najeriya mazauna kasar ta Qatar.
- Tun daga 1999 ba gwamnatin da ta kai tamu kokari —Buhari
- Shekara 61: Kasashen duniya sun taya Najeriya murna
A cewarsa, irin ayyukan da suke yi a kasar wacce ke yankin Gulf sun hada da aikin likitanci da injiniyanci da harkar gine-gine da sauransu.
Jakadan ya ta’allaka hakan da kyakkyawan shugabancin da kasar take da shi, wanda ya ce ya samar da yanayi mai kyau ga ’yan kasashen waje su yi aiki ba tare tsangwama ba.
Daga nan sai ya yi kira gare su kan su ci gaba da bin dokokin kasar sau da kafa tare da kare mutuncin Najeriya yadda a can.
Yakubu ya kuma jinjina wa kyakkyawar alakar da ake samu tsakanin Najeriya da Qatar, inda ya yi fatan za ta ci gaba da bunkasa, musamman ta bangarorin noma da hakar ma’adinai da harkar man fetur da iskar gas da kuma ayyukan raya kasa.
Ya ce, “Gwamnatin Najeriya ta tsara sabbin manufofi da zasu saukaka harkokin kasuwanci da zuba jari wadanda za su yi daidai da tanadin kasashen duniya.
“Wasu daga cikin irin wadannan tsare-tsaren sun hada da rangwamen biyan haraji da yin sassauci a kai da ma wasu da dama da za su inganta ayyukan kamfanoni,” inji Jakadan.