Farashin man fetur zai sauko a Nijeriya —’Yan kasuwa
’Yan kasuwa sun bayyana ƙwarin gwiwar cewa farashin fetur zai ragu a Nijeriya sakamakon fara lodin tataccen mai daga Matatar Fatakwal
Shugaba Bola Tinubu ya umarci Kamfanin mai na Najeriya (NNPCL) ya gaggauta farfaɗo da matatar mai Kaduna da Warri da sauransu, domin bunƙasa amsar da mai a cikin gida da kuma mayar da Najeriya babbar cibiyar makamashi.
Hakan na zuwa ne a yayin da ’yan kasuwa suka yi marhabin da fara fitar da tataccen mai daga matatar mai ta Fatakwal, inda suke sa ran hakan zai kawo gasa da inganci da kuma faɗuwar farashin man.
Bayan watanni 11 matatar man ta fara lodin kayayyakin man fetur, inda a halin yanzu motoci kusan 100 ke lodin mai daga matatar zuwa sassan Nijeriya.
Kamfanin NNPC ya sanar da fara fitar albarkatun man fetur daban-daban da suka hada da man fetur, dizal, da kananzir daga matatar Fatakwal a ranar Talata.
Shugaban Kamfanin na NNPC, Mele Kyari, ya bayyana hakan a matsayin babbar nasara ga Nijeriya, wanda ke nuna sabon zamani na ’yancin kai a fannin makamashi da bunqasar tattalin arziki.
Kungiyar Manyan Masu Kasuwar Makamashi ta Najeriya (MEMAN) ta yi imanin cewa yalwar man zai kawo raguwar farashinsa.
Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya (IPMAN) kuma tana sa ran wannan cigaban zai haifar da raguwar farashin saboda karuwar gasa.
Kimanin manyan motoci 100 ne ke lodin kayayyakin a halin yanzu, kuma matatar Fatakwal na da burin samar da manyan motoci 200 a kullum.
Matatar Fatakwal na da ƙarfin samar da albarkatun tataccen mai da suka haɗa da man fetur, kananzir, dizal, man fetur, da kuma iskar gas.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya kamfanin NNPC murna sannan ya bukaci a gaggauta farfaɗo da sauran matatun man, domin bunƙasa amsar da mai a cikin gida da kuma mayar da Najeriya babbar cibiyar makamashi.