Akwai yiwuwar Shekau ya rasu – JTF
Hukumomin soja a Maiduguri sun fadi a ranar Litinin da ta gabata cewa akwai yiwuwar Shugaban kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lid Da’awati wal Jihad ko Boko Haram, Abubakar Shekau ya rasu bayan da ya samu raunuka a artabun da jami’an tsaro suka yi da ’ya’yan kungiyar a watan Yuni.Kakakin Rundunar JTF da ke aiki samar […]
Hukumomin soja a Maiduguri sun fadi a ranar Litinin da ta gabata cewa akwai yiwuwar Shugaban kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lid Da’awati wal Jihad ko Boko Haram, Abubakar Shekau ya rasu bayan da ya samu raunuka a artabun da jami’an tsaro suka yi da ’ya’yan kungiyar a watan Yuni.
Kakakin Rundunar JTF da ke aiki samar da tsaro a Maiduguri, Laftana Kanar Sagir Musa ya ce a cikin wata sanarwa, “Rahoton sirri” ya nuna akwai yiwuwar Shekau jagoran Boko Haram ya mutu a tsakanin 25 ga Yuli zuwa 3 ga Agusta, lokacin da yake jinyar raunukan da ya samu a harin da sojoji suka kai dajin Sambisa.
Bayanin na JTF ya zo ne bayan mako daya da sanya wani faifan bidiyo a intanet da ya nuna wani mutum da ya yi da’awar shi Shekau ne yana magana kan batutuwan da suka faru wasu kwanakin da suka biyo bayan cewa ya rasu.
A cikin bidiyon da aka fitar ranar 12 ga Agusta mutumin ya yi magana kan karamar Sallah da aka yi ranar 8 ga Agusta da hare-haren da ’yan kungiyar suka kai Gamboru- Ngala da Bama da Malam Fatori a makon farko na watan.
Sai dai JTF ta ce bidiyon tamkar wasan kwaikwayo ne da wani ya fito a matsayin Shekau, domin ’ya’yan kungiyar su ci gaba da aiwatar da ayyukansu na ta’addanci, amma rahotannin sirri sun nuna Shekau ya rasu kwanaki ko mako daya baya. Rahoton sirrin ya nuna an harbi Shekau a ranar 30 ga Yuni a fafatawar dajin Sambisa. “An yi mugun rauni ga Shekau a yayin fafatawar kuma magoya bayansa sun gudu da shi zuwa garin Amitchide, wani gari da ke iyakar Najeriya da Kamaru don yi masa jinya…. Akwai yakinin cewa Shekau ya rasu a tsakanin ranar 25 ga Yuli da 3 ga Agustan bana,” inji Kanar Musa.
A ranar 14 ga Agusta, sojoji sun ce suna kashe Na’ibin Shekau mai suna Momodu Bama, wanda ake yi masa lakabi da “Abu Sa’ad.” Babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da rasuwar Shekau ko Bama.
Sai dai wata majiyar soja ta shaida wa Aminiya cewa tana da yakinin Shekau ya rasu, inda ta ce, rundunar sojan ta dauki lokaci tana nazarin rahoton sirri kan mutuwar Shekau kafin ta fitar da sanarwar cewa akwai yiwuwar ya rasu.
Majiyar ta ce, jami’an leken asiri na soja suna aiki da sauran hukumomin leken asiri na duniya wajen nazarin bayanan da suka sa aka yanke shawarar Shekau ya rasu.