Jami’ar Al-Azhar ta goyi bayan Hamas kan yaƙi da Isra’ila

Jami’ar Al-Azhar da ke Masar ta bayyana goyon bayanta ga kungiyar Hamas da ke ƙazamin faɗa da Isra’ila a yankin Zirin Gaza.

Jami’ar Al-Azhar ta goyi bayan Hamas kan yaƙi da Isra’ila

‘Yan sandan Isra’ila na korar ‘yan jaridar da ke daukar rahoton harin. (Hoto: Ammar Awad/Reuters).

Jami’ar Al-Azhar da ke Masar ta bayyana goyon bayanta ga kungiyar Falasɗinawa ta Hamas da ta shafe kwanaki biyu yanzu tana gwabza ƙazamin faɗa da Isra’ila a yankin Zirin Gaza.

A ranar Asabar Al-Qassam Brigade, reshen sojin Hamas ya ƙaddamar wani gagarumin hari kan Isra’ila a matsayin martani kan cin zali da mamayewar da Isra’ila ke ci gaba da yi a Zirin Gaza.

Rikicin bangarorin biyu da aka shafe sama da shekaru 60 na kuma da alaka da hare-haren Isra’ila kan mata da yara da tsofaffin Falasɗinawa da kuma masu ibada a Masallacin Kudus, masallaci mafi alfarma na uku a addinin Musulunci.

Al-Azhar wadda babbar cibiyar Ilimi da addini ce a Masar da ma duniya tsawon shekaru aru-aru ta jaddada cewa gwagwarmayar Hamas domin ’yanta kasar Falasɗinu daga mamayar Isra’ila babban abin yabo ne, kuma da alamar nasara.

“Muna ba da cikakken goyon bayan samun ’yancin Falasɗinawa, wadanda bayan tsawon lokaci na yanke kauna, suka dawo mana da kwarin gwiwa ta samun nasara,” in ji wata sanarwar Jami’ar Al-Azhar.

Ta kuma zargi kasashen duniya bisa yada suke baki biyu a rikicin Falasɗinawa da Isra’ila, “musamman a kan abin da ya shafi ’yancin Falasɗinawa.”

Daruruwan mutane ne aka tabbatar sun mutu a sabon rikicin, wanda ke zuwa shekara 50 bayan harin ba-zatan ƙasashen Larabawa a kan Isra’ila a shekarar 1973, bisa jagorancin kasashen Masar da Syria.

Isra’ila ta tabbatar da mutuwar ’yan asarta akalla 700 baya wasu sama da 100 da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza.

Isra’ila ta kaddamar ha harin jirage kan mai uwa da wabi a yankin Gaza, inda kawo yanzu aka kashe sama da mutum 400.

Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana damuwa kan yawan mutane da aka hallaka a sabon rikicin.

Ofishin UNICEF na Gabas ta Tsakiya ya ce yana sanya ido kan batun tafiyar hakkin kananan yara a yakin da ke ci gaba tsakanin Isra’ila da Hamas.

A ranar Asabar Hamas ta harba rokoki sama da 2,000 zuwa Isra’ila daga Gaza sannan mayaƙanta suka kutsa yankin Gabashin birnin Kudus suka yi wa Isra’ilar Lahabi, kafin ta mayar da martani.

Tuni kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta amsa kiran Hamas ga Larabawa da sauran kungiyoyin , har ta fara kaddamar da hare-haren rokoki kan Isra’ila.