Akwai yiwuwar Messi ya koma Saudiyya

Kungoyin kwallon kafa a Saudiyya na rububin dauko Lionel Messi daga kulob dinsa na Inter Miami da ke Amurka

Akwai yiwuwar Messi ya koma Saudiyya

Kungoyin kwallon kafa a Saudiyya na kokarin dauko Lionel Messi Gasar Kwararru ta kasar daga kulob dinsa na Inter Miami da ke Amurka a matsayin aro.

A zangon wasanni na bazara ne gwarzon dan wasan mai shekaru 36 ya koma Inter Miami bayan ya bar Paris Saint-Germain da gasar Ligue 1.

A yayin da yanzu sai nan da watan Fabrairu 2024 Messi sai ci gaba da wasa a gasar MLS Easter Conference tare da Inter Miami, kungiyoyin Saudiyya na kokakarin dauko shi a matsayin aro kafin lokacin.

Wakilin Sky Sports News, Rudy Galetti, ya ce tuni wani kamfani a Saudiyya ya fara zawarcin gwarzon dan wasan duniyan domin ya rattaba hannu ya dawo gasar Saudi Pro League kafin a zangao wasanni na hunturu.

A baya dai Messi dan kasar Argentina ya yi watsi da tayin albashin miliyan £350 daga kungiyar Al-Hilal da ke Saudiyya.

Al-Hilal ce kungiyar da tsohon abokin wasansa a tsohuwar kungiyarsu ta Barcelona, Neymar ya koma.

Yanzu dai rahotanni sun nuna kungiyoyi daban-daban a Saudiyya na zawarcin Messi inda ake zaton nan da gaba za a san kwanan zancen.

Zuwan Messi Saudiyya zai iya taso da gabar da ke tsakaninsa da babban abokin adawarsa, Cristiano Ronaldo, wanda a watan Janairu ya bar Manchester United ta Ingila zuwa kungiyar Al-Nassr ta a kan miliyan £162 duk shkera.

A gefe guda kuma, Barcelona, tsohuwar kungiyar da Messi ya bari, tana kokarin dauko tsohon dan wasan nata a matsayin aro.