‘Al-Makura ne Gwamna mafi adalci da rikon amana a Najeriya’

An bayyana Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura a matsayin Gwamnan da ya fi nuna gaskiya da adalci da rikon amana a Najeriya.&nbsp Wata kungiya mai zaman kanta da ake kira Transparency and Accountability Organization ne ta bayyana haka ta bakin shugabanta Mista Moses Godwin a lokacin ba Gwamnan lambar yabo a otel din Sheraton […]

‘Al-Makura ne Gwamna mafi adalci da rikon amana a Najeriya’
‘Al-Makura ne Gwamna mafi adalci da rikon amana a Najeriya’

An bayyana Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura a matsayin Gwamnan da ya fi nuna gaskiya da adalci da rikon amana a Najeriya.&nbsp

Wata kungiya mai zaman kanta da ake kira Transparency and Accountability Organization ne ta bayyana haka ta bakin shugabanta Mista Moses Godwin a lokacin ba Gwamnan lambar yabo a otel din Sheraton da ke Abuja.
Mista Moses Godwin ya ce kungiyar da ke da sassa a kasashen waje da dama tana sa ido ta kuma tantance ayyukan gwamnoni ne don gano wanda ya fi aiki da rikon amana da sauransu inda a cewarsa binciken da ta gudanar ta gano cewa Gwamna Al-Makura ne ya fi kowane Gwamna a kasar nan aiki wa al’ummarsa da rikon amana da kuma adalci.
Daga nan sai ya bukaci Gwamnan da ya ci gaba da haka don sauran gwamnoni takwarorinsa su yi koyi da shi.
Da ya ke mayar da jawabi Gwamna Umaru Tanko Al-Makura ya nuna farin ciki dangane da wannan karamci inda ya alakanta nasarori da yake samu ga hadin kai da goyon baya da al’ummar jihar baki daya musamman talakawa ke ba gwamnatinsa. Ya ce karimcin babu shakka zai kara masa kwarin gwiwa wajen ci gaba da gudanar da shugabanci nagari don canja rayuwar al’ummar jihar.