Akwai yiwuwar a samu shugaban kasa farar fata a Afirka

kasar Zambiya ba kasa ce da aka saba jin ta yi wani jawabi mai jan hankali ba a zauren majalisar dinkin Duniya da ake gudanarwa a kowace shekara a birnin New York na kasar Amurka, amma a bana da Shugaban kasar Michael Sata ya kasa gabatar da jawabinsa a gaban zauren taron, hankalin sauran wakilai […]

Akwai yiwuwar a samu shugaban kasa farar fata a Afirka
Akwai yiwuwar a samu shugaban kasa farar fata a Afirka

kasar Zambiya ba kasa ce da aka saba jin ta yi wani jawabi mai jan hankali ba a zauren majalisar dinkin Duniya da ake gudanarwa a kowace shekara a birnin New York na kasar Amurka, amma a bana da Shugaban kasar Michael Sata ya kasa gabatar da jawabinsa a gaban zauren taron, hankalin sauran wakilai daga sauran kasashen nahiyar ya karkata kansa.
Shugaban mai shekara 77 ya yanke jiki ya fadi a dakin otel din da ya sauka, ranar 25 ga watan jiya kuma yana karbar kulawa daga wasu likitoci da gwamnatin kasar Amurka ta aike masa da su.
Shugaban ya kwashe watanni ba tare da bayyana a bainar jama’a ba. A lokacin da yake jawabi a gaban majalisar dokokin kasar a farkon watan jiya, ya ce, “Ina nan ban mutu ba”, daga bisani kuma ya bar zauren majalisar ba tare da gabatar da jawabinsa ba.
Kamar yadda kudin tsarin mulkin kasar Zambiya ya tanada, Idan Shugaba Sata ya kasa gudanar da ayyukansa a matsayin shugaban kasa, mataimakinsa Guy Scott, wanda Bature ne, zai zama shugaban kasa har sai bayan gudanar da sabon zabe cikin kwana 90.
Idan hakan ya tabbata Mista Scott zai zama farar fata na farko da zai shugabanci wata kasa a nahiyar Afirka tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata a kasar Afirka ta Kudu kimanin shekara 20 da suka wuce.
Wani abu da ba a saba gani ba shi ne yadda ’yan kasar Zambiya suke ci gaba da bayyana damuwa – a wani abu akasin yadda aka saba gani a kasashen da ke makwabtaka da ita wato Afirka ta Kudu da kuma Zimbabwe, inda siyasar kasashen har yanzu ta ta’allaka ga launin fata da kuma mulkin mallaka.
Mista Scott wanda ya karanta fanin tattalin arziki daga Jami’ar Cambridge, kuma daya ne daga cikin fararen fata 40,000 da ke zaune a kasar. An haife shi ne a garin Libingstone kimanin shekara 70 da suka wuce, kuma mahaifinsa ya isa Zambiya gabanin samun ’yancin kan kasar. Kamar mahaifin nasa Mista Scott ya kansace wani fittacen dan majalisar dokokin kasar kuma wani mai adawa da mulkin mallaka. Kuma ya sha yabo a lokacin da yake ministan aikin gona a cikin shekarun 1990.
A lokacin da ya dare kujerar mataimakin shugaban kasa a shekarar 2011, shi da Mista Sata  sun kawo ci gaba ga kasar sosai, inda tattalin arzikin kasar yake bunkasa da kashi shida cikin 100 a kowace shekara.