Akwai yiwuwar nada babban dogarin Tinubu a sarautar mahaifinsa
Saura kiris a nada babban dogarin shugaba Tinubu, Laftanar-Kanar Nurudeen Yusuf, a sarautar Ilemona a Karamar Hukumar Oyun ta Jihar Kwara
Babban dogarin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Laftanar-Kanar Nurudeen Yusuf, na dab da darewa kujerar sarautar Elemona na Ilemona a Karamar Hukumar Oyun ta Jihar Kwara.
Idan aka nada Laftanar-Kanar Nurudeen Yusuf, zai gaji mahaifinsa, Oba Yusuf Omokanye Oyekanmi, wanda ya rasu a watan Mayu, yana da shekaru 95 a duniya.
Binciken da Aminiya ta gudanar a daren Laraba ya nuna cewa abin da ake jira kafin nadin nasa shi ne amincewa da kuma sanarwar a hukumace daga gwamnatin jihar.
Majiyoyin fadar shugaban kasa da masu ruwa da tsaki a garin Oyun da suka tabbatar wa wakilinmu zaben nasa, sun ce al’umma sun yi matukar farin ciki da zabin Yusuf.
- NAJERIYA A YAU: Rayuwar Sheikh Dahiru Bauchi Cikin Ƙarni Guda
- Tubabbun ’Yan Boko Haram 560 Sun Fara Koyon Sana’o’i A Borno
Wani tsohon shugaban majalisar wanda ya so a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin gamana kan batun a hukumance ya ce “Gaskiya ne amma har yanzu babu sanarwa a hukumance.
“A baya-bayan nan Yusufu ya kawo ci gaba a cikin al’ummarmu, kusan kullum yake kawo wa al’ummar Ilemona ci gaba.
“Ya kawo kwalejin ilimi kuma ya sake sayen mafi yawancin filayen da mahaifinsa ya sayar wa al’umma.
“Ilemona karamin gari ne, amma idan ka ga irin yadda ya bunkasa garin yanzu, za ka fahinci dalilin da ya sa majalissar zabar sarki mulki suka ba shi wannan mukami.
“Har yanzu bai ce ya amince ko ko ya ƙi ba. Amma kowa yana farin ciki da hakan.”
Wata majiyar gwamnati ta ce, “Sarakuna ne suka zabo Yusuf tare da mikawa ga ma’aikatar kula da harkokin kananan hukumomi da cigaban al’umma, domin amincewar gwamna.”
Da aka tuntubi kwamishinan ma’aikatar, Hon Abdullahi Abubakar Bata a daren Laraba, ya ce “ba a kammala aikin nadin nasa ba.
“Har yanzu da saura (nadinsa), ba mu sanar da komai ba. Ni ne wanda zan sanar da amincewar gwamnati.
“Na karanta abubuwa da yawa a shafukan sada zumunta game da shi amma na yi watsi da su.
“Nadin sarauta ba wani abu ba ne na sirri ko keɓantacce. Amma da zarar mun kammala, zan sanar da ku”, in ji kwamishinan.
Har ya zuwa lokacin cika wannan rahoto, gwamnati ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
Wane ne Yusuf?
Bayan ya kammala karatunsa a fannin kimiyyar kwamfuta daga Offa Polytechnic a shekarar 2000, Yusuf ya shiga makarantar horas da sojoji kananan hafsoshin sojin Najeriya (NDA) da ke Kaduna, inda ya kammala digirinsa na farko a fannin Injiniya (Electrical-Electronics).
Tsakanin 2004 zuwa 2005, ya halarci kwalejin sojoji na Royal Military Academy Sandhurst (RMAS) a Birtaniya.
RMAS wata cibiya ce da ake horar da dukkan jami’an sojin Birtaniya don kan jagorantar sojojin da ke karkashinsu.
A 2006 ya samu horo a makarantar leken asiri ta sojojin Najeriya da ke Legas inda aka horar da shi a fannin leken asiri da tsaro kamar yadda tsarin horas da sojojin Najeriya ya tanadar.
Kwas na Young Officer’s Infantry da ya yi a Kaduna a 2007 a 2007 ya ba shi ƙwarewar aikin soja kan amfani da nau’ikan makaman da ake amfani da su a cikin runduna ta musamman da kuma ayyuka na musamman.
A shekara ta 2008, Yusuf ya kammala kwasa-kwasan leken asiri da ba binciken tsaro don inganta kwarewarsa a matsayinsa na soja.
Daga 2009 zuwa 2018, jami’in mai magana da harsunan Yarbanci da Hausa da Ingilishi da Faransanci, ya samu horon soji da dama a kasashen Mali da Pakistan da China da Isra’ila da Birtaniya, Sudan, Masar, Faransa
A 2018 kuma, Yusuf ya samu digirinsa na biyu a fannin tsaro daga Kwalejin Kings da ke Landan.
Hakazalika ya samu shaidar kammala karatun digiri na biyu a fannin nazarin zaman lafiya da warware rikice-rikice daga Budaddiyar Jami’ar Kasa (NOUN).
A kwanakin baya ne Yusuf ya kammala wani kwas din soja da aka tsara domin kwamandojin sojoji a Jaji, Kaduna, kafin a nada shi a matsayin babban dogarin zababben shugaban kasa.
Ayyukansa
Yusuf ya yi aiki a matsayin jami’in da ke kula da na’urori na runduna ta 119 Intelligence Group, Legas.
Daga nan sai aka mayar da shi Birged na 4 da Benin, Jihar Edo inda ya yi aiki a matsayin Jami’in Ayyuka.
Ya kuma yi aiki a matsayin kwamanda rundunar leken asiri a fadar shguaban kasa.
A shekarar 2015, an kara masa girma zuwa jami’in rundunar tsaron fadar shugaban kasa a fadar gwamnati da ke Abuja.
A shekarar 2017, Yusuf ya yi aikin a matsayin ma’aikaci mai daraja ta daya na hukumar leken asiri ta Najeriya (NAIC).