Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohi 11

Hukumar Kula da Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) da hadin gwiwar Hukumar Kula da Ambaliyar Ruwa ta Najeriya (NIHSA), sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar za a fuskanci ambaliyar ruwa a jihohi 11 na kasar nan a tsakanin wannan wata na Agusta zuwa Oktoba.Jihohin da ake hasashen ambaliyar za ta shafa sun hada da Kaduna […]

Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohi 11

Hukumar Kula da Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) da hadin gwiwar Hukumar Kula da Ambaliyar Ruwa ta Najeriya (NIHSA), sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar za a fuskanci ambaliyar ruwa a jihohi 11 na kasar nan a tsakanin wannan wata na Agusta zuwa Oktoba.
Jihohin da ake hasashen ambaliyar za ta shafa sun hada da Kaduna da Kwara da Nasarawa da Yobe da Zamfara da Bauchi da Borno da Benuwai da Akwa Ibom da Kuros Riba da kuma Delta.
Hukumar NiMet a sanarwar da ta fitar a ranar Litinin da ta gabata ana sa ran samuwar ambaliya a wadannan jihohi ne saboda kasa ba za ta iya shanye ruwan sama da za a rika jibga musu ba a makonni masu zuwa, wanda hakan ya zo daidai da lokacin da ruwan sama ya fi sauka.
Idan za a iya tunawa a hasashen ruwan sama na bana (SRP), NiMet ta ce yayin da wasu yankuna za su fuskanci karancin ruwan sama sabanin yadda saba samun ruwa sosai, amma duk da haka za a iya samun ambaliya a wuraren da suke fuskantar ambaliyar.
“Wannan hasashe sun dace da ta Hukumar Kula da Ambaliya da Duniya (AFO) da Hukumar NIHSA ta fitar,” inji sanarwar.
Hukumar NiMet ta shawarci gwamnatocin jihohi da garuruwa da daidaikun jama’ar da suke fuskantar barazanar ambaliyar da su dauki matakan rigakafi kamar share hanyoyin ruwa da kwashe magudanun ruwa tare da kauce wa duk wani abu da zai toshe hanyoyin wucewar ruwa