Akwai yiwuwar tsagaita wutar yaƙin Isra’ila a Gaza albarkacin watan Ramadana

Yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza – wanda yanzu ya shiga kwana na 145 — ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 29,782.

Akwai yiwuwar tsagaita wutar yaƙin Isra’ila a Gaza albarkacin watan Ramadana

Shugaba Joe Biden na Amurka ya bayyana yiwuwar cimma nasarar yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin da Isra’ila ke yi a Gaza kafin kamawar watan Ramadana.

Masu shiga tsakani daga kasashen Amurka da Masar da kuma Qatar na aiki kan wani shiri na yarjejeniya wadda a ƙarƙashinta ake sa Hamas za ta saki fursunonin yaƙi da dama da ta yi garkuwa da su, inda ita kuma Isra’ila ta sako fursunonin Falasɗinawa da kuma tsagaita wuta tsawon makonni shida.

A lokacin tsagaita wutar ta wucin-gadi, za a ci gaba da tattaunawa kan sakin sauran wadanda aka yi garkuwa da su.

Kalaman na Biden a jiya Litinin na sake tabbatar da rashin goyon bayan Amurka wajen samar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin da nufin kawo karshen yakin na watanni 5.

Kafin kalaman na Biden dai bangarori da dama sun yi yunƙuri tare da mabanbantan tattaunawa a ƙoƙarin dakatar da yakin wanda zuwa yanzu ya kashe Falasɗinawa kusan dubu 30 baya ga jikkata wasu akalla dubu 70.

Cikin kalaman na Biden a zantawarsa da gidan talabijin na NBC, ya bayyana cewa Isra’ila ta amince za ta dakatar da hare-harenta a cikin watan Ramadana don samun damar kubutar da ilahirin fursunonin da ke tsare a hannun Hamas.

Isra’ila dai na ci gaba da zafafa hare-hare a Rafah wanda ya sake tagayyara ayyukan jin-ƙai a Gaza.

Yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza – wanda yanzu ya shiga kwana na 145 — ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 29,782, galibi yara da mata, tare da jikkata mutum 69,879.