Akwai yiwuwar mazauna karkara su sha wahalar canjin kudi a 2023 – Masani

Ya ce a yawan bankunan da ke Jihar Legas sun zarta na Arewacin Najeriya baki daya

Akwai yiwuwar mazauna karkara su sha wahalar canjin kudi a 2023 – Masani

Wani masanin tattalin arziki a Jamiar Ahmadu Bello da ke Zariya ya yi hasashen akwai yiwuwar za a iya fuskantar matsalar canjin kudi saboda karancin bankuna a yankunan karkara.

Farfesa Ahmad Bello Dogarawa, malami a Sashen Koyar da Kasuwanci na jami’ar ne ya yi wannan hasashen a tattaunawarsa da Aminiya a Zariya.

Ya gargadi al’umma da su guji yin fargar-jaji sai lokaci ya kure kafin su garzaya bankuna domin yin canjin duk da akwai dan sauran lokacin da aka diba na canza kudaden.

Dogarawa ya kuma gargadi ’yan Arewa musamman masu dabi’ar boye kudi a gida da su hanzarta mika su a bankuna kafin lokaci ya kure.

Haka nan kuma ya ce tuni mutanen Kudancin kasar nan suka yi wa ’yan Arewa nisa a harkar.

Ya bayar da misalin yawan bankunan al’umma da ke Jihar Legas da cewa sun fi yawan wadanda ke Arewacin Najeriya gaba daya.

Malamin ya kuma bukaci babban Bankin Najeriya (CBN) da ya fadada hanyoyin fadakarwarsa ta hanyar amfani da Limamai da kungiyoyin addinai da kuma kungiyar matasa saboda sune suka fi kusa da al’umma.

Farfesa Dagarawa, ya kara da cewa, karancin bankuna da kuma wuraren hada-hadar kudade sun yi karanci musamman a yankunan karkara, wanda ya ce hakan ne ya sa ake hasashen cewa al’umma karkara za su sha wuya wajan sanin kalar kudin.

Haka kuma rashin wayar da kai, ze haifar da asara ga mutanen karkara, kuma ana fargabar cewa wasu bata-gari na iya samun damar cutar da mutanan karkara da kudaden jabu.

Farfesa ya ce amma duk da haka amfanin da canjin ze kawo yana da yawa musamman wajan sayen kuru’u a lokacin zabe, duba da irin yadda ’yan siyasa suka rinka fitar da makudan kudade a zabukar fid-da gwani da ya gudana.

San nan hakan ze ragewa masu satar mutane don neman kudin fansa da suke karba a hannun mutane.