Akwai ‘yanci da rufin asiri a kasuwanci –Iliyasu Muhammad
Aminiya: A wane lokaci ne ka fara kasuwancin saye da sayar da buhunan leda? Iliyasu Muhammad: Na fara wannan kasuwanci na sayar da buhunan leda ne, kamar shekara 32 da suka gabata a nan garin Jos. Ko da yake na fara da sayar da takardar siminti da buhunan rama ne, daga baya kuma na hada […]
Aminiya: A wane lokaci ne ka fara kasuwancin saye da sayar da buhunan leda?
Iliyasu Muhammad: Na fara wannan kasuwanci na sayar da buhunan leda ne, kamar shekara 32 da suka gabata a nan garin Jos. Ko da yake na fara da sayar da takardar siminti da buhunan rama ne, daga baya kuma na hada da sayar da buhunan leda. Domin a da muna sayar da buhunan rama ne amma da zamani ya zo, sai muka yi sauki da sayar da buhunan rama, muka mayar da hankali a kan sayar da buhunan leda. Amma duk da haka har yanzu muna sayar da buhunan ramar, domin akwai masu sanya albasa da alkama da hatsi su kai Arewa da kasashen Afirka ta Yamma da ta Arewa kamar Nijar da Mali da Aljeriya da Libya saboda akwai zafi a wadancan wurare.
Aminiya: Kamar daga wadanne wurare ne kake sayo buhunan kuma daga ina ake zuwa a sayi wadannan buhuna a wurinka?
Iliyasu Muhammad: Muna sayo wadannan buhuna ne a wurare daban-daban, misali kamar buhunan da aka riga aka yi amfani da su. Wato buhunan da aka cire siminti da sukari da fulawa da shinkafa muna sayen su ne daga hannun diloli da suke tarawa. Kuma a bangaren sababbin buhunan leda, musa sayo su ne daga kamfonin leda da ke biranen Legas da Kano da nan garin Jos.
Kuma masu zuwa suna sayen buhunan leda a wurimu, suna zuwa suna saye daga ko’ina a kasar nan. Haka kamar buhunan zuba ma’adanai muna samun masu zuwa saye a wajenmu daga kowanne bangare na Jihar Filato.
Aminiya: A takaice wadanne nasarori ka samu a kasuwanci na sayar da buhunan leda?
Iliyasu Muhammad: A gaskiya mun samu nasarori da dama, domin duk wani abu da Musulmi zai yi a duniya, babban burinsa shi ne ya je aikin Hajji. To ta dalilin wannan kasuwanci na je aikin Hajji da Umara kuma na kai wadansu mutane da dama. Kuma ina rike da iyalaina ina daukar nauyinsu ta kowane fanni kuma ina rike da ’yan uwa da abokan arziki ta dalilin wannan kasuwanci. Kuma ina da muhallina da sauran abubuwa na rayuwa gwargwadon hali. Kuma ta dalilin wannan kasuwanci na sha zama da manyan mutane daga bangaren gwamnati da masu zaman kansu.
Kuma ta dalilin wannan kasuwanci na samu nasarar bude wasu bangarori daban-daban, kamar bangaren saye da sayar da tsofaffin karafa da bangaren noma da kiwo da sauransu. Don haka ban san yawan mutanen da suke cin abinci a karkashina ba, ta dalilin wannan kasuwanci.
Aminiya: Ko akwai wasu kalubale da ka taba fuskanta a wannan kasuwanci?
Iliyasu Muhammad: A gaskiya rayuwa ba ta rasa matsala, don haka na sha fuskantar matsaloli a wannan kasuwanci. Misali ko a ’yan shekarun nan, muna fuskantar matsaloli na tsadar buhunan leda da rashin ciniki. A yanzu sau tari, sai kun daidaita da kamfani ka bayar da oda, sai daga baya su ce maka ba za ta yiwu ba, farashin kaya ya tashi, dole sai an kara kudi. Kuma idan ka sayi ledar sai ka zo, ciniki ya gagara.
Haka wani lokaci sai mun sayo kaya, sai a zo a ce ba a son wannan kaya. Wadannan suna daga cikin matsalolin da muke fuskanta a wannan kasuwanci. Kuma dama kasuwanci ya gaji irin wadannan matsaloli.
Aminiya: A matsayinka na wanda ya dade yana kasuwanci, yaya za ka bayyana muhimmancin kasuwanci?
Iliyasu Muhammad: Harkar kasuwanci wata gona ce mai matukar amfani da take da rufin asiri. Kuma akwai wurare da dama da harkokin kasuwanci suka bambanta da aikin gwamnati. Na farko akwai ’yanci a kasuwanci, domin dan kasuwa yana da ’yanci fiye da ma’aikacin gwamnati. A kullum ma’aikacin gwamnati yana cikin zulumi. Amma shi dan kasuwa, matukar ya rike kasuwanci da gaskiya to ba ya da fargaba. Don haka kasuwanci yana da dadi.
Aminiya: Wadanne hanyoyi kake ganin gwamnati za ta bi, ta bunkasa kasuwanci a kasar nan?
Iliyasu Muhammad: Manyan hanyoyin da gwamnati za ta bi, ta bunkasa harkokin kasuwanci a kasar nan su ne ta tallafa wa manya da kananan ’yan kasuwa. Tallafin da gwamnati za ta yi wa manyan ’yan kasuwa shi ne ta halatta musu saye da samun Dala. Wato ta rika sayar wa manyan ’yan kasuwa Dala a Babban Bankin Najeriya, domin su rika fita suna sayo kaya daga waje. Su kuma kananan ’yan kasuwa gwamnati ta tallafa musu ta hanyar ba su rance. kuma ta inganta wutar lantarki. Idan gwamnati ta yi wadannan abubuwa harkokin kasuwanci zai bunkasa a kasar nan.
Aminiya: Wane kira gare ka zuwa ga ’yan kasuwa?
Iliyasu Muhammad: Kirana ga ’yan kasuwa shi ne su hada kai su rike gaskiya, kuma su yi adalci a tsakaninsu, idan suka yi haka za su zauna lafiya kuma za su samu nasara.