Akwai yiwuwar ƙara farashin fetur a Najeriya
Masana na zargin sanarwar NNPCL wata dabara ce ta tabbatar da ƙarin kuɗin man
Alamu sun bayyana da ke nuna yiwuwar ƙara farashin man fetur a Najeriya a hukumance.
Karo na huɗu ke nan da za a samu ƙarin farashin mai cikin watanni 15 na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Hakan na zuwa ne bayan Kamfanin Mai Na Kasa (NNPCL) ya sanar cewa yana fama da ƙarancin kuɗaɗe da zai biya ’yan kasuwa bashin kuɗaɗen tallafin da suke bi.
Tuni dai NNPCL ya sanar da Kwamitin Rabon Kuɗaɗen Asusun Tarayya (FAAC) cewa bashin tiriliyan hudu da biliyan 560 da ’yan kasuwa suke bi na kuɗin tallafin mai daga wata Agustan 2023 zuwa Yunin 2024 — sakamakon tashin Dala.
- Yadda ’yan banga suka yi wa Fulani 11 ’yan gida ɗaya kisan gilla
- Sojoji sun hallaka ƙasurgumin ɗan bindiga a Kaduna
Jami’in hulda da jama’a na NNPCL, Olufemi Soneye, ya ce yawan bashin kuɗaɗen tallafin da ’yan kasuwa ke bin kamfanin na shigo da mai, yana barazana samuwar wadataccen mai a ƙasar.
Duk da cewa mahukuntan NNPCL sun sha ba da tabbacin cewa akwai isasshen mai da zai wadaci ’yan Najeriya, a ƙarshe sun tabbatar cewa bashin da ’yan kasuwa ke bin ta na shigo da man ya yi yawa.
Hakan kuwa na barazana ga yiwuwar vi gaba da samuwar man a Najeriya.
A watannin baya dai kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar da rahoto cewa bashin da ’yan kasuwa ke bin NNPCL ya haura Dala biliyan shida.
A ’yan makonnin nan dai jami’an gwamnati na nuna alamun yiwuwar ƙara farashin man fetur a sakamakon tashin farashin canjin Dala.
Jami’an gwamnatin sun bayyana cewar ba za a iya ci gaba da sayar da litar fetur a kan N617 idan aka yi la’akari da tashin Dala.
A ’yan makonnin nan dai dogayen layukan ababen hawa sun dawo a gidajen man Najeriya inda ’yan kasuwa ke sayar da lita a kan N720, wasu gidajen man ma har N1000.
A watan Mayun 2023 farashin mai ya ninninku a Najeriya bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da janye tallafi a ɓangaren.
Daga bisani ta bayyana cewa ta ci gaba da biyan tallafi, alhali ta shafe tsawon lokaci tana musawa.
A wata takarda da Ministan Kiɗi, Wake Edun, ya aike wa Tinubu, ya bayyana wa shugaban ƙasan cewa kuɗin da za a kashe wajen biyan tallafin mai a 2024 ya haura Naira tiriliyan 5 da biliyan 400.
Hakan kuwa ya haura abin da aka kashe wajen biyan tallafin a 2023 da Naira tiriliyan ɗaya da biliyan 800.
Jami’in hulda da jama’a na NNPCL, Olufemi Soneye, ya ce duk da haka, kamfanin na ƙoƙari tare da sauran masu ruwa da tsaki wajen ganin ba a samu ƙarancin man ba.
Dabara ce kawai —Masana
Masana dai na zargin sanarwar ta NNPCL wata dabara ce ta samun dalilin ƙara kuɗin litar man fetur ya kai N950 zuwa N1,000.
Sun ƙara da cewa sama da makonni biyu ke nan da jami’an gwamnati maganar yiwuwar ƙara farashin.
A ranar Litinin Ƙaramin Ministan Man Fetur, Heineken Lokpobiri, had, on Monday, ya umarci NNPCL ya daina sayar da man a ƙasa da farashin shigo da shi.
Lokpobiri ya bayyana cewa hakan zai magance fasa-ƙwaurin man da ake yi zuwa ƙasashe maƙwabtan Najeriya.
A baya-bayan nan dai Ƙungiyar Manyan ’Yan Kasuwar Mai ta Najeriya (MEMAN) ta sanar da cewa a kan N1,117 suka shigo da fetur a watan Yuli, Man Dizel kuma a kan N1,157.
Wani ɗan kasuwa ya bayyana mana cewa, “kusan babu makawa sai farashin mai ya tashi, tun yanzu harkar ta koma hannun ’yan kasuwa.
“Duk da cewa NNPCL ne babban mai shigo da man, ’yan kasuwa ma suna shigowa da shi.
“Lamarin ya baci ne a sakamakon raguwar yawan ɗanyen man da Najeriya ke fitarwa, wanda hakan ke shafar yawan tataccen da take shigo da shi.
“Kungiyar OPEC ma ta tabbatar da raguwar ɗanyen man da kasashe suke fitarwa, ciki har da Najeriya,”